KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a matukar  wahale suka k’araso  gida  jaguwa  yay  saurin fitowa daga cikin mota   ya  k’arasa  da sauri  ya  bud’e  kofar shiga cikin ainihin falon gidan , su  jubi  suka  kamo  kamil  suna tafiya  dashi a hankali kafafunsa babu takalmi dan tuni sun cire masa tun acikin mota ,Kai  tsaye suka  nufi hanyar  falon   jaguwa  na mussaman dashi    suna  masa sannu,  a hankali suka kwantar dashi akan wani k’aramin  madaidai  gado wanda daman an tanadesa domin irin haka  ,kamil  ya runtse idanunshi saboda azabar ciwo , cike da hanzari jaguwa ya nufi Inda first aid box dinsa  yake ya d’auko  ya  dawo da sauri , eku ya janyo masa kujera  ya zauna  a gaban kamil yana masa sannu  .”

jin  motsin  shigowar motocinsu  da  maganar  wasu  daga cikin yaransa   sama  sama  yasa tanweer  lalla’bowa babu takalmi  a ka’fafunta tai hanyar  babban   falon   gidan    tana  bin bango tana  qarasowa bakin kofar falon ta tsaya  a hankali ta bud’e kofar ta shiga  bata   ga  kowa  a falon ba,  kasa  kasa  take jiyo  magangansu  , kawai   ta nufi   wani  dogon  korido  Inda  take  zaton daga  nan sautinsu yake fitowa  , a hankali  ta tsinci kanta acikinsu   kowannensu cikin tsananin tashin hankali , jaguwa  zaune a gaban kamil   cike  da tausayawa  yana k’okarin  cire   masa   harsashi . binsa tayi  da kallon mamaki  qirjinta na wani irin bugawa da matsanacin karfi shafa  idanunta   tai  hade da runtsesu  na second biyu sannan ta bud’e tana sake  sauke idanunta akanshi wanda zuwa   lokacin har yay nasarar  ciro bulet   din  yana kallo sannan  ya  saka acikin  farantin  silver dake rike a hannun jubi, yayinda sauran ke zaune cikin  tsananin tashin hankali gbdy idanunsu ya rufe babu wanda hankalinsa ya Kai Inda take tsaye .”

naunaye ajiyar zuciya  suka sauke lokacin  da jaguwa ya  cire wa kamil bulet  ita Kuwa tanweer zuciyarta ta shiga rawa had’e da tsinkewa  .”me zata  gani  yau ? daman likita ne shi  ko kuwa mafarki  take  ?   yes  wannan ba  mafarki take ba shine tagani  zaune  ya cire  bulet a kafar abokinsa, kasa tayi da idanunta tana kallon bayansa nan  idanunta ya  hango  bindiga pestol  soke a abayan wandon  jaguwa  ,nan   take ta  sake fita  daga  haiyacinta “bindiga ….! ta furta a kasan ranta ” me   Kuma yake  yi  da bindiga ? ya  Allah karka sa  abinda  zuciyata ke hasashe  akansa ya zama gaskiya dan bai cancanci haka ba ” wani kuka ya kufce mata   ta juya da sauri tana  shesheka   wanda  hakan  yasa  gbdy suka   d’ago suka ganta tana sarsarfa  , cike da matsanacin firgici   suka  tsura ma jaguwa   Ido    dan  jin abinda zai ce  bai yi magana ba haka zalika bai  nuna alamun  damuwa atattare dashi   ba , ya  mike  tsaye yana
furzar da numfashi tare da yiwa kamil sannu” ka kwanta ka huta kafin  akawo maka abinci ya gyada masa Kai  yana cewa” na gode abokina Ina alfahari da Kai ,nima haka   .”

jubi  ya dube jaguwa  yana cewa  “wallahi ban  ta’ba   shiga tashin hankali  ba irin na  wannan  lokacin na tsorata  matuka   na sadaukar zamu rasa  kamil  “ba  kai kad’ai ba inji cewar anas  tafiya  jaguwa  ya  fara a hankali   suka  biyosa   a baya  har gurin   shakatawarsa    “da’ace  sunyi nasara akanmu   zamu  iya rasa rayukanmu gbdy”. sai lokacin jaguwa ya motsa lip’s dinsa   “ina ai sai dai idan  tawa ta kare sannan zaku iya shiga  wannan  hali  amman muddin Ina tsaye akan kafafuna babu wanda zai yi  nasara  bare har mu rasa rayuka ”  ya  karasa maganar  tare da  tsayawa  cak ya  rike  karfen  runfar dake  kafe acikin   gurin  shakatawar , “hakika Nima na karaya  inji cewar jabir  ” Karku  ta’ba rungumar  Karaya arayuwarku duk halin da zamu shiga karku karaya saboda    rashin samun nasara  ba namu bane ,a duk lokacin da naga Kun Karaya  sai  naga kamar tun asalin ku din ba jaruman gaske bane, sannan baku ne jarum da mukayi gasar mutuwa dasu  ba  .”

murmushi sukayi gbdy suna sauke numfashi  “uhm wannan fa ba kamar gasar mutuwa bace  ,gasar mutuwa kowa yasan  mun saida rayukanmu ne dan biyan bukatarmu  wannan fa ?”bayan sai da rai har da  tozarci  zamu  janyowa  gangar  jikinmu  idan muka tsinci kanmu a hannun jami’an tsaro “.anas ya karasa maganar yana  dafa kafad’ar  jaguwa  “yanzu dai barkanmu  allah  ya k’ara karemu  .” ameen  jaguwa  ya fad’a acikin zuciyarsa.   “ka zauna    kana bukatar  hutu, jaguwa   ya  zauna  akan d’aya daga cikin kujerun gurin yana lumshe idanunshi ” me za’a  kawo maka ka d’an sha ? ya  girgiza  masa  Kai  alamun bai   bukatar komai , zama  anas yayi kamar yadda sauran abokansa sukayi  yana cewa  “ya za’a yi da wannan  yarinyar ta rigada taga komai , koma nace  taji wasu abubuwa akanmu ? ,yana  d’aya daga cikin abinda yasa kaga  banason yarinyar nan agidan nan “.”me taji ?.”Ko me mu kace ?yay masa  tambayar a dan kufule ” idan Kuma taji taji kenan shikenan daman abinda  take bukatar sani kenan  tasan su waye mu ” ya k’arasa maganar yana jan  dogon tsaki tare da  jin bakinciki  da takaici, haka nan Kuma ya tsinci Kansa da Jin fad’uwar gaba mai tsanani “.

Koda tanweer ta koma d’aki  ta kasa  tsaye ta kasa zaune sai zariya take  acikin d’akin  ita kad’ai, ta saka wancan ta kwance , kwakwaluwarta ta shiga tunani mai zurfi, babu abinda zuciyarta bata kisama mata ba akansu , abu uku  zuciyarta ta tsayu akansa  shi din  dan fashin ne  ko Kuma jami’in sirri ,ko  likita ,  idan ba haka ba me yake yi da bindiga ajikinsa ?  ta kasa hakuri dan  haka ta sake fitowa tai hanyar boys quarter nan fa hankalinta ya sake tashi ganin yadda yaran jaguwa  ke fitowa  da manya  bindigu suna adanawa a maboyarsu ,mutuwar tsaye tayi har sanda suka kwashe komai  suka  d’auki  katuwar jakar kudin da suka shigo dashi  suka nufi hanyar Inda jaguwa yake tare da abokansa suna tautaunawa ,  cike da matsanacin tsoro ta biyo bayansu  a tare suka k’araso ta ra’be jikin wata bishiya kasancewar yaran jaguwa  suna   gabanta yasa jaguwa da abokansa kasa ganinta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button