KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“mai zai sa zai zama haka “?babu yadda adnan dina zai zama dan fashi yafi yarda tabin hankali ne ya samu yarinyar nan amman babu ta yadda zai zama haka mutumin kirki ne mai dattako da tausayin da taimako da jin tsoron allah bazai iya satar ko silibiyar din wani ba bare ya zama rikakken dan fashi mumy ta kallesa “tunda danuwanka ne sai ka kai ni gurin mahaifiyarka ko mahaifinka na gansu su ganin sannan suzo suga illar da dansu yayiwa rayuwar diyata .”
“Haka zalika duk maganar da tanwer ta fad’a gaskiya ne adnan dan fashi ne domin nima nan sheida ce tunda dalilin wa gidanmu fashi yaga diyata ya saceta ya wuce daita tsawon lokaci muna nemanta bai dawo mana daita ba sai daya gadama allah dai ya shirya mana zuria kawai yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba .”

Cikin tsananin kaduwa dr sadiq ya dubi mumy yana girgiza mata kai sannan yace “ muddin adnan din danasani ne wallahi wallahi wallahi !!! ba dan fashi bane soja ne ba kuma zanyi kafara ba allah bazai sa ya zamo haka ba “kamar yadda ka fad’a haka soja kanina ya fada min muddin adnan din da sukayi karatu tare dashi ne soja ne saboda ni ina da hotonsu da suka dauka agurin traning lokacin dana fara ganinsa yazo duba tanwer na kirasa na tamvayesa wannan kalmar da ka fad’a shi ya fad’a min amman taya zan yarda da maganarka da maganarsa tunda ni sheida ce yayi mana fashi .”?
tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shi kuma dr sadiq yana auna dalilai har da zai sa adnan ya kasance haka “kai ban yarda ba akwai dai abinda ke faruwa “wannan ba zargi bane ba kuma karya bane abu a zahiri yake kowa yasani ka dai je kayi bincike da kyau danuwanka wannan sana’ar yake yi ku dai yana fakaice muku da shi soja ne amman gaskiyar labari ba …” wani qara tanwer ta saki tana toshe kunnuwanta duka yasa mumy ta katse maganar ta cikin karaji ta soma magana “mumy bana so jin komai qirjina zai fashe doctor zo kayi min allurar mutuwa ,dan allah ka taimakeni kamin allurar mutuwa bana son wannan rayuwar ta fara ihu tana fixge fixge dole sukayi kanta suka rirriketa .”

tabbas akwai lauje cikin nadi dan zuwansa hudu gidan malam mudi bayasa samun ganinsa kuma lallai idan shi din soja ne ya kamata duk tsawon kwanakin nan sun samu wani labari dr sadiq yayi shiru cikin tarin tunane tunane ya dinga maimaita sunan adnan bai sake cewa komai ba ya zubawa kasan tayis ido babu wanda zai fitar dashi daga halin da yake ciki sai malam mudi dan haka yau komai zai faru sai ya hadu dashi yana nan tsaye har akayiwa tanwer allurar bacci sannan ya soma daga kafafunsa da kyar yana tafiya yayinda mumy ke biye dashi lallai sai tayi ido hudu da iyayensa su san abun yi dan bazaa bar mata diya cikin tashin hankali ba shi sam bai ma lura tana biye dashi ba sai daya ji saukar muryarta a bayansa .”

“Ka daga idanunka ka kalli abinda ake nunawa a tv dr sadiq ya dago idanunshi da kyar zuwa ga makeken tv dake manne ajikin bangon reciption ya kura masa ido yana dubansa da farko hotun bana fuskarsa bane na wata fuskar ne dabam amman wanda aka nuna na headquarter nashi ne shakka babu adnan dinsa ne hannuwansa da wuyansa makale da sarka .”hawaye suka cika idanunshi yau wanda yake matukar qauna wai shine cikin wannan halin sai yaji kamar bai amince ba wani abu ne dabam sai kuma zuciyarsa ta amince .”

ya kalli mumy banyi tsamanin haka zai yiwu ba sam sam wannan rayuwar bata cancanta dashi ba ya fad’a a fili cike da takaice yana sake maida idanunshi ga kallon tv inda aka cigaba da nunawa da yadda mutane suke ihun basu yarda ba idan ma ya aikata hakan ayi masa afuwa hawaye mai tsananin radadi suka zo masa “itama abinda tanwer take fad’a kenan kullum wannan aiki bai dace dashi ba amman tabbas aikinsa kenan tare da yaransa .”

Allah sarki ammi koya zataji allah yasa bata ga wannan haskawar daakayi ba dan duk kwananki lafiyar jikinta yaki samuwa kullum da damuwa da ambaton sunansa take yini da kwana jiya tana masa kuka take fad’a masa “babu wani jin dadin da zanyi a duniyar nan idan na rasa adnan kullum adduata ta rigasa mutuwa domin bazan iya jurar rashinsa ba “ka natsu mana sadiq ka yarda cewar danuwanka ya aikata haka hakika duk mai tunani yasan akwai wani abu a kasa tun saninka da danuwanka a matsayin soja a shekaru dayawa tun lokacin yana karatu a kaduna ka ta’ba ganinsa da uniforma koda t shirt na soja.”?yayiwa kansa wannan tambayar shi kansa bai san iya lokacin daya dauka agurin ba cikin wannan halin kafin daga baya ya dinga daga kafafunsa da sukai nauyi da kyar yake dagawa mumy na biye dashi .”

A haraban hospital suka hadu da dady ya tsaidaita lokacin har dr sadiq ya shiga motarsa yana qoqarin bata wuta “ina zuwa haka “? gabadaya ta diririce tana nuna masa motar dr sadiq lokacin ya figi motar da mugun gudu “likinta da zai duba tanwer ne kuma danuwana adnan dinta ne uwa daya uba daya nan tashiga zayyano masa bayani abinda ya faru yay shiru yana bin hanyar da motar tabi kafin a hankali ya sauke naunayen ajiyar zuciya yace “kenan iyayensa ma suna cikin garin nan “?da alama kam numfashi ya sauke sannan ya riko hannunta “muje ciki nayi miki bayani yadda mukayi da alhj bello .”

Misalin karfe biyar na yammacin ranar suka isa dashi wani babban asibiti suna isa aka bude masa murfin kofar blackmaria da kyar ya yunkura ya mike saboda nauyin da kafafunsa sukayi ya fito polisawa na zagaye dashi tundaga nesa me gidansa ya gansa ai kuwa hankalinsa ya tashi matuka ,kai tsaye wani daki aka shiga dashi likitocin asibintin suka dakatar da polisawa tare da cewa “aikinku ya qare .”
cak suka tsaya wasu har sun fara juyawa mai gidansa kawai aka bari ya shiga inda yake kunnensa kunnensa manne da waya “godiya nake minister bazan manta da wannan taimakonka ba idan na gama da nan zan zo muga juna ya katse kiran ya qarasa gaban gadon daaka kwantar da jaguwa ya tsura masa idanunshi yana dubansa, ba wani abu ne ya firgitar dashi ba kamar ramar daya ga yayi gashi yayi baki ya zauna akan kujera dake ajiye .”

a hankali jaguwa ya bude idanunshi sakamakon jin kamshin turarensa alamun ya qaraso ,lokaci guda wasu zafafan hawaye suka fara zubo masa bisa kuncin ya kallesa kawai bazai tuna when last ya zubar da hawayen bakinciki haka ba ko dukan daya sha a hannun polisawa bai sa ya zubar da hawayen bakinciki irin wannan ba.”
lokaci guda ya dauke kanshi akansa dan shi kadai yasan abinda yake ji cikin ransa cikin karayar zuciya ya daure da kyar ya bude bakinsa amman kuma ya kasa furta komai sai hawaye kawai ke fita saga idanunshi su anas yake son a taimakawa kar su mutu a maboyarsu amman bakincikin abinda me gidansa yayi masa ya hanashi magana.”

A hankali ya sake dubansa cikin dauriya da karfin hali irin wanda bashi da zabi ya fara magana “sir su Ana’s suna underground duk tsawon kwanankin da aka kama ni suna gurin babu wanda yasan suna gurin na kasa samun natsuwa ina tausaya masu domin ni ne silar faruwar komai watakilla ma zuwa yanzu sun mutu duk yadda yaso ya daure bai samu ba , lokaci daya hawaye suka fara sauka kamar indararo babu kaukautawa hankalin me gidansa ya qara tashi ya fara goge masa hawaye da hankcy dinsa tare da bawa likitoci damar suyi masa allura bacci sannan su fara dubansa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button