KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Shi kuwa Alhaji sani fefa ya soma neman layin jami’an yansanda ya zayyane musu duk abinda ake ciki,cikin kankanin lokaci suka karaso har zuwa babban falonsa ya mike yana sake musu bayani suna dube dube tare da tambayarsa ko akwai wata sheida da zaa iya kama yan fashin “shiru yayi yana tunani mai zufi,“ina iyalin naka suke “?
“Suna wancan dakin ya basu amsa yana sake zurfafa tunaninsa “fatan dai basu taba lafiyarsu ba “?babu wanda suka taba dan lokacin da suka bude kofar suka shigo basa wannan falon suna wancan bangaren ya karasa maganar yana sauke numfashi yana mamakin taaddacin yan fashi “abinda zai baku mamaki kamar walkiya nagansu agabana ni har yanzu mamakin nake yayi shiru goye da hannunwansa duka abayansa can yace “yauwa akwai ajiyar kamarar camerar dana yi a falon ya karasa da sauri inda karamar camerar daya makala a bangon falonsa take mai kallon duk wanda zai shigo.
ya ciro memory “sun yi son ransu amman da wannan bazasu tsira ba domin duk fuskokinsu a bude yake yana magana yana kokarin jona momery din acikin flash sannan ya jona da tv bangon dake manne a falon ana gama hada komai sai ga fuskokin su jaguwa daya byn daya ta bayyana kowannensu rike da bindiga .
daya daga cikin jami’in tsoro yace “gsky kayi dabarar saka wannan karamar camera dan sam babu wanda zai fahimci akwaita dan haka gbdynsu bazasu tsira ba duk inda suka shiga acikin garin nan sai an fito dasu .
“gsky a fito dasu shine kawai kwanciyar hankalina “an gama ranka shi dade “.
Sosai suka maida hankali ga tv duk inda aka hasko fuskar jaguwa da abokansa sai yansada sun dauki hoto , fuskokinsu tas ta fito bazaayi wahalar kamosu ba, cikin kankanin lokaci suka tura hotunansu zuwa headquarters sannan aka tuwa kowaneni maaikaci dake aiki cikin garin sannan suka masa sallama suka wuce …..”
Jaguwa na zaune a mota sakon sky ya shigo “boss byn fitarku a gidan jami’an tsaro sun zo gidan alh sani ku hanzarta komawa masaukinku “.uhm “!
Kawai ya furta a hankali sannan ya katse kiran.
a rana ta uku basu samu bayanin komai ba akan mutun na uku da suke hari daga bakin sky haka ma rana ta hudu wasa wasa suka share kwanaki suna nemansa batare da sun gano inda yake ba dan haka gbdy suka raba kansu suka bazama nemansa yayinda hotunnsu ya baza acikin garin abuja tare da baza jami’ai a kowani titi.


Cikin wata shiga ta kamala wacce idan ka kallesu bazaka taba cewa su din masu sata da azalumai da gwanati bane suka shigo cikin club kowannensu ya samu guri dabam ya zauna yana kare wa yanayi gurin kallo har sanda babban yaron ajirebi ya shigo ya isa inda aka ajiye empty chairs ya zauna tare da ciro wayarsa yana daddanawa atare suka kalli juna sannan sukayiwa junansu sigina da ido.
Zaman sa bai fi da minti biyar ba maikatan club din suka karaso inda yake yana tambayarsa abinda yake da bukata , “yallabai me zaa kawo maka ?” ya dago a hankali ya kalli matashin maaikacin dake sanye da uniform fari sannan yace ” kwalba giya daya ma ya isa yaron ya juya da hanzari ko minti biyar bai yi ba ya dawo hannunsa rike da tire na silver da kwalbar giya da cup ya ajiye masa akan table duk su jaguwa na zaune suna kallonsa sai dai a shirye suke dashi a hankali ya dinga tsiyaya giya a cup yana sha har ya shanye tass cikin haka aka kira wayarsa ya dauka yay magana sannan ya mike tsaye yana kiran yaron daya kawo masa giya.
Yaron ya karaso cike da ladabi ya tsaya agabansa ya ciro kudi ya mika masa batare daya tsaya amsar canji ba ya juya yana isa haraban club din yaga an sha gabansa a matukar tsoarace yake kallonsu duk da bai san fuskarsu ba ya fahimci su din kamar zasu cutar dashi ne,ya juya da sauri zai gudu yaga mutun biyu a bayansa ,gbdy suka zagayeahi “ina bukatar ajirebi?”.
“Wani ajirebi kenan ?”
“kenan amsa kake bukata daga garemu ?” Anas ya fada yana harbin gwiwarsa ya saki kara mai sauti tare da zubewa kasa rike da kafarsa yana cewa “yana wani hotel amaitama no 21 ameka anyaku number dakin 104 suka karbe wayarsa sannan suka turasa cikin motarsa suka rufe shi batare da sun zare key ba suka juya daya byn daya suka shiga motorsu .
jaguwa ya maida hankalinsa ga kallon titi zuciyarsa na hasko masa fuskar tanwer yana kwadayin ganinta da jin muryarta amman wannan aikin ya sha gabansa bazai samu damar kiranta ba sai ya kammala numfashi ya fesar tare da sauke numfashi alokacin da motarsu ta shiga emeka hotel .
sun jima basu fito ba suna jiran umarni daga jaguwa a hankali ya bude murfin motar ya fito yana gyra wuyan rigarsa batare da yace musu komai ba.
suma basu damu ba domin sun san shirunsa yana nufi su biyosa ko kuma su kama kansu ya soma tafiya sam bazakace dan fashi bane .
kai tsaye ya nufi kofar glass wacce zata kai mutun cikin hotel din yana shiga ya tsinci kanshi a reciption yana kokarin tamvayar wata maaikaciya number dakin ya hango ajirebi ta gurin swimming pool yana zukar taba kai tsaye ya zarce zuwa gurin yana hamdala .
Ajirebi na zaune yana cigba da zukar sigari yayinda jaguwa ke nufo gurinsa anas ,da kamil da jabir suna biye dashi sky da jubi da eku , suna waje cikin mota suna jiran umarni .
Ajirebi ya zuki sigari ya busar yana lumshe ido ko da zai bude idanunshi kawai yaga mutane sun zagayeshi cike da tsananin tsoro ya saki sigarin hannunsa kasa yana dubansu gabansa na faduwa anas yayi sama da rigarsa nan idanunshi suka ga bindiga “tashi muje masaukinka cikin lumana kafin ranka ya zama fansa ,ka dauka zaka gudar mana ne?”.
Shiru yayi yana tunanin yadda akayi sukasan yana gurin “babu wanda yasan san ko su waye mu karka bari a fahimci komai dan kai zata kwabewa domin zaka bakunci lahira batare daka shirya ba inji cewar kamil dan.shi jaguwa ko uffan baice ba .
Cike da tashin hankali ya mike jikknsa na rawa suka jera da jaguwa har suka kawo bakin kofar dakin daya kama suna shiga jaguwa yasa kafarsa daya yay masa mugun bugu sai ga ajirebi akasan tayis timm
fuskarshi ta bugu da karfi “wannan na bata mana lokaci dakayi kwana da kwanaki ne ,dan kasan muna nemanka shiyasa kazo nan ka tare ,kana tunanin zaka bace mana ne ?” Ko Ka bace kayi aikin banza tunda karnunka na yawo kaga shigowarka hannu bazai wahala ba .
ya numfasa sannan ya cigaba da magana “ina kudin marayu ?”
Bakinsa na rawa yace “suna cikin akwatin can “very gud dan ka taimaki kanka da ka taho dasu dan wallahi da haushinka nazo idan kayi any mistake akanka zan fara kashe rai “.
Nawane acikin akwatin ?”70 million.
Ya bashi amsa jikinsa na rawa “ina sauran “?
“Suna account dina ,ina wayoyinka ?”
ya ciro guda daya acikin aljihunsa yana nuna musu “ina sauran wayoyinka?”suna gida .
“Me yasa ka barsu agida ?”
“Ranka shi dade bansan zan hadu daku ba .
“nawa ne acikin wannan account din “million goma shabiyar ne yana rufe baki sumy budurwar da aka kawo masa aminti talatin data wuce ta fito daga bayi daure da farin towel tana ganinsu rike da bindiga ta kwalla qara sannan ta zube kasa sumammiya.
jaguwa ya numfasa hade da runtse ido yana shafa goshinsa “kun sace kudin marayu kowanneku na cin duniya dashi.
Kowannenku ya kama hotel da karuwai iri iri yana cin hakin bayin allah yanzu ace na harbeka na aikaka lahira inda mahaifin yaran ya tafi ace ni barawo ne nayi maka fashi sannan na kasheka baasan abinda kai da sauran yanuwanka suka shuka ba .
kamil bashi account din marayun nan yasa kudin duka acikin “haba ranka shi dade idan haka ne ai bani kadai naci kudin marayu ba alhji usman
Koko betse tsohon farm sectry ma yaci nashi kason da sani fefa zan nuna muku inda suke da sauran …..”
“Kamin hiru har ka samu baki zayyano bayani ya daura masa bakin bindiga akanshi “tuni na gama dasu kai kadai ka saura dan haka kayi abinda na saka “.
jikinsa na rawa yace ” wallahi ba iya mu kawai bane akwai galadima shima yaci 50 millions ,ni iya million sittin ne kudin danasan naci sauran nawane “ba nasu bane .
“I said  shurt up mutumin daya saba cin hakin mutane komai aka samu agurinsa ba nashi bane duka zaka tura idan kagama turawa da kai zamuyi amfani gurin  fito da shi galadima dan kwandala bazakuci acikin kudin nan ba .
jikinsa na kyarma ya sake bude baki zai yi magana jaguwa ya buga masa wata hadaddiyar tsawa “Shut up or else I will get you lost in second are you insene?ina magana kanayi ?”kayi hakuri ranka shi dade nayi shiru hankalinsa a matukar tashe ya  shiga mobile baking dinsa .
Yana kokarin tura musu kudin kamil da jaguawa sukayi kan budurwar dake sume suna kallonta suka barshi  da anas wanda shima hankalinsa ke kansu bindigar ce kawai ya saita a qirjin ajirebi,”kalli yarinyar nan sak bahaushiya dan allah me zata tsinta agurin wannan katon bayarbe “?
Anas ya fada yana karewa fuskarta kallon tsaf kyakkyawa ce fara sol doguwa mai shape din coka cola ga suma kana ganinta kaga hausa fulani .
kamil ya numfasa yace”me zata tsinta fa kace?, kudi fa ta fito nema kaga kuwa tasan abinda zata tsinta ai abujan ba kyau, idan kaga yadda ake hadawa mata connection sai ka sha mamaki muma dan boss ya hana ne da mun shana da manya mata masu kyau da diri,suna ta magna akan yarinyar da bata san halin da take ciki ba  Yayinda hannun ajirebi daya ke sarrafa waya, dayan hannunsa kuma ke laluben bindigarsa a karka shin gado domin tsira da kudin……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button