KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“akan me Kenan kike min addua ? “akan alqalla fashin da kake ta sake subutar baki dan sam bata iya karya ba ,koda ake cewa duk wanda yabi maza zai yi karya ,zai yi sata zahra bata iya karya ba sannan bata sata barta dai da bin maza suma masu lasisi manya mutune manyan yan siyasa da manyan kusoshin gwanati ” .
yayi shiru Kawai yana cigaba da sauraronta tare da nemna Karin bayani “shiru tayi jikinta na sake d’aukar rawa gbdy ta daburce ta dawo tamkar wawiya agabansa “na shiga uku meye haka nake yi ? “
“me yasa na fad’a masa nasan sana’arsa ,ba abinda ya kawoni Kenna ba , dan dole na nemawar kaina mafuta tun kafin ya sake shakeni na mutu .
Kamar tsohon maye yake kallonta kafin a hankali yace “Kafarki ba a kasa take ba ki ajiyeta a kasa da kyau kiyi min bayani a ina kika san alqallata?
Muryarta cike da in Inna tace “Uhmmm …ammm sai Kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana wata hadadiyar tsawa ya buga mata yana sake tambayeta jikinta na rawa ta soma mgn ” nasan kana yi sana’ar fashi ne agurin dcp ,nan ta kwashe komai ta zayane masa a karshe tace “yanzu nasan bibiyeta suke domin su samu damar kamaka”.ta hada da Karya dan kar ya fahimci komai ..
“Ke ya’akayi kikasan suna waje yanzu”? “wayar da kayi da anas naji komai gbdy sai tunanina ya bani ni suke bibiya domin su samu damar kamaka .
kallonta yayi a d’age yana ta’be baki ,bani zaki rainawa hankali ba ,kanki zaki rainawa hankali an hada baki dake ba, dan Akamani Shine Allah ya matsi bakinki Ko?”
“To kisani bani da bakin uwa yadda na shigo lafiya haka zan fita lfy , “a’a ka tsaya ka fahimceni na yita kiranka domin na fad’a maka komai dake faruwa kasan matakin da zaka d’auka amman kaki d’aukar wayata .”to yanzu ya ake ciki malama zahra ?ya sake tambayeta a d’age yana sauke numfashi a boye dan gbdy ya gama ganota itace ma tabasu number wayarsa da yake zargin abokansa da yaransa ne.”
“burinsu su kamaka dan Allah ka fahimceni Ina sonka zan iya auranka da wannan sana’ar da kake zan taimaka maka akan sana’arka ta yadda zaka cigaba da samun nasarori sannan kayi nasara akan polisawa dake son ganin bayanka .”
tsaki yaja yana cewa “baki da hankali, Karki d’auka dan kinsan Ko ni waye zai sa ki samu abinda kike so agurina a’a babu wannan damar Idan kin ga dama ki had’a kai dasu ,Ko kuma ince ki qara hada kai dasu ba damuwata bace zasuyi amfani dake ne abanza akarashe kece zaki kwana ciki ya karasa magana yana sake juyawa yasa kai zai ya fita daga d’akin .”
“Wayyolhhly Allah Adnan why please wallahi Ina sonka ka taimakeni bazan iya cigaba da rayuwa babu kai ba na bar zunzurutun miliyoyi kudinn saboda qaunar da nake …”
“Karya kike munafukar Allah
“Ba dai saboda qaunar da kike min ba yasa kika bar damarki Allah ne ya tona asirinki “,karka ce haka please Ina sonka
“bani kike so ba kinsan abinda kike so ajikina ,me zai hana ki hakura dani , jijiyar mazaje nawa kika ci duk baki samu wacce tayi daidai dake ba sai nawa zaki makalewa?” kudi Kuma ki Koma ki karba abunki idan zasu baki kenan ,domin yaudara acikin police kmr tare suka zo duniya ya k’arasa fita daga d’akin gbdy .
Hawaye take har sanda police suka banko kofar dakin suka shigo tana durkuahe a tsakiyar d’akin tasa hannu ta janyo zanin gado ta rufe jikinta tana zubar da ruwan hawaye.
commissioner ya dafa ta ya fara tmbyrta jaguwa alokacin daya Kuma sauran police suna dudduba d’akin ,sai dai babu shi ba alamunsa ita kuwa kuka take sosai da iyakacin karfinta, tayi biyu babu ta fada masa komai sbd tunaninta zai saduda ya sota amman duk da haka bai saduda ba bare hakan yasa ta zama wani bangare na rayuwarsa duk tmbyr da suke mata bata bud’e baki ta basu amsa ba.”
A hankali police suka cigaba da duba lungu da sako kafin suga fitowar commissioner, jaguwa yana ganinsu yay sauri ya boye yana tunanin ko ya haura sai kuma ya fasa ba mamaki wasu police na dakon baya tunawa da yayi ba da fuskar da suke nemansa yake ba Kawai ya fito daga maboyarsa ya soma tafiya a natse Suna bincikensu yazo ya wucesu , sai dai bai tsaya shigar motarsa ba ya bar hotel din .
tare da commissioner zahra ta fito “kin kuwa d’aukar mana hotonsa na ainihi ?”.
“Yallabai nayi k’okarin yin haka sai dai yaki yarda kasan mugun wayo garesa “kiyi k’okarin ki samo mana hotonsa domin da shi kad’ai zamu hanashi yawo acikin garin nan dan zamu baza hotunansa kinga duk inda ya shiga zamu Samu information har bakin motarsa suka k’arasa suna cigaba da tautaunawa ita gsky tana ganin zata hakura da kudin da zasu bata dan bazata Iya kasadar mikashi ga hukuma ba bama zai kamu ba gashi daga haduwarsu duk ta daburce ta fad’a masa komai kuma yaki yarda daita tasan ita dashi har abada .”
Tun akan hanya jaguwa ya Kira baba ya labar masa jikinsa yaki amsa bango “okay to shikenan baba zanzo .”
da misalin karfe tara na safe dady ya zaunar da tanwer yayi mata nasihohi sosai tare da jan hankalinta akan kuskuren da take neman aikatawa, har yayi ya gama bata ce uhm ba bare uhmm, abinda ma bai sani ba babu kalma daya data shiga brain dinta domin kuwa tana kan bakanta na son jaguwa da Kuma son aurensa muddin ya canza sana’a , duk ta inda zasu bullo mata ita dai babu sauyi jaguwa take so .”
Tunda jaguwa ya isa gida ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake yana zukar tabar wiwi yana cewa “ni zahra zatawa haka ?taso yaudarata fa dan dai ni din ba mayen mata bane ?anas ya matso ya dafa shi “wai meye zaka d’aga hankalinka akan zahra din banza babu abinda ta Isa tayi maka baga shi ka ganota ba ” gani tayi zata bukunci lahira shine ta dinga fada min kalaman yaudara wai tana sona bata son na cutu ,kasan wani abu tun sanda ka kirani na ganota kawai na batsar dan naga gudun ruwanta ,Kai lallai ne na kama zahra na rabata da rayuwar waje idan ba haka ba daita za’a had’u a cutar dani, ina bukatar adanata zahra …..” ya fad’a da karfi yana dukan bango nan take hannunsa ya tsage sai jini ya fara zuba gbdy ya fita haiyacinsa anas ya amsa sauran wiwin hannunsa ya kamosa ya zaunar dashi “karka qara shan komai Ina zuwa ya fita da sauri ya bar jaguwa, bai dade ba ya dawo yayi masa dressing din hannunsa jaguwa ya kishingida yana tunanin yadda zai kamo zahra anas ya sake fita ya barshi .
Tunda anas ya fita bacci ya d’aukesa bai tashi ba sai gurin karfe hud’u Kuma har lokacin anas bai dawo gidan ba ,ya tashi ya shiga bayin dake manne da falo ya dauro alwala ya fito ya gabatar da azahar da la’asar shiru anas har bakwai bai dawo ba ,nan hankalinsa ya fara tashi ya shiga neman layinsa kira d’aya ya dauka yana cewa” gani nan shigowa ” .
ko cikakken minti shabiyar basu da gama waya basu yi da gama waya ba ya shigo jaguwa na ganinsa ya mike ya k’arasa ya rike masa hannu” ina kaje kasan banason kanayi nisa dani ko”.
“ba gani a gabanka ba muje kaga wani abu ya jashi zuwa wani daki dake kusa da wanda suka saka alqali, suna shiga jaguwa yaga zahra d’aure har bakinta sai faman zare Ido take .
Jaguwa ya kallesa ya juyo ya Kalli zahra sannan ya kwashe da wata hadaddiyar dariya ya rungume anas ajikinsa “gsky ka burgeni yau kayi abinda ni kad’ai zanyi ,yanzu zuciyata zata samu salama .
ya zare hannunwasa ajikin anas ya dawo Inda take zaune ya dan durkusa a gabanta ya cire pilastar da’a ka rufe mata baki.
“Sannu tantiriya ni zaki yaudara ko? idanunta suka kawo ruwan hawaye ta girgiza masa Kai alamun “a’a !
“har kamar ni zaki yaudara ?”dan Allah kayi hakuri ba yaudararka nayi ba” shiiii……” “rayuwarki tazo karshe zahra kinga kin huta da yawon d’aukarwa kanki zunubi domin kuwa anan zaki cigaba da rayuwarki yana gama fad’ar haka ya mike ya dafa kafad’an anas “muje abokina karka sa a kwanceta sai tayi sati a d’aure ,
“angama mutumina, nan suka sa kai suka fita daga d’akin suka barta tare da kullewa .