KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Fashewa tayi da kuka zuciyarta na zafi kamar zata fito waje ,a hankali ta mike ta fito ta nufi dakinta ta kwanta akan gado amman har karfe biyun dare mumy bata runtsa ba tana tunanin wulakamcin da dady yayi mata gbdy damuwa tayi mata yawa but halin da Tanwer take ciki shine worst da yafi damunta dan tasan idan har dady yaki amincewa ta auri adnan zata iya rasa rayuwarta.”
Mumy tayi kuka har taji babu dadi duk sanda ta tuna bakaken maganganun minister sai sabon kuka ya kufce mata ,tana kwance tana matso ruwan hawaye daga cikin idanunta ya shigo dakin yyi kokarin tabata don ya rarrasheta ya kuma sake fahimtar daita illa abinda take son biyewa tan su aikata ta goce ya numfasa sannan ya hade hannunwansa guri daya ya fara magana “zainba ki yafe min maganganuna nayi kuskure amman lokaci yayi daya dace ki fahimceni nasan kina da right akan tanwer amman ta wannan bangaren sam bai dace ki goya mata ba da wannan hadin ba ,wallahi babban ciwo ne atare damu ,duk yadda dady yaso mumy ta fahimcesa amman ina hakan bai samu ba dan kuwa bata sauraresa ba sai ma wani mugun kallo take masa cike da tsana da bacin rai “me kuma zaka fada min nida ba uwar arziki bace ?har kana dauting ina da hankali bare aje batun hangen nesa ,ni da bani da cikakkiyar hankalin da ciwo acikin kwalkwaluwata ta yaya kake son na fahimceka yanzu ?.Yayi shiru yana cigaba da dubanta domin yasan wadan nan maganganun sun fi sauran tsaya mata arai da mata ciwo “am sorry zainab kiyi hakuri amman duk kece sila kina tunanin wani abu zai samu tanwer ne akan rashin aurensa ? “ wallahi babu abinda zai sameta idan ta gaji da kanta zata ma kanta nasiha ta hakura dashi .”

“Ba abinda zaka ce min insaurareka ko in fahimceka tun tuni ya kamata na fahimci cewar yanzu kai baka damu damu ba sai kanka da Ibrahim kake tunani,ka daina damuwa dani da diyata tun randa adnan ya shigo rayuwar tanwer yanzu baka damu da rayuwar kowa ba baka damu da farincikinmu ba ,baka damu da lafiyarmu ba sai kanka data Ibrahim , yarinya tana fama da ciwo acikin zuciyarta amman baka damu ka tausaya mata ka nemo mata magani ba bayan duk kai ne silar faruwar komai ka shuka abinda sakaya ta koma kanta bata ji bata gani ba , alhj tahir yaci amanarka amman duk da haka ka lashi takobin sai ka hada zuria dashi mutumin da yana nan baa nemeshi an rasa ba da zai iya kawo karshen numfashinka at any moment tunda ya iya turo maka yan fashi ai komai ma zai iya yi yaga bayanka,wallahi abubakar kaci amanarta da diyar cikinka …”
“Ki fahimceni zainab Ibrahim dabam mahaifinsa dabam idan kuma kema bakya son Ibrahim ki fad’a mata ta kawo min wani amman banda wannnan mutumin dan …”nima bance Ibrahim bashi da karki ba yana da daidai nashi amman ka duba ciwon da diyarmu take dauke dashi tanwer na dauke da ciwon soyayya wanda at any moment zata iya rasa ranta nidai tunda tace bata so Ibrahim ga wanda take so mu bata mu taimaka mu sa hannuwanmu
mu janyosa jikinmu mu inganta rayuwarsa ya bar sanaar “kina ganin idan shi ya bari sauran abokan sana’arsa zasu bari ne ko kuwa dukkanin su zamu taru mu inganta rayuwarsu dan son rai irin naki?
“Nice ma nake da son rai ?
“Kwarai kuwa zainba kina dashi ke nifa na soma tunanin ba kece kika haifi tanwer ba ina bukatar gwada jinina da nata domin na tabbatar da cewar tanwer diyata ce wacce na diga ko kuma akasin haka kawo min ita a matsayin diyata ban sani ba .”ya karasa maganar a fusace yana dafe goshinsa daya ji yayi masa mugun sara da karfi ,a matukar firgice take kallonsa kafin daga bisani ta fara magana cikin zafin rai da zuciya “gsky ne tunaninka yayi daidai , tanwer ba diyarka bace nima ba diya bace kaga sai ka daina takamar banza akan diyar da bata ka ba ,
kuma kasa ido ka gani zan tsaya mata ta auri adnan inshaallahu kuma zai zama mutun kirki har ma kayi alfahari dashi wata rana.”

jikinsa da hannunsa rawa suka kama ya kasa cigaba da tsayuwa adakin ya fito waje yana kai kawo tausayinkansa dana matarsa dana diyarsa ya kamashi ya kife kansa a bangon falon yana kuka yayinda yake ganin laifinsa ne domin dai yasan shine silar komai shine ya kawo alhj tahir gidansa da har yasan sirrinsa , sannna alhji tahir shine silar da dan fashi ya dasa mugun ciwo azuciyar diyarsa har adalilin haka ake shegenta masa diya ,ya sake fashewa da wani kuka “ya allah kawowa tanwer saukin abinda take ji akan yaron nan ,tanwer ko ba diyar cikina bace ta zama tawa har abada bazan iya rabuwa daita ba bare ma nasan karya ne babu wanda zai kalli yatsun kafafunta yace masa ba diyarsa bace fuska da tsarin jiki ne kawai na mahaifiyarta amman hatta hakoranta irin nashi ne .”
Ranar dai a gidan minister babu wanda ya runtsa daga mumy har dady da tanwer.”

Washegari gidan ya kasance tamkar anyi mutuwa babu wani jin dadi gabdayansu suna daki ,ruky ce kawai ke kai kawo a tsakanin masu aiki ,ta shiga dakin mumy bakinta dauke da sallama yayinda hannunta ke rike da flaks din abincinta ,ta ajiye akan center table ta karaso ta tsaya gabanta “sannu mumy ga abincikinki dan allah ki daure kici wani abu “.kai kawai ta daga mata sannan ruky ta fito ta shiga dakin tanwer ita kanta ta shiga damuwa sosai sakamakon ganin yanayin mumy “sister karki damu inshaallahu komai zai daidaita amman karki yarda ki bata da iyayenki akan wani nmj can wanda zai iya juya miki baya .” tana zaune a dakin tanwee tana kwantar mata da hankali dady ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama ya tsaya akan tanwer rukayya ta gaishesa ya amsa mata sannan ta fita ya kalli tanwer ya girgiza kai ita kanta tanwer din sai data sha jinin jikinta da irin kallon da yake mata sai daya numfasa sannan yace “Shikenan tanwer kin hadani fada da matata ? ta girgiza masa kai alamun”a’a !
“Wallahi da Kinsan tarihin haduwarmu da zainba har zuwa lokacin da muka sameki da bakiyi abinda zai kawo tashin hankali a tsakaninmu da zainab ba ,bamu taba samun matsala da zainba sai akanki ya fada yana furzar da iska sannan ya cigaba da magana na fada mata ta fada miki idan baki son Ibrahim ki kawo min wani zan baki shi amman banda wannan dan Iskan yaron ai tana jin haka “tasa masa kuka da karfin gaske “dady ya zanyi wallahi bani da karfin zuciyar da ina da karfin zuciya da zan iya kawar da komai a zuciyata na hakura dashi “
“Dan allah ki ka min dan iskan baki wallhi matsawar kika auri yaron nan tanwer babu ni babu ke sai dai ki nemi wani uban bani ba, “to ai dady bana halaka da kowa bare batun soyayya ko Ibrahim ma ni a mutunci na daukesa daga baya kamai ya sauya ni adnan kawai nake so bayan shi bazan iya rayuwa da kowani nmj ba , da dashi na yarda na amince in zauna in mutu a gidansa sai dai bazan só naga kun samu sabani a tsakaninku ba “ karki ce bakya son mu samu sabani mana kina so dan gashi kin janyo uwar ki tana jin haushina bayan bamu taba samun sabani daita ba sai akanki “ina sonku iyayena bazan so naga kun samu sabani akaina ba kune farincikina kune garkuwa,bangon jingina agareni ,wallahi ina sonku domin kunyi matuqar kokari akan kuga tarbiyyarta ta gyaru wallahi dady nasani ban maka adalci ba amman ban san yadda zanyi bane dady ka min addua ko zan daina jin abinda nake ji akansa ta karasa mgnr tana fashewa da kuka “wallahi da akwai abinda zanyi na daina son shi dady zanyi dan nima na gaji da wannan wahalar sai kuma jikin dady yayi sanyi , jiki a sanyaye ya fito daga dakin dan bazai iya jurar ganinta tana kuka ba ya shiga dakin mumy tana zaune ya karaso ya bude kular abincin daaka kawo mata bata ci ba ya kalleta ta kawar da kai alamun bata son ganinsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta “kiyi hakuri uwar gidana na fahimci halin da kike ciki ,na fahimci son da kikewa diyarmu ne yasa kike son biye mata amman kisani baa rayuwar aure a haka zainba wallahi aurawa tanwer yaron nan bashine karshen matsalarmu ba .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button