KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bayan sati biyu bincike ya tashi zanga zanga dan cp ya bada umarnin a kamo alhj sani fefa da alhj usman ,alhj sani aka fara kawowa akai kaishi dakin bincike aka fara tambayarsa halakarsa da honorable “aboikin kasuwancina ne , ya bada amsa da hakan “babu wata magana ta kudi atsakaninku ? Dcp habib ya tambayesa shiru yayi kafin daga baya yace “akwai Ina zaune honorable Abdulaziz ya kawo min ajiyar kudi amman dolar’s ne na kimanin million dari uku a lokacin ya sheida mana akwai wanda yake nemansa zai kwace kudin a hannunsa amman yarda da amana da yayi mana tasa ya bani ajiyarsu sai dai ya sako sheidu wato alhj Usman galadima ajirebi, garunmallam,bayan wani lokaci kawai sai muka ji labarin mutuwarsa ,sosai mutuwarsa ta girgizamu matuka gabadayanmu mukaje janaizarsa sai dai acikinmu babu wanda ya fito ya fadawa iyalinsa batun kudin daya bayar ajiya muka bi ta kan kudin muka rabe a tsakaninmu kwatsam muna zaune sai iyalinsa wato matarsa ta kira daya daga cikinmu “ ina kudin da mijinta ya bawa daya daga cikinmu ajiya?a lokacin sai muka hada baki mukace aa babu kudinsa ahannumu ,wanda alokacin mu bamu san cewar ya rigada ya fada ma matarsa cewar ya bamu kudi ajiya ba .
Wata biyu daya wuce ina zaune sai alhj usman ya kiramu yace mana wanda ya kashe alhj Abdulaziz ya kirasa yana tambayarsa kudin daya bamu ajiya da budar bakina nace masa yayi blooking dinsa hakance ta kasance yayi blooking dinsa tun daga ranar duk number daaka kira mu dashi muddin ba suna bama dauka ana cikin haka sai wasu da bamu san ko su waye ba suka fara bibiyarmu har sukayi nasara akanmu a yanzu dai gbdy babu wanda baa karbi kudi a hannunsa ba a yanzu abinda ya tsargu a zuciyata duk yadda akayi wanda ya kashe Alhaji Abdulaziz ne ya turo wadan mutanen ya karasa maganar yana Jan dogon numfashi tundaya fara magana dcp da kwararrun maaikata dake fuskantarsa suke sauraronsa har sanda ya dasa aya..”
Suka numfasa atare saboda maganarsu ta bambamta abinda garunmallam ya sheidamusu a wancan ranar da dabam abinda shima ya fada musu dabam suka tsura masa ido yana goge zufar rashin gsky dake tsatsafo masa sannan suka mike suka bar dakin zuwa wanda aka ajiye alhj usman suna shiga kowanne ya samu guri ya zauna akan kujera daya daga cikinsu ya kunna abun daukar magana “da fari ya sunanka?sunana alhaji usman “Meye sanarka ko aikin da kake ?ni tsohon farm sectry ne ,bayan nayi ritaya na koma harkar kasuwanci .
“Meye halakarka da marigayi alhj Abdulaziz ?abokina ne tare mukayi karatu dashi,meye sanarsa?shi dan siyasa ne,babu wata halaka ta kudi dake tsakaninsa dashi?shiru yayi gabansa na faduwa saboda tsananin tsoron tambayarsa daake sai daya dauki sama da minti goma sannan yace “aa.
“Ko kasan irin mutuwar da yayi da inda ya mutu “wannan wace irin tambaya ce ? “ ka tambayeni halakarmu na fada maka bayan wannan ni ban san komai ba dan banga abinda ya hadani da sanin irin mutuwar da yayi ba da kuma inda ya mutu ni dai ance min ya rasu kuma munje munyiwa iyalinsa taaziya shikenan iya abinda nasani kenan “.ya karasa maganar yana goge gumi dan gudun ac dake aiki a dakin bai hana gumi tsatsafo masa da alamun shima dai karya ya shirya musu gbdy suka tattara bayani suka nufi dakin cp “sir gbdy bincikenmu a yanzu ya nuna mana wadan mutanen masu laifi né zaa tabbatar da haka ne idan aka tsananta bincike akansu dan ina ji araina akwai boyayyen abu da suka haka suka binne a tsakaninsu damu bamusani ba .
“babu shakka akwai kuma boyayyayen abun ba komai bane illa sun taru sun kashe mutumin nan dan su dannen kudinsa haka zuciyata tafi raya min cp ya fada cikin zafin rai yana jujjuya a hankali akan kujera “karka samu damuwa zamu tsananta bincike yanzu bari mu hadasu guri daya .
cp yace “kuje kuyi abinda ya kamata duk suka juya cike da girmamawa office dinsu na bincike suka shiga suka fara tsara yadda zasu bullo musu sun dauki sama da awa daya suna tautaunawa sannan duk suka mike a wani babban daki aka hadasu babu wanda bai firgita da ganin danuwansa ba,a yanzu suka fahimci anyi haka ne domin suji bayanin kowannensu allah kasa babu wanda ya tona sirrin daaka binne a tsakaninsu gbdynsu kana kallonsu kasan sun shiga cikin tashin hankali matuka “.
jiki a sanyaye suka samu guri suka zauna gaban kowanne daga cikinsu yana dukan uku uku .
“Me yasa kuka taru kuka Kashe alhj Abdulaziz ? sam ba haka bane yallabai,” alhji sani ya fada a firgice “haka né mana kune kuka kashesa “.garunmallam yayi shiru gabansa na faduwa ya kasa cewa komai ”ku fada mana gsky me yasa kuka kashesa ? mu bamu kashesa ba wannan karon suka hada baki su biyar gurin fadar haka”karku manta yiwa dansanda karya babban laifi né domin idan ya gano gsky da kansa hukuncinsa zai zarta laifin da yayi dan haka muna jinku ku fada mana gsky kune kuka kashesa”.?
Juyin duniya suka tsaya akan basu ne suka kashesa ba “me yasa kuka danne masa kudadadensa to “?shiru suka yi “me yasa kuka takura masa lallai sai ya siyi fili alhalin bashi dashi har kuka hada masa da asiri ?nan ma shiru suka yi .
“Me yasa kuka nemi ku juya masa baya alokacin da yace bazai siya filin ba?duk duniya babu wanda ya yarda dasu tamkarku me yasa ya kawo maku kudadensa ajiya kuka danne ?idan kuma duk kunce ba haka bane ku fada min gskyar abinda ya faru kafin mu fada muku yadda kuka bi kuka kashesa saboda mun san komai akwai sheidu a hannunmu yanzu ya rage naku ku fadi gsky ko kuma mu mufito da gskyar da kuke boyewa .”
Shiru babu wanda yayi magana acikinsu sai zufa data rufe kowannensu gbdy tattare suke da tsoro da firgici alhj sani ya kalli alhj usman shi kuma ya kalli garunmallam haka suka dinga kallon juna “wannan shi ake kira da anyaka tatashi “bari mu tashi mu baku guri kuyi shawara a tsakaninku amman fa kusani mun san komai “.wanda ke maganar yana gama fadar haka ya mike tsaye ya shiga tattara kayan aikinsa har ya juya alhj sani yace “tsaya!
cak ya tsaya tare da juyowa ya zuba masa ido yana sauraronsa “kana ji ko”.
,ami’an bincike wanda ake kira da Interlleget suka cigaba da kallonsu suna karanta yanayinsu,zamu iya gyarota cikin sauki ku fada mana abinda zamu baku a rufe case din nan, grgiza kai habib yayi a ransa yace “tabbas sun aikata abinda ake zarginsu dashi amman dake suna da matukar wayo gyarota suke son ayi muryarsa a fusace yace “kaga munyi muku kama da wadan da zaku bawa cin hanci?duk jami’in dake zagaye daku babu wanda zai anshi cin hanci a hannunku ku dai ku fadi gsky domin mun san komai .
Yana gama fadar haka ya juya sauran ma suka rufa masa baya suna zaune suna kallon tafiyarsu har suka fice daga office din , sannan suka dawo kallon juna suna tunanin yadda zasu kubuta batare da asirinsu ya tono ba “wannan fa shi ake kira anyanka ta tashi “.
Ahankali jaguwa ya fito daga cikin motarsa range rover ya tsaya a bakin titi mile 2 sanye yake cikin kananan kaya riga light blue da bakin wondo gaban rigar bai kulle botir guda daya daga sama ba wanda ya bayyana farar singlet dinsa ,kunnensa manne da waya ,yana cewa “shikenan abu salma gamu mun karaso yanzu haka ina kasan gidan kai nake jira musan yadda komai zai tafi cikin tsari .
“no wannan ba matsala bane agurina wuyarta mu samu damar shigowa komai zai tafi daidai yana kokarin cire wayar a kunnensa on-expeting ya jiyo sautin muryarta ta bayansa “adnan dina ……”
A hankali ya juyo bayansa alokacin har ta karaso kusa dashi sosai suka fuskanci juna wata irin soyayyarta ce ya taso masa daga zuciya yana jin idan babu ita wani mummunar abu zai samesa gdy sai yaji qirjinsa yayi masa nauyi .
ajiyar zuciya suka sauke alokaci daya “ina yini ?ta fada cikin sanyayyar muryarta wacce ta sake kashe masa sansar jiki dan gbdy ji iyayi Kmr ya fixgota zuwa faffandan qirjiinsa yayi mata kyakkyawan masauki .
Kanshi kawai ya samu damar gyada mata yana kallon mutun biyu din dake tsaye abayanta suna kallonta “ yaushe ka dawo ?
“ tun last week ya fada ataikaice ,okay amman shine baka nemi ba gashi kona kiraka baka dauka,baice mata komai ba ya cigaba da kallon bayanta.
a hankali ta juya taga su rukky da muyis yake kallo,” nida yaruwata rukayya ne da doctor muyis abokin aikina munzo mu dan yi siyaya ne daga nan mu wuce gurin shakatawa “fuskar macen bai santa ba koma yace yau ce rana ta farko daya fara ganinta, shi kuwa nmj bazai taba manta face dinsa ba ya taba ganinsa a office dinta ranar daya je daukota ya kaita gidansa aduba masa ita.
“Muna tsaye na hangoka shine nace nazo ,naji dadin ganinka sosai tayi mgnr tana sauke numfashi.