KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a hankali ta shiga girgiza Kai “no no impossible bashi  bane sam bai yi kama da irin wad’an nan mutane ba dukkanin  alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne   zuciyarta ta  tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba  da tafiya  cikin Isa da  izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa  wani  yawu ta hadeye   tana  qoqarin daidaita  numfashinta da  natsuwarta  ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa  yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta  shiga d’aga ka’fafunta  kmr walkiya ya nemeta  ya rasa Yana nan tsaye su anas  suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa  kowanne ya kama gabansa kasancewar  kowannensu akwai bangaren  da  yafi so  .”


Tsaye   tanweer    tayi  aguri d’aya  kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda  ta tsinci kanta a yau din nan ,  ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi  akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya samu guri ya zauna  akan  d’aya daga cikin fararen kujerarun dake gurin  ta waiga bangarenta  na dama tsaye  taga  wasu  matasan   mata  su  biyu    akan  stage  daya  sanye  da kaya  wando da riga yellow dinki gbamu gbamu ka’fafunta sanye da sander  shima baki hannunta rike da speaker  tana rera waka yayinda yaranata ke mata amshi  dayar mata  itama sanye da wando da riga sai dai nata  kalar ja ne gbdy  haraban gurin   shirye  yake  da  fararen kujeru da table a tsakiya .”
tun daga nesa mawakiyar  ta fara bud’e hakoranta dan ganin anas  na shigowa nan take salon wakar ya canza salo  ta soma  masa waka tana sake fad’ada fuskarta da  murmushin  irin nasu na gogaggun  yan  duniya  Shima  murmushi ya sakar mata  sannan  ya soma   qarasowa  Inda take itama ta nufo shi   suka rungume juna har da kiss ta manna  masa a goshi    kana  ya  nufi gurin  empty  chairs   ya samu  guri  ya  zauna zamansa ke da wuya  ma’aikatan gurin suka qaraso garesa  tare da kwalaben giya da soyayyen nama da yaji yaji   domin sun san irin abinda yake bukata kenan  sa’banin  jaguwa da malt  kawai yake sha idan yazo.

“subhanallah  tanweer  ta furta a ranta tana  mamakin  “wai yau itace a irin wannan  gurin wasu hawaye ne masu zafi  sukayi nasarar biyo gefen fuskarta tana k’okarin sharesu jaguwa ya  qaraso gabanta yana girgiza mata  Kai alamar kartayi kuka sannan ya  rungumota  jikinsa ta kwantar da kanta a faffadan qirjinsa dake fitar da sihirtaccen  kamshi , cikin tsananin  tashin hankali yasa hannunsa ya share  mata    hawaye  ya  sake rungumeta  tsam yana zagaye weist dinta da hannunwansa duka wani irin tsalle hade buguwar zuciya tanweer tayi  Wanda har hakan ya  haifar mata da tsayawan numfashi na wasu yan  mintuna haka duk wani tunani dake tafiyar da bugun zuciyarta sai daya motsa ta dinga Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta.
yau ce rana ta farko da jaguwa ya rungume mace acikin mutane batare daya    ji   komai ba ajikinsa  hasalima wani  sanyi  yaji yana bin jijiyon jikinsa ,bakinsa ya Kai cikin kunnenta yana mata rad’a  wanda hkn yasa tsigar jikinta tashi  “kukan ya Isa haka please  kar zazzabi ya kamaki ”  cike da muryar kuka tace “me yasa ka kawo ni nan  ? shiru yay mata  tausayinta na kamashi  ya  d’ago  fuskarta  suna kallon kwayar idanun  juna can ya motsa lip’s dinsa “baki so mu wuce na mai dake  gida  yanzu  ?shiru  tayi ta  cigaba da kallonsa  yayinda zuwa lokacin  idanun mutane sunyi caa akansu ciki  kuwa  har  da  abokansa  da  alqali daya samu nasarar  shigowa  “kiyi min magana idan baki bukatar kasancewa damu  anan na mayar dake ” nan ma shiru tayi hawaye na sake  zubo  mata masu zafi da radadi “wai  kasancewa dasu ko su dawa oho masa ?tafiya ya soma yi daita tana makale ajikinsa har ya Kaita kan table din  daya fara zama ya zaunar daita a hankali .
kuka tayi sosai taki  yin shiru  yayi  mata magana yafi sau goma dan gbdy ya manta Kansa a gabanta  sai wani narke mata  yake zuciyarsa na sanyi akanta  sannan baya son rabuwa daita   shiru  tayi kawai tana makale ajikinsa  tayi  yawo  kasashen duniya sosai  amman bata ta’ba Kai kanta irin wad’an guraren ba sai gashi a kasarta ta tsinci  kanta da kyar ya rarrasheta  tayi  shiru ya bude mata kwalban malt  ya  Kai bakinta idanunshi na kanta  . suna  nan  zaune mawakiyar  ta fara bin Site by site  tana waka yayinda  mazauna  kan table   suka dinga mata liki har ta k’araso table din da jaguwa ke zaune  bai daga idanunshi ya kalleta ba sai anas ne ya taso daga mazauninsa ya shiga lika mata ‘yan dubu day day ta dan durkusa tare da furta “thank you sir shiyasa nake son ganinka  sannan ta tsaida wakar tare da cewa ayi mata tafi nan take gurin ya d’auki tafi raf raf  banda jaguwa da tanweer , sautinta ne ya cigaba da karad’e gurin anas  ya tashi yana layi ya shiga rawa bayan ya gama rawa ya nufi gurin zamansa Yana rawa  aikuwa makiyar  ta biyosa nan gurin ya hargitse da dariya har shi   anas  din  dariya yake sakamakon ya fahimci abinda take bukata daga garesa kudi take so ya fito da bandir din  kudi ya shiga lika mata yana rawa irin tasu ta mashaya .”

Yammata  ne  su uku  zaune  acikin  runfa  me  zagaye  da wutar lantarki sai  tsirarun bishiyoyi   kowacce  daga cikinsu hannunta rike  da  karan    sigari da  glass cup dake cike  da  ruwan  giya “Kalli   d’an  iskan mutumin nan , ai na sha fad’awa  sweet  zahra  ta fita  hanyarsa  ta  tsaya taci  lokacinta  taki kamar jijiyarsa ce kadai ke da dadi , “ai  Ina  ganin sai  ta  tsinci  kanta a lahira  zata  gane  matakin  daya dace daita , sam  taki yarda tayi  muamula da masu bukatarta  inji cewar helen  “kyale  banza yanzu  dey  kirata tazo ta ganewa   idanunta  wata Killa  tasan  Inda  ke mata  ciwo  wallahi tunda ta had’u  da mutumin  nan komai nata  yayi  qasa Ina dalili  inji  cewar   hafcy no-no suna cewa mata haka kasancewarsa tana da  dukiyar Fulani over  “haka  za’a yi  hafcy  bari na kira shegiya ta bud’e jakarta ta  ciro wayarta  kira d’aya  zahra ta d’aga wayar   cikin  fara’a”   sweety nah  dake  haka  suke Kiran junansu  dashi “yes sweet  Helen  meye labari ne  ? ta  amsa mata   ciki fara’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button