KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ya bude idanunshi da kyar yana cewa nayi sai ka sakar min hannu ya fada yana fixge hannunsa cikin na anas, ya dafe kansa yana cewa “allah banason ganinka cikin damuwa bare damuwar ma akaina yayi mgnr zai durkusa masa jaguwa yace “no karka durkusa min please kar ma ka sake min irin haka kai fa aminina ne kuma danuwana ba iya halakar aminta kawai ke tsakaninmu ba akwai soyayya me karfi ya fada yana ciro hanky da sauri ya soma goge masa hawayensa “kana dani meye abun kuka “?karka damu nayi maka alkwarin muna komawa zaa tura manya ne mammaka aure “.
“Allah sarki aminina kana sona dayawa “yes ina sonka sosai sbd kai ma kana sona maimakon anas yayi magana sai ya daura kansa akafadar jaguwa yana jin yadda yake sauke numfashi da ajiyar zuciya wanda yasa hawaye ya gangaro masa jaguawa ya dagosa “me kuma abun zubar da hawaye kai da ka kusan an gwancewa da amaryarka”? a yanzu nafika matsuwa naga wace zata auri bin malik dina “amman kai nafi son kayi tunda kana da wacce take sonka “share kawai ni aure yanzu baya gabana na haseera zamewa zan……”
“please jaguwa karkayiwa Ammin haka yayi saurin katsesa “koda yake samun mahaifiyar kayi ni nayi mana “ya karasa mgnr muryasa na rawa “zaka fara ko ?to shikenan zanyi duk abinda take jubi ya bude kofar ya shigo ya tsaya yana kallonsu kamar zasu shige jikin juna…”
Ranar haka garunmallam ya dinga zagaye airport allah yasa da jami’an tsaro da an zargesa tun safe har yamma yna zagaye gurin kafin daga bisani ya koma gida agajiye yana shiga gida ya kira headquarters na police yace ga kudin fa ,tun jiya banga kowa ba, yau ma tun safe nake yawo har airport ban hadu da kowa ba .
“mun sani saboda muna biye da kai sun ma sun zo fahimta sukayi ana biye da kai amman lallai zasu zo yau” ranar bai runtsa ba da zarar ya rufe idanunshi sai yayi firgigib ya bude rana a zaune ya kwana, wasa wasa har kwana shida basu zo ba jami’an yansanda suka turo masa jami’an sirri aka musu kyakkyawan masauki abakin get din gidan wanda hakan ya kwantar da hankalinsa.
su jaguwa basu zo ba sai randa sati ya cika garunmallam na zaune yana tunanin ta yadda zai rabu da kudin hankalinsa ya kwanta kawai yaji kamar ana duro gidansa yana yunkura tashi yaga manya karta maza majiya karfi na shigowa falonsa a firgice ya koma ya zauna arasa yace “sai yau allah yayi ?
a natse suka gama shigowa kowane ya rufe fuskarsa da bakin kyale wanda yafi kama da yadi .
mamaki ne ya kamashi ta yadda akayi suka shigo gidan har cikin falonsa byn akwai jami’an sirri a bakin get dinsa nan da nan suka kewayesa da bakin bindigar dake rike a hannunsu cike da rashin jin tsoro jaguwa ya karaso inda yake rike da bindigarsa “garnakaki uban shegu barawo ne ni amman mai mugun wayo , yau dai dubunka ya cika,ina kariyar daake baka take? ya fada tare da karasowa zuwa gabansa ya tsaya kikam sannan ya cire glass din daya rufe masa rabin fuska tare da cewa “ina kudin suke? cike da rawar jiki yace “gasu can ya tashi yaje ya dauko jakar kudin ya dawo da sauri ya ajiye musu a gabansu “lallai ka kyautawa kanka sai dai ka tabbatar da kudin da suke ciki sun cika cif ,ko kwandala ban taba ba yadda akabani haka suke “very gud ,eku shiga dakunan gidan ka fito min da duk wanda kagani “ok sir!.ya nufi hanyar shiga dogon falon da idanunshi ya kai .
Garunmallam yayi saurin durkushewa kasa ya rike lafafun eku yayinda idanunshi ke kallon jaguwa “dan girman allah karka taba min lafiyar iyalina ,abinda kuka bukata gashi nan na baku ku tausaya min “a she kuna son a tausaya muku amman ku bakwa tausayawa mutane”? eku kayi abinda na saka ,gama jin haka ke da wuya eku ya fizge karfarsa ya nufi dogon falon .
a hanakli ya dinga bin daki daki yana fito da mutanen gidan cikin tashin hankali fuskar data fito karshe ce ta janyo hankalin jaguwa da tawagarsa gbdy suka zuba mata ido suna dubanta, sosai jaguwa yake kallon fuskar tabbas fuskar da ya gani ce ba kuma zata bace masa ba yayi murmushin takaici” lallai ana burouba a duniya kamar yarinyar da muka gani da ajirebi a hotel ?”inji cewar kamil .
“ba kama bace itace “kaga tsantsar cin amana ko ? a junansu ma basu bar junansu ba suna kwana da yayan juna jaguwa ya fada yana gaurawa garunmallam wani lafiyayyyen mari wanda yasa yayi yar dungure ya fada byn kujera mai zaman mutun uku yana haki wata irin zufa na tsatsafo masa bisa goshinsa “kaci saa muna kan hanya ne wallahi da kasha azabar da har sai ka gwamaci mutuwa da rayuwarka ,sannan ya juya a natse yayi taku biyu ya tsaya a inda yarinyar ke rakube cike da matsanancin tsoro.
taji tsayuwar mutun amman tsoro bai barta ta iya dagowa ba cike da bakin ciki yake mata wani irin mugun kallo mai dauke da sansar tsana “wallahi bai dauka yayan masu arziki nabi maza ba sai yayan talakawa marasa galihu keyi, ko da yake ta yuwa ba dan kudi take ba tana da manufar yin haka ,sai daya gama mata kallon kasa da sama na banza sannan a matukar tsawa ce yace “ke …!
Ta dago a rikice tana runtse idanunta “ki canza rayuwarki !.
Ta bude idanunta a rikice tana dubansa “yes dake nake ,ki canza rayuwarki ko bake muka gani tare da ajirebi a hotel ba a wacan ranar? Saurin girgiza masa kanta tayi cike da matsanancin tsoro alamun aa .
A zuciye ya daura bakin bindiga a tsakiyar kanta “ni zakicewa aa?kece ko bake bace kafin na fasa kanki yanzu ?eh..ni nice, ta fada muryarta na rawa” very gud tun yaushe yake kwana dake?ta nuna masa yatsunta uku ,ya juyo ya kalli garunmallam dake barin jiki “ka gani ko diyar cikinka da amininka suna kwana da juna mutumin daka yarda dashi na ma barka da wannan ciwon ya isa ya karar da rayuwarka.
tunda jaguwa ya fara magana akan diyarsa nabeela kwalkwaluwarsa ke juya maganar babu ta inda zai karyata tunda gashi ta tabbatar da gaske anyi ,wani duhu ya gilma acikin idanunshi ,zuciyarsa ta jagule kamar ya fasa ihu sai ma yaji duk wani tsoro da fargaba ya kau a zuciyarsa ya daina kallonsu jaguwa ya dawo kallon diyarsa “.
“Eku ku taho da mutun biyu a cikin manyan yayansa maza dasu zamu fita bazamu sakesu ba sai mun kammala aikinmu ,”okay boss nan take eku ya cakumi wuyan Abbas da muhd da sauri suka mike yayi waje dasu “.a tsawace jaguwa yace “Ina makulin get din baya? tsawar da jaguwa ya buga masa ne yasa ya dawo haiyacinsa jikinsa na rawa ya dauko ya bashi har ya juya ya tsaya batare daya juyo ba “zan wuce da yaranka ya rage naka ka kira jami’an tsaro , idan kayi min ganganci zan maka ganganci zan nuna maka sheidancina ya wuce yadda kayi tsammani ,daga haka bai sake cewa komai ba ya da kai ya cigaba da tafiya sauran tawagarsa suka marasa baya suka fice daya bayan daya .
Atare gbdy ahalin gidan suka sauke ajiyar zuciya yau su suka ga tashin hankali babu wanda cikinsa bai duri ruwa ba ,Anas ya jarbi key a hannun jaguwa ya bude musu karamin get ,Ahankali suka fara fita daya bayan daya suka shiga motocinsu dan daman dasu suka zo aguje suka ba unguwa .
sai da suka kammala da abinda ya kai su abuja sannnan suka dawo lagos cike da nasarori bai sheidawa tanwer ya dawo ba ,washegarin randa suka dawo malam mudi yazo sakamakon kiran daya samu daga jaguwa suna zaune a babban parlour’nsa sconpio ya shgo da katuwar ghna most go da hannu jaguwa yayiwa sconpio umarnin ya wuce ya juya da sauri ya bar gurin.“Malam mudi ga kudi nan mun samu nasarar amsowa babu abinda yayi ciwon kai aciki sai ka dauka ka kai wa mahaifiyar yaran allah kuma ya jikan mahaifinsu“sannuka da kokari adnan ,allah ya cigaba da kareka inshaallahu karshenka sai yayi kyua da albarka ,allah yasa ka gama da duniya lafiya sannu da kokari nasan kun sha wahala sosai ? “babu komai malam mudi mun rigada mun saba, kuma mun bada rayuwarmu a irin wadan nan ayyukan, wahala kuma idan da sabo mun saba tunda dama gbdy rayuwar wahala tafi yawa acikinta ni rayuwata na dauketa qaddara,
“Qaddara kuma tana fadowa bawa daidai yadda allah ya hukunto masa sai dai addua tana sausauta qaddara ya karasa maganar muryarsa na rawa “.
“inshaallahu komai zai zama tarihi
Malam mudi ya fada cikin sare wa sannan ta numfasa yace “ya kamata ka duba bangren masu safarar hodar iblis suma iyayen yaran na kuka da wannnan matsalar bayan tafiyarka abuja wallahi kimanin mutanen da suka mutu adalilin shanta bazasu kirgu ba “matsalr manya kasar ne ,
dayawa daga cikin masu kudin kasar nan suna da sa hannu acikin tafiyar da harkar kasuwancinsa acikin kasar nan,bibiyarsu zai ballo ruwa gara abarsu kawai ,”.
“aa kayi iyakar kokarinka zamu tautauna daga baya zanyi maka bincike sosai kafin mu shiga cikin aiki “to shikenan na gode sai naji daga gareka ya mika sama hannu sukai musabaha sannan ya wuce.