KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Yayinda eku daya rigasu isa abuja tun safe
ya kama musu daki a humble star hotel a second floor ,yayi musu shopping kayan bukatarsu sannan ya zauna zaman jiran karasowarsu karfe bakwai daidai ya nufi airport ya jima kadan kafin ya karasa saboda nisan dake tsaknin inda yayi musu louge yana gama karasowa ya tsaya ariver domin jiran karasowarsu .
Karfe takwas daidai suka sauka,suna sauka eku ya dukesu kai tsaye unguwar Funsho Williams avenue suka nufa bai tsaya akoina ba sai abaki tafkeken get din humble star hotel ,get din abude yake kmar koda yaushe ya sanya hancin motar cikin haraban hotel din maakata hotel din suka taso suna nuna masa inda zai yi parking yana gama parking suka fito daya bayan daya cike da jin kai suke taku har suka karaso cikin reciption “gsky eku ka kama guri mai kyau da sirri allah yasa yadda wajen hotel yayi kyau cikinsa ma haka yake?”inji cewar kamil “ai kana gani ba magana jabir ya fada yana sosa keya suna gama karasowa second floor ya mikewa kowanensu key’n dakinsa sannan ya karasa da sauri bakin kofar dakin jaguwa room 120 ya bude ya tsaya har sai da jaguwa ya shiga sannan ya biyo bayansa babban daki ne dayaji komai da kayan more rayuwa zama yayi akan kujerar kwaya daya dake ajiye adakin eku ya dauki remut ya qara masa karfin ac dake aiki a dakin yayida jaguwa yayi shiru yana kallon tsarin dakin murya cike da ladabi eku yace “boss me zaa kawo maka?shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma ya motsa lips dinsa “wani abu mara nauyi “okay sir ya juya ya fita jaguwa ya zuge zip din yar saman rigarsa ya ajiye akan gado ya kwanta flat yayi pillow da hannuwansa duka sannan ya runtse idanunshi babu wacce yake gani acikin kwayar idanunshi sai tanwer dinsa laulausar gashinta,surar jikinta uwa uba dukiyar fulaninta a yanzu ko baa fada masa ba yasan yana quanrta kamar shine ya haifeta musaman a irin qaunar da take masa mai tsanani sai dai duk wannan qaunar da yake mata zai rusheta ya zamanto kamar baa yi ba , zai bar wannan sirri acikin zuciyarsa bama zai bari wani mahaluki ya fahimci halin da yake ciki ba .
a hankali ya fara jin ana knocking a kofar dakin da kyar ya bude bakinsa ya bada Umarnin shigowa kuma har lokacin bai bude idanunshi ba maaikaciyar hotel din ce sanye cikin riga da siket iya gwiwarta ta gaishesa bai amsa ba ta ajiye faranti silver ta juya ta fita ta rufo masa kofa .
Byn fitarta da kamar minti gomasha biyar ya mike zaune yana jin sauyin yanayi ajikinsa ,iska ya furzar mai zafi sannan ya kira number anas da sauran abokansa kana ya janyo akwatinsa ya bude bindiga pistol ya soma fitowa dasu daya byn daya yana kallo kusan guda shida yana kokarin fito da cikon ta bakwai suka fara shigowa one by one anas ne ya shigo akarshe yayi wa kofar key.
Zama sukayi gbdy a gbansa suna kallonsa ya dago ya kallesu “bana bukatar kowanne aciinku ya kwana da kowace mace daga yanzu har zuwa sanda zamu Kammla abinda ya kawomu,bamu samu isashen lokacin tautaunawa ba kafin mu taho amman nasan kowa yasan abinda ya fito damu abu ne mai mahimanci.
Gyada masa kai sukayi “yanzu dame zamu fara?”jabir ya tambaya ya mike tsaye ya jingina da bangon dakin tare rugunme hannuwansa”zamu jira sky muji bayyanan daya samo mana akansu tukun idan ta kama ma a daren nan ma zamu iya fita .
zamuyi wannan aikin bisa kasada da rayuwarmu idan mun fadi ku yafemin idan kuma munyi nasara muyi farinciki tare.
” inshaallahu zamuyi nasara inji cewar Ana’s “idan kaji ajiknka zamu fadi mu hakura mana?jubi ya fada yana dubansa “sam banji ajikina cewar zamu fadi ba amman wannan rayuwar tattare take da abubuwa ya fada yana lumshe ido sun jima suna tautaunawa har karfe dayan dare basu samu wani bayani daga sky ba dan haka ya sallamesu byn ya mikawa kowannensu bindiga sannan ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta ruf da ciki gbdynsu sun yi bacci amman Banda jaguwa bini bini zai dauki wayarsa ya duba ko zai ga wani bayani daga sky à hankali Sakonni sky ke Shigowa wayarsa ya zabura ya mike daga kwance da yake ,kwana yayi yana tsara yadda fitarsu zata kasance yayinda minister suka kwana suna tashin hankali da hjy zainab .
Washegari yana tashi ya bude school bag ya dauki brush da toothpaste ya shiga bayi bai jima ba ya fito yana kallon murdadden jikinsa zuwa kan nipple dinsa abinda yafi daukar hankali mata kenan akanshi inda zai sakewa mata da ya ci mata bilaadadin ya goge jikinsa ya fito da turare mai dadin kamshi ya feshe ilahirin jiinsa ya dauki riga da wondo bakake ya saka ya janyo wayarsa nan ya sake cin karo da sakon sky cikin sauri ya shiga neman layukan abokansa ,a haraban hotel din suka hadu suka shiga mota suka fita .”
tun da sanyi safiya shima dady ya shigo d’akin mumy ya isketa zaune ya tsaya a gabanta yana dubanta idanunta duk sun kubura saboda kuka “ni zanyi tafiya zuwa kaduna wata killa na dawo yau ko gobe “bata kallesa ba ta cigaba da jan casbaha “,kiyi hakuri zainab a halin yanzu zuciyata cike take da gariri da tashin hankali bama haka ba har cikin zuciyata nake Jin nadamar abinda nayi .
Wallahi Zainab nayi nadama tun kafin kisan komai na dade wani abu bai sake shiga tsakanina da diyar kowa ba adduata Allah ya yafe min ya Kuma min sausauci bata ce masa um ba bare um’um har ya Karaci maganarsa ya juya ya
tsallake ya bar garin zuwa kaduna yana fita
mumy ta tashi ta shiga d’akin tanweer ta sameta kwnace lamo tana tunani jaguwa yayinda hannunta ke rike da casbaha tana ja tana masa adduar
Allah ya karesa mumy ta samu guri ta zauna kusa daita tana shafa kanta hawaye suka shiga gangaro mata tanweer ta yunkura ta mike zaune taga mumy na Kuka cikin muryar kuka tace “kiyi hakuri mumy nasan saboda ni kike kuka ko ?” inshallahu zan canza, ta girgiza mata Kai tare da riko tafin hannunta cikin nata cike da tausaya mata
Sun dade a haka Mumy na shafa kanta so take ta furta mata abinda ke ranta amman ta rasa dalilin dayasa ta kasa .
cike da jajircewa irin ta sky jaguwa da abokansa sukayi nasara domin kuwa sun amshi makudan kadade kimanin million hamshin a hannun alhj usman koko betse farmer farm sectry , mutun biyu suka rage dan hk suka dawo masaukinsu cike da farincki sun so suyi ashararanci jaguwa ya hanna dan baya wasa da aikinsa sannan kuma baya son aka masa wasa”.
Washgari suka fita neman Alhaji sani fefa shima cikin saa suka shiga gidansa suka amshi kudi mai yawa a hannunsa mutun daya yayi saura wato ajirebi .”
Su jaguwa na fita daga gidan alhj sani fefa suka kama gabansu ,shi kuwa zama yayi jagwab akan kujera mai zaman mutun daya zuciyarsa cike da matsanancin mamaki “shi da yake wa mutane fashi shine yau aka wayi gari har gidansa aka biyosa? dadinsa ma basu taba masa lafiyar iyali ba koda yake sun fada masa abinda ya kawo su “kudin da yayi ruwa yayi tsaki aka dannewa marayuwa suka zo amsa “.
Cike da rawar jiki da tashin hankali ya kira number alhj usman farmer farm sectry yana dauka ya fara cewa”anyaka tata shi fa domin kuwa anbiyo kudin da mukaci satin daya gabata “.
Naunayen ajiyar zuciya alhji Usman ya sauke yana mikewa tsaye daga zaunen da yake “sosai kuwa nima cikin tashin hankali nike domin kuwa jiya iwar haka ina cikin tashin hankali har gida barayi suka zo suka yasheni tasss “ kace kai ma anzo maka kenan nan?
“Kwarai kuwa?
“amman me yasa baka kira ka sanar dani ba har kabari suka riskeni har da takamar kudin marayu suka zo amsa ? kasa kunne nayi naga ta inda zanji wanda zaa wa acikin mu tunda yanzu anzo har gida anyasheka nasan ba daga gurinka bane nafi tunani daga sama ne tunda nima sun fada min wannan kalmar kudin marayu suka zo amsa “ ya karasa maganar yana cewa bari na hadamu conference cikin minti biyu kacal muryar ajirebi data galadima da garunmallam ta bayyana a bayanin da Alhaji sani fefa ya cigaba da yi yasa suka fahimci komai “ to wa yasan da wannan maganar “.?
“Byn mu biyar din nan babu wanda yasani “lallai akwai wanda yasani munyi shuka ne a idon wasu , lallai ya kamata mu san ko su waye suka fara bibiyarmu domin bana tunanin wanda zai iya karawa damu bare har ya bibiyemu, “ wannan gsky ne“.
“Gani nan zuwa kafin nazo ka kira jami’an tsoro lallai dole akama wadan nan yan fashi tun kafin su riski sauran dan haka lallai su maida hankali a kamo wadan nan barayin farmer farm sectry na gama fadar haka yayi disconnecting din kira yadda yayi haka sauran sukayi cikin tsananin tashin hankali ajirebi ya hada kudaden daaka raba aka bashi ya zuba cikin akwati ya bar gidansa dan daman cash suka amsa domin gudun idan asiri ya tono ko anbi diddigi bazaa gano daga inda kudn suka shigo ba.”