KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

da sauri ta hau share hawaye ta fad’a jikinsa gbdy ta rungumeshi very tayt “Na gode Sosai masoyi  ajiyar zuciya ya sauke ya cire hannunwanta ajikinsa dan bazai juri jinta ajikinsa ba komai zai iya faruwa  “muje Ko kafin ta sake cewa Wani abu ya fice daga d’akin dole ta biyosa .
ya bud’e mata gaban Mota ta Shige ya zagaya ya Shiga suka bar gidan sun yi tafiya me dan nisa har suka karasowa   gurin shakatawa wanda ke had’e da cinima  cike da farinciki tace “,dan Allah ka bari mu shiga gurin shakatawar nan”.
“Muyi me ?”ya fad’a a taikace “Na dade banje gurin shakatawa ba Sau d’aya Kawai ka bari muje tare da kai bai ce uffan ba Kai tsaye Wani gurin shakarawa ya nufa daita suna zuwa mai gurin ya karaso ya taresa yana cewa “yallabai daman kayi aure ne baka sanar damu ba, Ai ya Kamata ka sanar damu  muzo tayaka murna amman dai matarka tana da kyau sosai , “shiiii …dan Allah kayi shiru haka mana,”.
” ranki ya dade gsky kin shiga uku da dade jaguwa  yayi saurin zaro masa Ido cikin tsanani tashin hankali yana d’aga masa yatsa ya sake bud’e baki zai mgn yace” haba duk waya tambayeka wannan surutun ?”
  ita kuwa tanwer banda murmushin farinciki babu abinda take” yauwa ke bazaki gane ba kinyi saar miji ba, wallahi mutumin kirki ne muje na sammarmuku guri na musamman ,mutumin yayi gaba suka biyosa Abaya ta sakalo hannunta acikin na jaguwa shi kuma mutumin  yana cewa “bazaki taba samun miji mai kirki kamrsa ba ,yauwa ga guri ku zauna atare suka zauna mutumin yaje ya Kawo musu abun sha ya tsiyaya mata a glass cup ya bata ta amsa  tana masa godiya ” na gode  sosai .
gbdy ta kasa boye murnanta,dan  taji dadin yadda mutumin ya yabesa ya tsura mata Ido Kawai yana kallonta batare daya ce uffan ba ,jikinta ya Bata ita yake kallo ta waigo inda yake  zaune suka had’a Ido nan take ta hadiye rai tana jijiga kafarta d’aya “Ina ganin fa soyayyata ta fara fasa ruhinka ya bud’e baki zai mgn  domin bata amsa  kiran Anas ya shigo ya d’auka”kana ina ne ?
“Ina gurin shakarawa.
ita yarinyar fa a ina ka barta?  “dan matsala muna tare daita ” okay to shikenan “ba dai kaki samawar zuciyarka abinda take so  ba wallahi zaka aikata kuskure akan kuskure.
Shiru jaguwa yayi yana ciza lips dinsa na kasa “Ko yaakayi yasan tanwer tazo gurinsa kai Anas akwai saka Ido “a ina ma kasan tazo “?”A camera naje bincika wasu abubuwane naga shigowarta .”

“Wai ya za’a da mutumin nan ne ya kamata ka ga gansa fa ?”okay gani nan zuwa yanzu ya mike yana katse wayar “Ke Tashi mu tafi na saukeki “haba mana ka bari zuwa anjima, lokaci na tafiya kinsan side dinku akwai nisa gashi banason na janyo miki damuwa agurin iyayenki “.
ya soma tafiya dole ta biyosa ,a daf da gidansu  ya sauketa ya juya da mugun gudu .
ta wuce gida da sanda tana daf da shigewa d’akinta mumy tace “Ke dawo nan tsuru tsuru ta juyo cike da tsoro  Kamar wata mummuna tayi kasa da Kanta “yanzu rayuwar da kika daukarwa kanki Kenan tanwer “?
“Babu kunya ba tsoron Allah kifita har kije gurin aiki sannan kisa kafa ki kama gabanki saboda kin rika  daga gurin aikin Ina kika wuce ?
Naunayyen ajiyar zuciya ta sauke muryarta can kasa tace “gurin adnan “.
Ran mumy yay matukar baci dan ubanki ni zaki fadawa gurin adnan kikaje?”
” akanki aka fara sanin da nmj ?gaban tanwer yayi mummunar faduwa “Allah mumy ba abinda Kike tunani bane Babu komai a tsakaninmu Kawai muna yin hi …”
Kiyi min shiru kafin na tsinka miki mari  wallahi wannan shine karonki na farko Kuma na karshe da Zaki sake fita daga gidan nan kinji Ko bakiji ba ?
“Naji ta fad’a ataikace ta shige d’akinta mumy ta  Samu guri ta zauna tana zama Kiran uncle bashir ya shigo ta d’auka suka gaisa ya tambayata labarin tanwer “tana nan a yadda kuka tafi kuka Barta abun yafi nada dan binsa take yanzu “dan Allah aunty ki kwantar da hankalinki kiyi addua zamu san abunyi Karki saka bakinciki aranki “Ai ya Zama dole bakinciki Kam ,kiyi Imani aunty bakinciki baya taba zama tarihi sai da Imani Allah dai ya  banu Ikon cinye jarabawarmu .
ta numfasa hawaye na zubo mata tace “ameen Bashir  “
“Kinsan Wani abu aunty ?
Tace a’a bashir Sai ka fad’a “ni da minister zai yarda da an aura masa ita sai mu zauna dashi yaron Muga ta inda zamu iya canza masa rayuwa “.
“Wani zunubi na aikata a rayuwata hka  da zan ga wannan mugun Abu ?
“Bashir baki maganarka ba amman bazan Iya ba, rayuwarta zata qare cikin wahala ….”
ta k’arasa maganar tana zubar da hawaye cike da tashin hankali yace “kiyi hakuri mu cigaba da addua amman ina tabbatar miki yadda take ji a yanzu tafi qaunarsa akanmu Allah dai ya kyauta ta amsa da ameen suka cigaba da hira .”


Satin biyu kenan babu shiga ba fita gbdy ta fita haiyacinta saboda zuciyarta na cike da soyayyar jaguwa da kewarsa dan haka da yammaci ranar talata byn sallar laasar kafin karfe biyar gbdy ta manta da fadan da mumy da dady suke mata babu abinda take so face ganin jaguwa kewarsa ta gigita kwakwa
luwarta ta birkitata  adduar istaharar da take ma ji take kmr ta barshi dan babu abinda take ji yana raguwa daga cikin son da take masa.
kamar wacce aka tsurawa allura ta zabura ta mike ta d’auki mayafi tayi rolling din kanta daman can jallabiya ce sanye ajikinta ta  suri mukulin motarta ta sanya takalmi ta fito .
kanta tsaye ta fice zuwa haraban gidan ta shiga mota ta  fice daga gidan kai tsaye bata tsaya a koina sai a kofar  gidan jaguwa tai hon mai gadi ya leko ta karamin huji ta bud’e motar ta fito yana ganinta ya ganeta ya koma ya bud’e mata ta shigo .

D’akin baccinsa ta shiga tana shigowa yana fitowa daga wani  d’akin Wanda shi kad’ai ke shifgarsa hannunsa rike da wani karamin tukunya ya tsura mata Ido yana kallonta cike da mamaki murmushi tayi tana cewa ka tsaya kana kallona kamar bakaji dadin ganina ba sannu da zuwa ma ya kamata ka fara min yace “baza’a miki sannu da zuwa ba ya fada yana ajiye tukunyar hannunsa a karkashin gadonsa .
sannan ya mike   ta kamo hannuwansa ta zaunar dashi sannan ta zauna gefensa tana murmushi “,saboda me zaka ce haka ya watsa rikitattun Idanunshi cikin nata “haka mukayi dake “?
Ta rungumishi ajikinta tana murmushi “,wallahi kana raina bazan iya daina zuwa ganinka ba ,bama kasan yadda nayi kundibala ba yanzu ma satar hanya nayi  na fito surutu kawai suke kamar akaina aka fara soyayya, mumy  ta sa min Ido in fact ma ta hanani fita koina  “.
sai ki hakura ai tunda basa son kiyi  soyayya  ”  wallahi ina sonka kana cikin raina bazan iya  ba kai kasani bani da wani buri da wuce inkasance da Kai  shiyasa ma yanzu nazo na ganka .
“Na gode ya fad’a a takaice yana shafa kanshi ta tsura masa Ido shima ita din yake kallo tana bashi tausayi , anya bazai zubar da komai ya rungumi rayuwarta ba Muryarsa a sanyaye yace  kina sona tanweer ?
“sosai soyayyar da zan rayuwa da kai muddin rai mikewa yayi ya janyo jallabiya blue ya sanya yace” tashi muje ya mikar daita  tsaye ya  sumbaceta yana cewa  “ina alfahari da wannan soyayyar “.
ta rausayar masa da kwayar  idanunta tare suka fito yana rike da hannunta har gaban motarsa ya bud’e mata ta shige ya dawo mazaunin direba yaja Suka fita  kai tsaye unguwar idiara ba ya nufa daita basu tsaya koina ba sai a kofar gidan daya kai hasera .
ya fito itama ta fito suka shiga gidan suka tsaya a tsakar gidan makale da juna ya dubeta yace “kinga gidan nan”?
Tace “na gani gidan waye “?
Zaki iya rayuwa dani acikinsa murmushi tayi tana  fuskantarshi ta sanya hannunta duka ta zagaye wuyansa  zuciyarta na harbawa da sauri sauri “me zai hana Adnan wallahi ya fiye min kowani gida muddin da Kai zan rayu acikinsu ,karka wani damu. a hankali ya gyada mata Kai tare da   zuba mata Ido cikin tsananin shaukinta lallai tanweer tana mutuwar sonshi “,
“Ta cigaba da kallonsa sannan ta furza masa numfashinta wanda yayi sanadiyyar bugar masa da zuciya “zan zauna da kai ka yanke shawarar barin aikinka kenan muyi aure ?”
“Nup dashi zan aureki ya fad’a atakaice yana sanya kwayar idanunshi cikin nata had’e da janyota jikinsa suna shakar numfashin juna.
A hankali yaga ta zare jikinta  tana cewa ” a’a Adnan me zamuyi da wannan saanar  na sha fada maka wannan rayuwar ba rayuwa bace ka daina Tsaki yaja ya juya ya soma tafiya cikin fushi ta biyosa da sauri kafin ta fito har ya shiga mota itama ta shiga suka koma gida da kyar ta bashi hakuri ya sauko har da kukanta suka makale juna kowannensu na nunawa danuwansa yadda yake da mahimmanci agurinsa a hankali har bacci ya d’auketa anas ya shigo yace “Kai bazaka maida yar mutane ba dare fa yayi sosai “bazan iya tashinta ba tana bacci duk sanda ta tashi zan maidaita idan sai da safe ta tashi shikenan .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button