KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bayan sun gama waya da barister ta nemi layin dady domin taji ko yayi nasarar ganin wanda ya fita nema sai dai kira biyar tana yi masa bai dauka ba ,Kanta taji ya dan sara mata a hankali ta zame ta zauna a inda take tana cigaba da neman layinsa abu daya ake ce mata switch off “oh allah me yake faruwa kuma haka ?”wasu hawaye suka zubo mata Komai yayi worst gareni allah ka kawo min mafuta ka bawa yarinya lafiya ,kayi mata zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwarta ta dafe goshinta daidai inda take jin yafi sara mata bayan kamar minti goma wayar ta sake daukar qara ta lalubo tare da bude idanunta da kyar sunan kaninta bashir taga yana yawo a screen din wayar ,cike da sanyin jiki ta dauka.

“Alhamdulillah taji sauki ta fad’a cikin rawar murya , doctor muyis yace yau zai zo, yanzu dai jiran zuwansa mike yi ,eh to dai da sauki zamu ce tana cin abinci wani lokacin kuma sai ta kwana ta yini bata ci ba , eh babu masu zuwa sai important people’s ke zuwa dubata ,wannan damuwar bashir cireta ba me yuwu bane ,wallahi na sani duk shine ya janyo mana wannan matsalar gashi yayi sanadin jefa rayuwata cikin tashin hankali tun matsalar nan bata Kai haka ba ka kawo shawara amman yaki yau gashi shi kansa yana cikin damuwa yanzu haka wajen yayan alhj bello yaje ko allah zai sa adace a fito dashi yaron cikin sirri sai a inganta rayuwarsa duk abinda ake ciki zan kira na fad’a maka suka shiga da tautaunawa .”

Sama sama tanwer take jin maganar mumy na tashi a dakin domin yinin ranar bacci take a hankali ta bude idanunta ,yau dai allah ya taimaka da sunan allah a bakinta ta farka sannan ta kai dubanta ga mumy dake zaune tana waya can ta dauke idanunta akanta ta maida ga kallon sama tana kallon fankar dake bisa cili sai faman juya take ,tana son tuna wani abu amman ta kasa ,doctor muyis ne ya turo kofar dakin ya shigo bakinsa dauke da sallama bai gama shigowa ba doctor sadiq ya turo kofa ya shigo shima bakinsa da sallama jin tasa murya tasa tanwer ta dawo daita daga son tuno wani abu daya shude kwanaki kadan da suka gabata.”

Da sauri ta mike zaune tana dubansa tana murmushi
hakan ya janyo hankalin mumy dake waya da bashir sak me kama da adnan dinta ta gani sai dai bambamcin launin fata domin shi dai adnan dinta fari ne sol sabani wannan da take gani chocolate colour ne , shi kansa dr sadiq kallonta yake yana kokarin son tuna inda yasan fuskar duk da wacan fuskar daya sani ta dan bambamta da wannan .”
“Wannan tayi duhu kadan na rashin lafiya bangaren damuwa kuwa daman haka ya ta’ba ganin fuskar cike da tsantsar damuwa ruky ta shigo dakin hannunta rike da basket din abinci a daidai lokacin da dr muyis ya fara magana a tsanake “alhamdulillah mumy yau dai ga dr sadiq nan yazo domin duba lafiyar tanwer kuma inshaallahu komai zai zama normal.”

“Alhamdulillah sannu da zuwa ta fad’a itama tana masa kallon sani bai amsa mata ba domin har lokacin dubansa naga kallon tanwer data dan samu natsuwarta ba kamar kullum ba a natse ya matsa bakin gadonta da sauri sauri abubuwa suka fara dan dawo mata sai dai fahimtar datai Kanin adnan ne yasa ta runtse idanunta brain dinta na sake shiga tunani me tsanani data tuno harbin daaka dingawa gidansa wanda ita a tunaninta wannan harbin duk wanda ke cikin gidan bai isa ya tsira ba domin harbin zai iya samun kowa .”

a hankali ta bude bakinta “ina adnan dina yake .”?tanwer ta tambaya dr sadiq.“Tabbas ita ce yarinyar daya ta’ba gani tare da yayansa ya kawota gurinsa domin ya duba masa lafiyarta kenan itama tana nemansa ne kamar yadda suma suke nemansa .”?
wasu hawaye ke sauka a kuncinta masu matukar quna duk suka zuba mata ido suna kallonta hawaye ne ya zubo a kuncin mumy “wannan soyayyar me karfi ce ,ta rasa wani irin so tanwer takewa adnan .”

“Soyayya kamar wacce akayiwa asiri ?a lokaci daya tanwer ta bude idanunta ta sake daurasu akan dr sadiq qirjinta na wani dokawa yayinda jikinta ya dauki rawa ,sukai shiru suna kallon juna cikin sheshekan kuka ta kira sunansa data ta’ba jin jaguwa ya kira a gabanta “sadiq kuma kunji abinda ya afka wa adnan ko .”? tayi masa tambayar cikin tsananin tashin hankali.”

Wani irin lugude bugu qirjinsa yayi da karfi “acikin dan kankanin lokaci mun rasa adnan ya mutu ya bar duniyar nan ya barmu da sauri ya zare medical glas din dake makale a idanunshi yana mata wani irin duba tausayinta ya ratsa duk wanda yake cikin dakin dr sadiq ya shiga girgiza mata kai jikinsa na rawa amman ya kasa furta komai tanwer ta sake karfafa kukanta “wannan wace irin qaddara ce babu mamaki munyiwa allah wani gagarumin laifi ne yasa qaddara ta tsananta agaremu “.
Can kuma ta soma zarewa “adnan ya zame min wahala da tashin hankali sai da nace masa ya hakura da wannan sana’ar ba sana’a bace gashi…”
Ruky tace “tanwer ki natsu ki kwantar da hankalinki ubangiji baya daura qaddararsa akan mumini sai in har zai jarabeshi ki daure kici jarabawa ta ubangiji kada ki dauka hakan rashin qauna ce daga ubangiji duk wanda allah ke só tô zai jarabeshi dan haka ki kwantar da hankalinki kisa addua agaba da yarda allah itace zata kawo saukin abinda ya afka masa .”

Dr sadiq ya waiga daga inda ya jiyo sautin muryar yaji kalamanta wani iri har cikin ransa ita kuwa tanwer yatsun hannunwasa take kallo masu tsantsar kama dana adnan dinta “yau kwanan adnan nawa da rasuwa?.”sadiq ya sake rikicewa yana mata wani irin kallo “ kwana tara kenan ta bata amsa dan ita a tunaninta mutuwa yayi kamar yadda tanwer take fada tana maimaitawa .”

akwai abinda dr sadiq yake son tambaya amman ya gaza zuciyarsa ce kawai ke suya tana aúno masa abubuwa kar dai maganar hally ya tabbata mutuwa sukayi ? “to taya zasu matu basu sani ba sannan babu wani sako daya zo masu duk da bai maida hankalinsa ga kallon news ba acikin kwanaki saboda damuwar da yake ciki da ayukan gabansa yasan bazai yuwu su mutu haka batare daya an sanar masu ba ,yadda zuciyarsa ke quna haka na tanwer ke quna duk da bata tantance mutuwarsa ba amman tabbas abinda tagani mutuwa ce .””

Tunaninta ya tsaya anan cak ganin Ibrahim data gani yana bada umarnin harbi wani irin ihu ta saki me karfi tana cewa “na tsaneka Ib na natsenaka bana sonka I hate you bazan ta’ba yafe maka ba tunda ka kashe min adnan nan ta dinga fadar wasu batutuwa wanda kan dr sadiq ya daure ya gaza dauka bai san dalili ba amman ya kasa yarda da maganganunta da take kokarin sheida masa ,kashesa akayi danuwansa barawo ne ta hanashi sanar fashi yaki bari sadiq ya dube dr muyis yana jin wani irin radadi a zuciyarsa dr muyis ya dungule wani yawo da yayi zariya acikin makoshinsa yace “haka muke ta fama daita kamar yadda na fad’a maka wani saurayi take mutuwar so wanda ya kasance dan fashi da makami shine jami’an tsaro sukayi nasarar kamashi yanzu haka yana hannu amman ita abinda idanunta suka gani tayarda dashi yanzu me kake ganin zaayi dan abun nata bai yi karfi ba saboda kulawar da’ake bata da kuma adduaoi iyaye da mutane .”?

“Adnan dai wanda na sani suke soyayya danuwana ne uwarmu daya Ubanmu daya shine dan fashi ?”cike da tsoro dr muyis ya sake maimaita masa cikin tsananin mamaki jin abinda dr sadiq ya fada gabadaya kallo ya koma kan dr sadiq cike da damuwa yake girgiza kai “ba dai adnan dina ba .”
ya furta a fili yana sake girgiza kai .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button