KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

You’re very stupid da shine ya kawoki hospital “wai tanwer me zakiyi dashi ? wallahi kinji na ratsen muddin baki fita hanyar wannan ba zan mugun saba mki,ganin idanunki zan shayar dake mamaki ,jaguwa ya juya da sauri cikin tsananin tashin hankali ya bar dakin “wallahi bazan hakura na bar masa ke ba sai dai shi hakura ya bar min ke,idan na sake jin yazo hospital dina ko na sake ganinsa sai na sa an kamamun keda shi nafiki iya wulakaci tunda ke bakisan rarrashi ba,muna lallabaki ne ba dan muna jin tsoronki ba amman tunda baki san rarasshi ba zanyi maganinki yana gama fadar haka ya juya fuuuuuu ya bar daki.
Tanwer ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan tace “rukayya ina wayata ta ciro acikin Jakarta ta mka mata number jaguwa ta kira kira daya ya dauka yana cewa “tanwer yaakayi ne? muryarta a sanyayye tace “kayi hakuri please,daakayi me kuma?abinda dady yayi maka,no karki damu komai zai wuce inshaallahu nine fa nayi laifi ina janyo miki bacin rai ga fushin da iyayenki suke dake inshaallahu sai rabaki da wannan ciwon ki zauna lfy ki daina samu matsala da iyayenki .
qasa tayi da murya tana cewa “no karka min haka please “dole zan miki domin duk uba na gari bazai so diyarsa tayi soyayya da mutun irina ba bare har takaisu ga yin aure “zanyi comfuse dinsu,no ke kike daukar hakan da sauki alhalin babu sauki domin wannan shine dabiyar mutane babu uban da yana ji kuma yana gani ya bada auren diyatsa ga irinmu zan rikeki a matsayin kanwa kema kuma ki rikeni amatsayin yaya sai nazo gobe yana karasa maganar ya katse kiran yana jin wani irin ciwo mai tsananin acikin kanshi dan dole na raba zuciyata da tunaninki ta kowani hali.
Rukayya ta matso kusa daita “na zuba miki abinci?no adnan ya bani,gsky shima da alamun yana sonki sosai kinga yadda ya rikice ya shiga tashin hankali lokacin da motar nan ta bugeki har da hawayensa intakaita miki dashi aka shiga emergency room a gabansa akayi miki komai ina ma su dady da mumy zasu yarda da ba karamin sa’ar miji kikayi ba.
dadi ya lullube tanwer nan take taji kashi hamsin daga cikin damuwarta ta kau ta dinga jin sanyi dadi na bin jijiyoyin jikinta “gashi kyakkyawa gsky yana da kyau sosai a yanzu bana ganin laifinki gashi da ganin zai yi tausayi da bawa mace kulawa girgiza kai kawai tanwer tayi lokacin dataji mgnr ruky ta karshe sai dai aranta tace “allah sarki ruky ai kyaun dan maciji garesa suna tare har mumy tazo tanwer bata boyewa mumy komai ba akan zuwan adnan da abinda dady masa “allah mumy ina son shi matuka zafa ku rasani akanshi “rukayya ta daura da nata”gsky mumy yana da kirki ga natsuwa uwa uba kyau shine fa wanda na nuna miki jiya zaune a koridoor dana ce ya taimaka ya kawota hospital mumy kisa baki dady ya barta ta auresa ni sam banga ilarsa nan tashiga koro mata dalilin accident din “
Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke batare data ce komai “dan allah mumy ki dan samu lokaci ki gansa ki kare masa kallo na musamman na san zaki fahimci wani abu attare dashi domin kina da tunani mai tattare da kaifin baseera ta karasa maganar tana kamo hannunta “naji zanyi wani abu.cike da farinciki tan ta kwanto jikin mumy tare kamo hannunta ta matse cikin nata “na gode mumy .
Mumy ta kai hannunta tana shafa bayanta ita daman ta mika wuya fatanta allah ya tabbatar musu da alkhairi za dai tasan hanyar dazaa bi domin komai yazo da sauki “ta mike ta bar rukayya ta dawo gida.

“Kai tsaye jaguwa gidan mlm mudi ya nufa Kansa na ci gaba da sarawa ,a hankali ya zauna akan kujerar kushion dake falo ya daura kafarsa daya akan daya yana shafa kwantaccen sumar dake kwance a fuskarsa yana cigaba da tunanin tanwer “Oh my godness wai meyake faruwa da nine komai ya zama worst a gareni?shine tambayar da yayiwa zuciyarsa.yana zaune malam mudi ya shigo ya zauna cike da girmamawa ya gyara zamansa ya gaishesa “ya dai adnan fatan dai lafiya naga duk kayi wani iri ?lafiya ya bashi amsa yna shafa sumar kansa,to allah yasa mu dace jaguwa yace “ameen yana dan ciza gefen lips dinsa ya numfasa kana ya soma mgana a natse “akwai wasu baynai né malam mudi da kace nazo ?”
“Eh akan dai batun koken din da nayi maka mgn ne har yanzu raina nason kayi aiki akansa karkayi tunani manyan kasar nan dake da hannu ciki kayi dan allah da kuma alumna ,iyayen yara bilaadadin zasu ji dadi “tô shikenan zanga abinda zan iya yi akai .”Yauwa kayi kokari kayi wani abu nasan dakatar dasu ba komai bane agurinka ai baka manta da dukkanin bayanan dana baka ba?”eh ban mata ba nima kabani lokaci zan sake zurfafa bincike idan lokacin fara aikin yayi zan nasar maka nan suka cigaba da tautaunawa mlm mudi yasa yarinyar safna ta kawo masa abinci.”

mumy na komawa gida ta zubewa kasa tana zubar da hawaye a gaban dady a matukar tsorace yake kallonta “ka daina mamakin ganina a durkushe agabanka ba dan kai na durkusa ba saboda rayuwar diyata nayi domin zan iya komai akanta kasani nasani diyarmu ta fada iftilain soyayya “kasa hannu mu san abunyi akan lamarin tanwer , rayuwar diyarmu is very very important agurinmu , kayi hakuri bazan juri ganin mutuwar tanwer ba gara na mutu na barta.
Dady dake zaune yana kallonta da karanta yanayinta ya numfasa yace “ karna sake jin kin zo min da makamanciyar magana irin wannan .“ka duba irin damuwar da zan shiga idan na rasata “kin dade baki shiga damuwa ba indai akan tanwer da wannan tsinannan yaron ne ya fada a matukar fusace cikin muryar kuka tace “tanwer ta tabbatar min da zamu iya rasata akanshi “wallahi zainba dana aurawa dan fashi diyata gara na barta ta jaraba mutuwa ,bari na fada miki wani abu tanwer ta fada miki haka ne dan ki amince ta auresa amman ko kadan bazata taba gwada mutuwa ba , da ta daukemu da mahimmanci a rayuwarta da tabi umarninmu don haka muma yana da kyau muyi duk yadda zamuyi ta ciresa azuciyarta batare da mun cika mata burinta ba ,Ko kuma ta zaba ko mu ko shi amman muddin ina raye bazan amince da wannnan auren ba idan ke mahaukaciya ce nida hankalina idan kuma taji ta gani lallai sai shi ki barta ta mutu mu huta”.A firgice mumy ta tsura masa ido tana kallonsa tace “yanzu kana ganin wannan maganar daka fada babu wani gyara a ciki?taya zamu haifi yarinya da cikinmu ace kuma mu barta ta mutu ?kafin ta karasa maganar har dady ya mike ya fita daga dakin…fashewa tai da kuka …


A hankali anas ke taku acikin haraban gidan jaguwa dake magodo hannunsa rike da goran band energy drink yayinda kamil ke gefensa “shikenan nan aikin da muka fita jiya dominsa ya rushe?”
“Bakaga uban gayyan baya cikin haiyacinsa ba inji cewar anas ?
kamil ya numfasa kana ya cigaba da magana “yanzu yana ina dan tun safe ban sanyashi acikin kwayar idanuna ba?”ya tafi zuwa hospital duba lafiyarta anas ya bashi amsa tare da kai goran bang bakinsa ya kurba yana lumshe idanunshi .
kamil yaja ya tsaya yaki cigaba da tafiya yana dan dukan kafadan anas shima anas din tsayawa yayi yana dubansa “naji ance kaima ka fara batun ajiya iyali ga kuma jaguwa shima da alamun zai auri yarinyar nan zakuyi aure ku barmu abaya muna yawon akan titi ?”.
“Kuma kuyi kokari ku ajiya dayawa masu irin alqallarmu suna da iyali wasu kuma basu dashi basa ma son su ajiye saboda yanayin kasar dake tattare da tashin hankali zasu iya riskar kansu a hannun hukuma amman ni dai gsky zan yi aure ban san dalili ba hakan nan nake jin araina gara nayi aure shiyasa ma kaga na rage wasu abubuwa “.
“A ina ka samo matar ne ?”
“Kuma yarinyar tana sonka?”kamil yayi masa tamvayar ajere yana tsaresa da idanunsa murmushi anas yayi masa sannan ya cilar da goran hannunsa ya dafa kafadan kamil “anan garin kuma yarinyar tana sona sosai nima ina sonta ina jiran jaguwa ne idan ya gama ruwan idonsa sai ayi magana domin ina son muyi aure rana daya .”ya karasa maganar yana dariyar karyar da yayi masa .”
kamil ya masa gyada “duk kun zama yan soyayya dai shima jaguwa na lura yana qaunar yarinyar nan sosai ka gansa lokacin da tayi accendent ya dauketa kmr jinjira yasata a mota yana kuka ya kaita hospital sannan yaki barinta yana tare daita har dare har sai da iyayenta suka zo gashi tun sassafe ya sake fita zuwa gurinta “wannan shi ake kira soyayya sai dai shi yallabai din bai yarda yana cikin soyayya ba da aka tsareshi zai ce maka ba soyayya bace tausayi ne “.lallai kuwa ai duk inda tausayi yake soyayya tana makale daita a natse suka cigaba da takawa har zuwa cikin babban parlour gidan .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button