KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

mintuna kaɗan ta dawo hannuta ɗauke da tire Wanda ta jera plet din abinci tana ƙoƙarin ajiyewa jabir ya ɗauki ruwan daya sa daya daga cikin masu aikin gidan ta kawo musu shi ya kafa a bakinsa , kuwa jaguwa cikin wani irin salon mugunta yasa ƙafarsa daya ya daki kasan tiren tun kafin ta k’arasa ajiyewa take tiren abincin yayi sama ya zube ajikinta, kwanuka suka tarwatse duk jikinta ya ɓaci da jollof din macaroni gabad’aya su jabir suka juyo dan daman basu juya duka ba suna bukatar ganin abinda ke faruwa , cike da izza yake kallonta itama kallonsa take kamar zatayi kuka ,dariya taso bashi saboda yadda tayi da fuskarta sai dai yayi kokarin had’iye dariya dake neman kufce masa , muryarsa a kasanlance ya soma magana ” babu abinda zanyi da wannan banzar abincin na gidanku, nayi haka ne dan na wahalar dake sannan wannan ne lafiyayyen abinci ?”irin wannan abincin uwarki take dafawa ubanki ? yayi maganar kamar ba daga bakinsa ya fito ba wallahi wallahi sai kinyi da kinsanin marina a rayuwarki ya dinga zazzaga mata balai gaba-daya ta rikice sai lokacin iyayenta suka fahimci abinda ya faru a dakin , Anas ya tsaya kawai yana kallon jaguwa dake maseefa abinda bai taɓa ganin yayi ba a tun tasowarsu wannan shine karo na farko cike da kuzari ya mike ya damki bayan wuyanta ya nufi hanyar fita daita, nan iyayenta suka shiga bashi hakuri gang d’insa suka soma shirin fita still Jaguwa na rik’e da wuyan tanwer “Please dan Allah kubar muna ‘yarmu karku kashe min ita bani da kowa sai ……”.

“Shhhh! yayi saurin katsesu tare da cewa “tare da ita zamu tafi idan kuka yi kuskuren sheidawa police tabbas zaku rasa d’iyarku har abada ” Jaguwa ya fad’a tare da fusgar Tanweer wacce tunda suka fito idonta ke rufe saboda tashin hankali, jin da tayi zai tafi da ita yasa ta bud’e idannunta ta soma ko’karin gudu, cak Jaguwa ya d’agata ya da’ura a saman kafad’arsa tana ihu tana kiran suna iyayenta tana dukan bayansa sai dai bai direta a ko ina ba sai a cikin motarsa, pito jabir yayi da bakinsa duk suka hallara suka shiga motocinsu suka ja da k’arfin gaske ..

Hajiya zainab najin barinsu gidan ta soma buga kanta da kujera tana ihu tana kuka “shikenna sun tafi min da yarinya minister ya mike ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa ya soma zagaye parlou’n yana neman number police ta mike a firgice ta fixge wayar tayi jifa dashi ” idan ka kirasu zasu kashe min yata shikenna na saura bani da kowa ta karasa maganar tana zaman dirshan a kasa tana dukan cinyarta , ya karaso gareta ya dafa kafad’arta “ki kwantar da hankalinki dole sai hukuma tashiga cikin wannan matsalar babu abinda zasu yi sun fadi haka ne saboda su tsoratarmu yana gama fadar haka ya mike ya sake ɗaukar wayarsa ya kira number IG cikin Sa’a bugu daya ig ya ɗauka ko cikkake minti goma ba’a yi da tafiyar su jaguwa ba police suka karaso har da Ibrahim daya amsa Kiran minister sun so subi bayansu Hajiya zainab ta hanasu tana tabbatar musu da abinda yan fashi suka sheida mata “wannan ba wani abun damuwa bane zamu san abin yi ina Camera gidan take ta haka zamu samu sauƙin bincike ,kai tsaye minister yayi hanyar waje dasu yayinda Ibrahim yayi mutuwar tsaye qirjinsa na wani irin mahaukacin bugu ,nan police suka shiga bincike gidan sai dai babu wata hanya dasu jaguwa suka bari domin ganosu sun bata komai jinjina kai sp yayi “wadan nan yan fashi sun san abinda suke sannan sun kware matuka a gurin taaddanci sai dai duk da haka zamu san abun yi suka ci-gaba da zagaye gidan inda suka dinga cin karo da polisawan dake tsare da gidan a kwance da alamun wani abu aka shaka masu …..

Wani irin gudu motocinsu ke yi a saman titi kamar zasu tashi sama yayinda Tanweer take wani irin kuka a jikin Jaguwa har da cizonsa sai dai ko gezai bai yi ba ganin ta damesa yasa yayi mata mugun bugu a kafad’a nan take ta sulale ajikinsa ta sume kamar matacciya bata k’ara sanin inda kanta yake ba har suka iso gidansa ,Jabir yayi ko’karin da’ukarta zuwa ciki Jaguwa yayi saurin dakatar dashi ta hanyar buga masa muguwar tsawa ya zaga da kansa ya d’auketa ya sabata a kafad’arsa zuwa cikin gidan.

“Meke damunsa ? me yasa ya daukota?”Jabir ya tambaya Anas dake tsaye kusa dashi yana ƙoƙarin cire face marks din fuskarshi “Uhm nifa Ina tsoron kar dauko wannan yarinyar ya samu a matsala fa yar Minister ce… “Shhhh! duk Ku yi shiru boss yasan me yake ba abunda zai faru” Anas Ya basu amsa yana cire Safar hannunsa duk suka kalli juna da sauran da kusan a tsorace suke sannan suka nufi wani bangare na gida da jakunkunan kudi ..

Kai tsaye d’akinsa ya wuce da ita direct ya k’arasa da ita bakin makeken gadonsa ya shimfid’eta kamar wata baby yana ko’k’arin d’agowa idannunsa suka Kuma fad’awa kan ‘yan nonuwanta da rigar baccinta ta janye zuwa gefe guda har yana iya ganin kan nipples dinta dake tsaye cikakku gwanin burgewa.
Wani irin yawu ya had’iya Kamar wanda aka taba yayi saurin mik’ewa yana mai runtse idannunsa na second biyu sannan ya bud’esu ya sake k’ura mata ido , yarinya ta had’u sosai ya furta hakan a kasan ransa , girgiza kansa yayi ya shiga bathroom dinsa dake manne da d’akin ya dibo ruwa a cikin roba ya dawo ya zauna kusa daita ya shiga shafa mata ruwan a fuskarta zuwa qirjinta ,a hankali ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta cigaba da sauke numfashi da kyar ,fuskarta tayi jazir saboda kukan data yi, gashin kanta ya kwanto gefen fuskarta ,sauko da kyakkyawan idanushi ya yi akan cinyoyinta dake waje a dalilin rashin sakowar rigar baccin sosai , Kallonta yake har sanda ta takure jikinta guri daya tana turo masa karamin bakinta ya kai hannunsa ya ja blanket dake gefe ya rufe mata jiki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .

sanyin A/c d’in dakin yaji yayi yawa ya d’au remote ya rage maimakon ya fita sai ya tsinci kanshi da zama kan side chair dinshi me laushi da kyau, fuskarshi na fuskantarta har wani lumshe ido yake yana cigaba da kallonta kwance a takure yayinda numfashinta ke sauka a hankali ya jima zaune daga bisani ya kashe light d’in da’kin sai hasken corridor dake haskata ,cike da jarumta ya soma cire kayan jikinsa ya nufi bayin ya tsaya yana sakarwa jikinsa ruwa bai dade ba ya fito ya sauya kaya ya fita daga dakin zuwa wani dakin dake kallon wanda take kwance ya kulle kansa daman kuma ka’ida ne duk sanda yayi operation Sai yayi wannan wanka tare da kebe kanshi .. .

Washegari

A hankali ta soma motsa idanunta da mika har ta farka tana buɗe idanunta kadan kadan , ganin inda take yasa ta karasa bude idanunta da sauri, tana kallon dakin data tsinci kanta , babu abinda babu na more rayuwar duniya ,ga wani sihirtaccen kamshi na musamman dake tashi mai haɗe da sanyi ac lokaci daya zuciyarta tayi wani irin bugawa da karfin gaske runtse idanunta tayi saboda motsin taɓa kofar dakin data ji anyi dan bata son ganin fuskar mutumin daya daukota daga gidan iyayenta , tsawa taji an buga mata “ke dan ubanki zaman me kike yi fito min a daki cike da razana ta bude idanunta wanda ta gani tsaye a gabanta ne yasa ta zaro idanuwanta waje cike da mamaki , yana tsaye a gabanta rike da gefen kugunsa ya haɗe gira sama data kasa idanunta ta murza domin tabbatarwa kanta mafarki ne ko kuwa a zahiri shi take gani a gabanta …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button