KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

cikin mintuna da basu wuce talatin ba anas yayi knowking ya shigo hannunsa rike da farar leda ya iske jaguwa zaune a falonsa ya daura kafa daya akan daya yayi zurfi cikin tunani ya ajiye ledar ya dafa shi nan ya sauke numfashi da karfi sannan ya maida kallonsa ga ledar dake ajiye “sorry my friend ka rage damuwar nan ka bar tuna abinda ya faru daita,ya zan iya mantawa byn ni ne sanadi ya fada fuskarsa da tsantsar damuwa ,da kyar anas ya lalllabashi yaci arsh da soyayyar kaza ranar sam jaguwa bai yi bacci ba ga tsananin bacci yana ji amman ya kasa saboda so da tausayin tanwer dake nukurkusan zuciyarsa sai faman juyi yake,shima anas bai yi bacci ba duk motsin da jaguwa zai yi zai motsa ya rarrashesa jaguwa karshe ya mike zaune ya kunna wutar dakin yana cewa “anas ina ganin zan koma hospital gara kawai na zauna tare daita hankalina zai fi kwanciya ya fada yana durowa daga Kan gado dariya ce ta kusan subucewa anas amman yayi saurin dannewa dan yasan yana Kuskuren yinta zai janyo wa kansa matsala dan zuciyar maza zata matso.
“kajika da wata mgn kafin iyayenta sonta ne ko me ? ”kaji dan iska nace maka ina sonta ne na damu ne kawai saboda ni ne silar accident din da tayi.”wai kai har yanzu bazaka daina yaudarar kanka ba?wallahi ka guji ranar da zuciyarka zata gaza hakuri akanta,ka guji ranar da nadamarka bazata maka amfani ba , sannan ka guji ranar da hakin yarinyar nan zai kamaka wannan fa zalinci ne qarara kake yi ,jaguwa yayi tsuru yana kallonsa qirjinsa na dokawa ,”eh mana kana zalintar yarinyar nan over “.
.please anas ka bar maganar nan karka min baki ,wallahi babu wani batun baki sai gskyar da kake ki ce nake fada maka kai kafi kowa sani muna fadawa juna gaskiya koda kuwa zamu samu matsala da juna”ya sake yi shiru dan yasan gsky ya fada masa ka koma ka kwanta babu inda kazaje adaren nan dan ko ka koma bazaka samu natsuwar da kake bukata ba saboda iyayenta na tare daita anas ya fada tare da komawa ya kwanta ya juya masa baya .
jiki a sanyaye jaguwa ya kashe wuta ya koma kan gadon sai dai ya kasa kwanciya ya jingina bayansa da abun gado ya janyo pillow har guda biyu ya matse aqirjinsa ,hhhhhh kadan ma kagani jaguwa ba dai taurin kai ba.Bangaren tanwer har safiya tayi bata san inda kanta yake ba duk ta galabaita ciki ciki take fidda nunfashi .”

Tunda sassafe ya tashi ya shirya ya bar gidan sai daya tsaya yayi mata siyayya kayan amfani sannan ya nufi asibitin,ahankali yayi parking din motarsa a haraban hospital ya kashe ya fito zuwa ciki jikinsa sanye da blue black din riga da dogon wondo baki, hannunsa daya daure da agogon fata baki yayinda dayan hannun ke daure da band baki .
Kai tsaye hanyar dakin da take kwance ya nufa qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfin gaske dan bai san su wa zai tarar a dakin ba ,
adduarsa kada ya iske kowa ,cike da natsuwa ya tura kofar dakin ya shiga bakinsa dauke da sallama aiko ya taki saa babu kowa adakin sai ita kadai .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya cigaba da taku a natse kamar bai son taka kasa har ya karaso bakin gadon da take kwance ya tsaya idanunshi na kanta ,jikinsa a matukar sanyaye ya samu guri ya ajiye ledar hannunsa ya zauna still kwayar idanunshi na kallon kyakkyawar fuskarta yayinda take sauke numfashi a hankali a hankali ,
hannunta daya na saman ruwan cikinta kusan 20 minutes yana zaune yana kallon kafin daga baya ya mike a hankali ya soma zagaye gadon da take kwance yana cigaba da kallonta zuciyarsa na narkewa akanta bashi da ja ya rigada ya kamu da matsanancin soyayyarta sai wani ikon allah ne kadai zai fitar dashi amman zai yi iya yinsa ya bawa zuciyarsa hakura domin kuwa samunta ba abune mai sauki da yuwu agaresa ba.
Sama da awa daya yana zariya a cikin dakin amman duk bata motsa ba ya juya ya fita zuwa office din doctor ya cike wasu takardu ya sake dawowa dakin ya jingina jikknsa da bango dakin hade da rungume duka hannuwansa a qirjinsa yana dubanta cike da tsananin tausayawa ,hawayen tausayin kansa suka cika idanunshi ya kai hannunsa ya goge sannan ya dawo kusa daita ya zauna .Ahankali ta fara motsa jikknta yayi saurin mikewa ya tashi ya nufi kofar fita domin kiran doctor …
“Adnan dina …..!”
Ta kira sunansa muryarta a raunane ,ya juyo da sauri ya dawo ya tsaya a gabanta ta sakar masa murmushinta mai bugar masa da zuciya tana cewa “ya kake?”
Ya matsota sosai Kmr zai shige jikinta tare da riko laulausan tafin hannunta cikin nashi wani irin yanayi suka tsinci kansu mai wuyar misaltuwa “ni ya kamata nayi miki wannan tamvayar “.Ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya tare da jin wani sanyi dadi na ratsa sansar jikinta .
a hankali ta canza fuska zuwa ta shagwaba kamar zatayi kuka ” ya ka hade fuska haka ?”Idan bana ganin murmushi akan fuskarka bana jin dadi tayi mgnr idanunta na cikin nashi .
Ya tsuke bakinsa yana duban cikin kwayar idanunta batare da yace uffan ba “zafi nake ji sosai a goshina tayi mgnr cike da shagwaba tana matse hannunshi dake cikin nata.”Karki damu zaki samu lafiya bari na kira doctor yayi kokarin zare hannunsa ta rike gam “in da ka amince munje gurin shakatawa da kai da yanzu kaima kana kwance a gadon asibiti kamar ni”karki damu haka allah ya qaddara kema zaki samu lafiya “kai ma ka kwantar da hankalinka lafiyata lau ,na tsaya ina kallonka ne ban san mota ta taho ba .
Murmushin jin dadin yadda take sonshi ya bayyana akan fuskarsa ya dawo daidai kanta ya daura hannunsa a kanta ,yayinda dayan hannun ke cikin nata yace “is okay zaki samu lafiya amman ki rage wannan son tanwer yayi yawa adnan fa da kike mutuwar so ba kowa bane kamar yadda kika dauka dayan hannunta ta daura akan hannunsa tana shafawa “kaine kake ganin haka amman ni nasan kowa ne kai , kai din mutumin kirki ne mai tausayi inshallah rayuwarka zata canza bazaka kare rayuwarka a wannan sana’ar ba…”
“Ya girgiza kai me yasa kike irin wannan maganar ?ta bude baki zata sake mgn ya katseta “ba wannan tunanin ne agabana ba ni dai ki samu lafiya sannan kiyi min alkawarin bazaki sake min wannan ganganci ba da wani abu ya faru dake fa? “inshaallahu karka damu zan dinga kiyayewa bai ce komai ba ya gyara mata kwanciya ya jingina bayanta tare da sa mata pillow yana mata sannu sannan ya ciro toothpaste peppermint ya matsa akan brush ya dauko farantin silver ya bude goran ruwa roba daya zo dashi ya dawo kusa daita ya kai brush bakinta “ki wanke baki kafin su kawo miki abinci kici sai ki huta dan kina bukatar hutu tayi murmshi tace “bazan gaji da yi maka adduar shirya ba allah ya kawo karshen damuwarka ,ta fada hawaye na cika idanunta .
“na gode ya fada atakaice zuciyarta tayi sanyi da jin abinda yace numfashi ya sauke lokacin daya gama wanke mata baki “allah sarki tanwer kwanciyar hankalinsa shine nata haka tashin hankalinsa shine nata bata son ganinsa cikin damuwa .”

suna zaune suna kallon juna aka turo kofar dakin da teburin abinci baa tsaya dashi akoina ba sai gefenta “adnan !Ta kira sunansa bai ce uffan ba ya maida abun wanke baki ya dawo ya bude plet din farko white rice sai dayan plet din shi kuma stew ne sai dan karamin jug dake dauke da ruwan zafi “adnan !”
Ta sake kiran sunansa bai amsa ba ya tsura mata ido kawai yana sauraranta “ni cikakkiyar masoyiyarka ce shiyasa kaga ina kyamatar aikinka ka yarda dani amatsayin masoyiya zan tsaya maka akowani hali bazan taba cutar da kai ba amman ka mika kanka ga hukuma saboda zan shiga ciki bazasu cutar da kai ba wallahi muddin baka daina wannan sanar ba zaka cigaba da rayuwa ne cikin dar dar, “ har yaushe zaka daina rayuwa atakure? kowa so yake yasan fuskarka ta ainihi “Dan allah ka amince da shawarata bazan gujeka ba zan rayu da kai akowani hali please kace ka amince.
Kansa ya kawar gefe”yana jin kamar ya amince da maganarta sai dai zuciyarsa tace “no karka yarda bakasan a wani hali zaka tsinci kanka ba dan haka ya furta mata “aa ! amman a ranshi yace
inshaallahu zanyi kokarin na rage wasu abubuwa ko dan hankalinki ya kwanta .ya tsiyaya mata ruwan tea a cup ya bata ta sha kadan kana ahankali ya kai spoon din abinci bakinta taki bude baki , ya sake kai bakinta “no bana ci ta fada tana hade fuskar “ya kamo yatsun hannunta da dayan hannunsa yana murzawa ahankali yana sake kai spoon bakinta yadda ya dinga mata ko bata da niyyar ci dole sai yasa ta fara ci a natse ya dinga bata abinci yana kallon kyakkyawar fuskarta yana cigaba da murza yatsun hannunta itama din shi take kallo taci abinci sosai sannan ta kawar da kanta alamun ta koshi ta lura hakan yasa shi farinciki matuka sannan ya ciro hanky a gaban Aljihun rigarsa ya goge mata baki sannan ya dinga kokarin sata dariya bai wani dade ba yace mata zai wuce har ya mike ta tsaidashi ya tsura mata ido kawai suna kallon kwayar idanun juna dady ya shigo tare da rukkaya rike da basket din abinci motsin shigowarsu yasa ta maida hankalinta ga kofar dady ganin dan haka tayi saurin sunkuyar da kanta kasa shima jaguwa kasa yayi da idanunshi kirjinsa na bugawa kamar zai fashe “oh my god tanwer me yasa kika saidani?Cikin yanayi na tashin hankali dady ya karaso ciki sosai yana cewa “waye wannan “?ta dago kanta agigice jin tmbyr dady “da….dady ad…ad….”sai kuma ta kasa karasa maganar “ad…ad “me ya kawoshi ?muryarta na rawa cike da in ..inna tace” shi shine ya kawoni hospital.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button