KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Yau ma kamar jiya a bakin kofar shigowa falon ya tsaya yana sallama ta leko daga kitchen tana yi masa sannu da zuwa ,ya amsa yana cigaba da tsayuwa agurin yana kallonta cikin doguwar riga ya kashe masa idonsa daya “me kike jira da bazaki karaso ki tarbi mijinki ba tunda Kinsan abinda tsayuwatsa take nufi ?”kai ya anas!
“Kai ya Ana’s ko gskiya ina jira ta koma cikin kitchen din ta wanke hannunta ta fito ta tsaya a gabansa cike da shagwaba ya dage mata girarsa daya ya janyota kusa dashi sosai ta fada jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana sakin numfashi sai daya gama jin dumin jikinta sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya hade bakinsu guri daya ya shiga tsotsa “bayan runguma har da wannan nake bukata okay.

Ta zare jikinta taja shi zuwa ciki sosai ta zaunar dashi akan kujera tana shafa fuskarsa “ina ka tsaya yau ka dade ,ina tare da adnan tun fita ta bari na kawo maka ruwa ka sha da alamun akwai gajiya atare da kai ta mike ta shiga kitchen ta dauko ruwan gora mai sanyi da cup ta fito ta tsiyaya ta mika masa ya amsa hade da hannunta yana dubanta itama shi take kallo ya zaunar daita a cinyarsa ya kai cup bakinsa ya sha kadan ya mika mata ta ajiye cup din akan table “ki shirya gobe zan kaiki kiga ammi ,da gaske ta fada tana zubewa jikknsa gskiya naji dadi sosai amman kwana zanyi ko ?ya riko hannunta cikin nasa yana kallonta “kwana my princess?ta gyda masa kai “idan kika kwana ni kuma na kwana dawa?ta marairaice masa fuska ,kiyi hakuri kije kiyi ma ammi yini na rigada na saba kwana ajikinki amman idan ki yarda kawai sai mu kwana tare tayi saurin zaro ido waje ,yes dan gsky bazan iya kwana ni kadai yanzu ba “.

“Shikenan naji amman sai dare zakazo ka daukeni ?ya dage mata gira ,muje kayi wanka kaci abinci ,
Wanka dai amman abincin nan no space kamar jiya suna tsaka da hirar soyayyarsu aka kira sallah ya fita zuwa masallaci a daren ma kwanan farinciki sukayi rungume da juna sabanin tanwer da adnan .
washegari da safe ta tashi ta hada musu break suka ci suka fice ya bude mata gaban mota ta shiga ta zauna ta rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar suka bar gida bini bini zai jiyo ya kalleta sai murna take zata gida ,ya lalubo tafin hannunta cikin nashi yana murzawa yana janta da hira da tsokana har suka karaso unguwarsu yayi parking adaidai kofar get din gidansu zata bude bangarenta yayi saurin cewa “no my princess bari karki wahalar da kanki ya fita da sauri ya bude mata a hankali ta fito ya kulle motar suka jera suka shiga gidan ,”

A haraban gidan anas yaja ya tsaya ta shiga falon bakinta dauke da sallama ammi na zaune bisa kafet ita da haseera suna breakfast ammi ta dago ta kalleta ta kuma kalli bayanta “ina bin malik din yake ?ta karaso ta tsugunna a gabanta tana gaisheta ammi bata damu da ansa gaisuwar ba ta sake tmbyr anas “yana waje ammi ta bata rai “dan sakarci irin naki me yasa zaki bar min yaro a waje maza ki tashi kice ya shigo cike da mamakin irin wannan qaunar da ammi take masa ta mike tana riko hannun haseera “aunty hasera ya kwana biyu ?Lafiya lau auta duk kin wani canza kinyi kyau Kmr wata india tayi murmushi ta nufi kofar fita ta tsaya a gabansa “muje ko dan kasa mamanka tana min fada tai mgn tana zumboro masa baki yayi murmushi ta juya yana biye daita .”

Cike da ladabi da biyaya ya shigo bakinsa dauke da sallama ammi ta amsa tana fadada fuskarta da murmushi dan shima yayi kyau kamar yadda diyarta tayi hally ta dauko dadduma ta shimfida masa ya zauna kusa da ammi “anas ya aiki da hakuri da auta ? Alhamdullahi ammi babu abinda zance sai Godiya hasera na kallonsa amman bata ce masa uffan ba abun ya dan tsotsa ran hally shi dake mai saukin kai ne yace “hasera ina yini fuska a hade ta amsa da “Lfy! atakaice dan gani take har dashi acikin masu zuga adnan kar ya aureta hasera ta maida hankalinta gurin hally “hally uwar kyau wannan ai kinfi karfin akiraki mai kyau sai dai uwar kyau hally tayi mata banza “kinga kuwa yadda kika kara kyau kika murje?da kyar tace “na gode mumy kuwa abincin gabanta ta turawa Ana’s tana bashi umarnin yaci babu mutsu ya fara ci hally tasan ya koshi amman bazai iya mutsu daita ba ta tsura musu ido kawai tana jin dadin yadda ammi take qaunarsa byn ya danci kadan suka koma kan kujera suna hira ita ammi da anas da ita kanta hasera sunyi hira sosai cikin haka anas yayi wa ammi sallama ya ajiye mata kudi bandir din yan dubu day day na 50k “ga wannan babu yawa ni zan wuce ,haba anas har da wata hidima?babu wani hidima ammi ki samin albarka shine abinda nafi bukata daga gareki ,allah yayiwa rayuwarku albarka gbdy ya daukakaku a idanun duniya ya rufa muku asiri duniya da lahira Ameen ammi na gode sai anjima ya sa kai zai fita hally ta biyo bayansa domin masa rakiya ,”

A haraban gidan haseera ta samesu kamar zasu shige jikin juna ganinta yasa suka dan bawa junansu tazara ta karaso tana cewa hally ki dan mana exuse bata damu ba sai ma shigewa ciki da tayi haseera ta gyara tsayuwa tana tsura masa ido “ada tunanina kana cikin wadan da suke zuga adnan akan kin aurena amman a yanzu na fahimci Kai mutumin kirki ne sannan nasan kasan matsayin da nake dashi azuciyar abokinka ko zan iya sani wani abu karka min karya ka fad’a min gsky sbd allah ?” yayi shiru yana kallonta d’an ta dauresa tunda ta kira allah ,
“Adnan yana da burin aurena ko kuwa wata can yake da burin aura?Kamar yace mata eh sai kuma yayi shiru” idan ma bashi da burin aurena gara ya fada nasan matsayina ba nayita jiran gawon shanu ba “kibi komai a hankali haseera Kinsan shi alamarin na aure nufi ne na allah da zarar lokaci yayi kuma kece matarsa zaa yi idan bake bace haka zaki hakura“.

“Bama zai zamo bani bace matarsa dan da yaje ya kwaso wata gara ace nice zan shiga gidansa kai ni aurensa ko ba alkhairi bane ina rikon allah ya mallaka min shi yayi shiru yana kallonta yana hadiye wani dunkukallen abu daya tsaaya masa a makoshi
“jikina yana bani zuciyarsa naga wata amman nasan kowacece bazata fini da komai ba sannan bazata zamo min natsala ba ,ga sako ka fada masa idan ma zai dawo da hankalinsa gareni yayi idan bazai dawo ba sai dai ya mutu bai yi aure ba amman ko zanyi yawo tsirara sai na zama mata agidansa domin shi din nawa ni kadai , idan baka sani ba na fada maka wani abu mahaifina ne ya taimaka masa har ya kawo matsayin da yake a yanzu amman dake shi dan adam masu manta alkhairi , yanzu kai a ganinka ya dace sakayyar taimako da mahaifina yayi masa ya fada akan wata bani ba …?

Sai allah ya kaimu byn sallah ayi sallah lafiya karku manta da naman sallahna lol love you guy’s

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button