KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Tanweer ta rarrafo tazo gurin mahaifinta “dady please kayi hakuri wallahi bazan sake ba ” sai lokacin yay mgn cikin karfin hali “karki sake fada min haka, sau nawa kina min irin wannan alkwarin kina sabawa?”
ta sake bude baki zatai mgn
yace ” enough tanweer banason jin komai daga bakinki tashi ki bani guri ” ta yunkura da kyar ta tashi ta shige d’akinta tana yiwa kanta fad’a “tanweer ya dace ki canza kodan samarwa iyayenki da kanki kwanciyar hankali ,ki daina zuwa gurin Adnan , shi me yasa bazai zo gurinki ba sai ke?”
Ta zauna a bakin gadonta cike da Jin nadama aranta.
tana zaune tana goge hawaye rukayya ta shigo tana cewa”haba tanweer ,dan Allah ki canza wannan rayuwar bata dace dake ba dan ma Allah yasa gidan nan ku kadai ne , ya kike tunanin halin da iyayenki zasu shiga ace akwai mutane atare daku ?”.
Hawaye masu zafi suka zubo mata .
rukayya ta zauna gefenta “Ki daure ki cigaba da addua “.
“Ina yi rukayya wallahi har na gaji da yin addua “ta fad’a tana kuka “ba’a gajiya da addua sai dai kina yi kina avoiding din wasu abubuwa ne, ki d’aure ki koyi hakurin rashin zuwa gurinsa wallahi a hankali kina addua kina rarrashi zuciyarki zaki rage soyayyarsa.
girgiza kai kawai tanwer tayi a ranta tace “rukayya bazaki gane ba, rukayya soyayyar nan nada wuyar bari ,ita wallahi bancin iyayenta ma da tarewa zatai agurinsa sai dai yasan yadda zai yi daita.
“tanweer!”
Rukayya takira sunanta bata amsa ba sai dai ta d’ago ta zuba mata Ido tana sauraronta “ki dinga karanta ya hayyu ya qayum ya zaljalalu wal ikiram sannan da laila ailla anta subhanaka inni kuntu minal zalimin inshallahu zaki samu sausauci da natsuwa kina addua Kuma kina nacewa wadan zikirorin suna matukar yayewa mutun damuwa .”rukayya tafi minti shabiyar a d’akin tanwer tana bata shawara kafin daga bisani ta barta ta koma d’akinta .
Bangaren jaguwa kuwa karfe daya daidai ya shgo gidansa yana shiga falo ya k’arasa gurin fridge ya bud’e ya d’auki goran ruwa mrs v tare da kafeshi abakinsa ya shanye tasss sannan yayi wurgi da rabon zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun falon yana sauke numfashi yana Jin kamar tanweer na kwance ajikinsa ne , wata irin zazzafa soyayyarta ne ke ratsashi yana tuno duk abinda ya gudana a tsakaninsu ,bai yi tunanin zai rufta har haka ba, lallai maganr anas ta tabbta koma yace bakinsa ya kmashi ji yayi an dafashi a zuciye ya juyo da niyyar yiwa kowa ye maseefar katse masa tunani sai yaga anas ne “cool down mutumina karka saukemin maseefa ya fad’a tare da zama a gefensa “ya ka maida tanweer ?”um na maidaita wallahi sai naji dama na barta. “bangane dama ka barta ba ?”ka barta ka dinga kwana da yarinyar mutune ko me ?”.
tsaki yaja “kai wallahi wani irin mutun ne ko yanzu banyi komai daita ba ,”bayan na farko kana son kace baka sake ci ba ?”.
“Naci mana amman sau daya ne daga shine dai babu kari.
“Shikenan ka dinga kiyayewa please kasan yarinya ce karama .”
“nasani shiyasa ma kaga banason kusancina daita wallahi idan tana zuwa zan din cin yar mutane né kawai ,zan ma fad’awa mai gadi kar ya sake barinta ta shigo idan tazo “gsky abar wannan relationship din haka tunda bazai kaiku ga yin aure ba .”
Har yanzu kaki ganin mutumin nan sai faman binka nake ,ka hadashi da wancan mutumin ayi komai a gama ayi musu tsakani zuba masa idanunsa dake cike da giyar soyayya yayi sannan ya mike tsaye ya fara zare jallabiya dake sanye ajikinsa ya rataya akafadanshi ya nufi d’akinsa yana cewa ” zuwa yanzu nasan ya horo sai dai ban shirya ganinsa ba sai mun dawo daga abuja mugama da aikin nan da aka kawo “. Yana shiga d’akinsa bathroom ya shiga ya tsaya rike da kugunsa yana tarawa kanshi ruwan wanka babu abinda zuciyarsa ke yi sai faman tunanin tanweer hankalinsa gbdy baya jikinsa tube boxes dinsa yayi ya shiga bathtube anatse yayi wanka ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna tanweer murmushin farinciki ne ya subuce masa a haka yayi wanka ya fito .
Ya goge jikinsa ya bud’e Inda kayan shan iskansa yake ya dauko gajeren wando ya sanya ya shirya tsaf sannan ya kwanta batare daya sakawa cikinsa komai ba.
Washegari da safe byn fitar dady mumy ta iske tanwer a dakinta kwance ,ta tasheta ta mike ta zauna tana dubanta “ina kwana mumy?” Kin tashi lfiya mamana ?” Lafiya ta amsa atakaice mumy ta kamo yatsun hannunta sannan cike da marairacewa tasoma mata nasiha mai ratsa jiki tana rikonta “ki tausaya min surayya wannan rayuwar nasan qaddara ce amman ki daure ki cinye jarabawar karki kauce hanya ina miki addua zaki samu wanda yafi shi komai take hawye ya shiga turereniyar zubo mata “wannan alfrma ce na nema agurinki zaki min ko kuwa na hakura na cire raina akanki na bar masa ke ya maye mki gurnina “?kanta ta shiga girgiza mata alamun “a’a “.
“Kinyi min alqawarin zaki hakura dashi “?ta gyada mata kai alamun”eh! dan babu yadda zatai amman hakura da jaguwa ma bai taso ba mutumin da duk saukar numfashinta da tunaninsa aciki.
“Na gode allah yayi miki albarka allah yaye miki “.
da misalin karfe uku tana zaune a falo taji motsin shigowa dolapo ya shigo da manya ledodi ya ajiye a gefe yana gaisheta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta mike ta koma d’akinta ta kwanta , dolapo bai k’arasa fita ba dady yasanyo Kai yayi saurin yin gefe ya bashi hanya mumy tayi masa sannu da zuwa kallon da yayiwa mumy gabansa ya fadi sannan ya amsa mata sannu da zuwan datai masa ya zauna a falo yayinda ta tashi ta shiga kitchen ta dauko masa ruwa mai sanyi ta kawo masa ta zauna a gefensa tana sake masa sannu da zuwa byn ya sha tayi masa ya aiki ” alhamdulillah yana ganki ke kadai shiru ina ita wannan yarinyar ?” ya tambayeta gabansa na faduwa kar ace bata nan .
“Tana d’aki yanzu ta shiga “
naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana samun natsuwar zuciya “hankalina na kanku saboda nasan na barki cikin wani hali “ai inshallahu komai yazo karshe ta fad’a tana fad’a masa yadda sukayi daita da safe byn fitarsa “Allah yasa Iya wahalarmu kenan tace Ameen “ai muddin ta saba alkwarin taki natsuwa acikin gidan nan zan bata mamaki domin dole ta zaba komu ko shi wancan dan iskan barawon banza inji cewar dady.
ita kuwa uwar gayya tunaninta ba’a kansu yake ba dan tana shiga daki ta d’auki wayarta abun mamaki missed calls din jaguwa ta gani guda uku ajere murmushin jin dadi tayi ta soma neman layinsa kira d’aya ya dauka alokacin yana zaune akan kujera a falonsa system ne a gabansa ya dauka ya manna a kunne idanunsa na kan screen din wayar “hello tanweer ?”
Shiru tayi tana sauke naunayen ajiyar zuciya tare da Jin dadin zazzakar muryarsa “ina yini ?”
“Lafiya ya Kike fatan komai lfy ko dan jiya da tunanin abinda zai faru a gidanku na kwanta hope babu abinda aka miki?”
Babu komai fad’a ne kawai Kuma kamar yadda kace hakuri nayita basu “that’s good haka ake so “.
yayi shiru itama tayi har sai data d’auka ko ya kashene ta cire wayar a kunnenta ta duba taga har lokacin yana kan layi ta maida tana sauke masa numfashi tana cewa “hello !
“Ina jinki tanweer yaakayi ?”
“last Kafin zuwana jiya gurinka kace min zaka zo gidanmu ?”
Shiru yayi yana sauraronta batare daya ce komai ba illa mikewa da yayi tare da gyara rigarsa sannan ya nufi d’akinsa ya d’auki wasu abubuwan amfaninsa ya karaso Inda akwatinsa red and black yake ya bud’e sama ya zubasu sai lokacin yace “ina sauraronki sauri nake domin akan hanya nake tafiya zanyi zuwa Abuja jirgina karfe shida daidai zai tashi “.
me zakaje yi abuja ?” Tayi mgnr kmr zatai kuka dan tuni idanunta sun cicciko.
“alqalla !” Yana daure fuska dan karta kawo masa wasa a aikinsa.
shiru tayi kamar ta karasa fashewa da kuka “banason aikin nan adnan ……”
“kullum maganarki kenan ” ya katseta ta hanyar fadar haka cikin zafin rai “shine damuwata nafi son ka zauna empty baka aikin komai akan wannan sana’ar, ka tausaya min mana “naji !” Kukan da take dannewa ne yayi nasarar kufce mata ta soma rera masa kuka har da shesheka “meye hk Kuma ?”ke me yasa kuka baya miki wahala né ?”
“idan wani abu ya sameka ya kake son nayi ?
Sosai tausayinta ya kamashi dan hk ya kwantar da muryarsa kmr tana gabansa “ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameni zama yayi domin rarrashinta wanda bai san yanayin hakan ba ,
” kwana nawa zakayi ?” zanyi kamar sati daya zuwa kwana goma “haba Adnan me yasa baka tausayina ne kwanakin nan sunyi yawa “.
Ya sake yin kasa da murya abinda zai kaimu din ne dole sai munyi taking time “shikenan Allah ya tsare min Kai “ameen ya furta a can kasan makoshi yana lumshe idanunshi “yanzu sauran awa daya da wani abu kenan ku bar gida yace “um ! “zanzo na ganka kafin ku fito zuwa airport Kona zo airport din direct “?
“No karki zo “
ya fad’a atakaice tare da katse Kiran dan bai son tazo sannan bai son mgn dayawa dan ma itace shiru tayi rike da wayar taso taje ta ganshi kafin ya wuce har ta fito mumy ta kasa ta tsare kamar tayi kuka ganin take iyayenta basa mata adalci a hukuncin da suka yanke mata a zatonsu zata iya zama na tsawon lokaci batare data d’aura idanunta akanshi ba ?”.
ta lumshe idanunta daga tsayen da take “bazan iya ba gsky sai daí kuyi hakuri wallahi ta cigaba da sakar zuci .