KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Aa ammi adai yi min hakuri su ayi nasu ni nayi daga baya idan allah ya nufa “Adnan !
Ta kira sunansa cikin yanayin nason yasan maganar da zatai yi tana da mahimmanci ya natsu sosai “ka fada min gaskiya ko baka da lafiya ne ?qirjinsa na dokawa yayi kasa da kansa yana jin wata irin matsananciyar kunya shi da a yanzu a hannu yake da zai samu mace ma sai tayi mugun jin jiki a hannunsa “tambayarka nake karka barni cikin duhu ko kana da wacce zaka fadawa damuwarka né data wuceni?ya girgiza mata kai alamun a’a “okay ina jin ka? .
“lafiyata lau ammi “Neman mata kake yi da aure ya gagareka ?ya sake dagowa a rude yana cewa “haba ammi why?haba ko gskiya mai cikakkiyar lafiya da shekaru irin naka going to 40 ai dole ya bukaci ya ajiye iyali amman tunda kafi son nayi maka auren dole zan maka yayi murmshi” haba ammi ai bayiwa nmj auren dole ta hararesa “ai kuwa zaa fara ta kanka ya riko hannunta cikin nashi “hakuri ammi kiyi min addua kawai idan da rabon zanyi zanyi ne ”sun dauki minti shabiyar suna tautaunawa sannna suka fito anas na nan zaune a inda suka barshi cikin zullumi suka samu guri suka zauna jaguwa ya fara magna a hankali.

Tunda jaguwa ya fara magana kanshi na kasa amman daya zo gurin bashi auren hally da sauri ya dago kansa gabansa na faduwa yana duban ammi da jaguwa A hankali ya motsa bakinsa “wayyo allah ammi ni akawa wannan kyautar? suka daga masa kai “na gode na gode lallai ke din mahaifiya ce ya fada cke da rauni dan sam bai tsammaci wannan karamcin daga garesu ba “karka damu anas nasan halima zata samu dukkan kulawar data dace a hannunka “duk da haka ammi na gode fuskarshi cike da murmushi mai hade da rauni,hankalinsa ya kwanta lallai wadan mutanen biyu suna matukar qaunarsa bai yi tsamaninn ba ,bai ma dauka aurensa me yuwa bane ya matso gaban ammi ya dafa kafafunta ya ma rasa me zaice mata kawai digar hawayensa taji “kaga anas tashi tashi bana son ganin hawayenka ai kafi karfin komai agurina anas .”
a hankali jaguwa da ammi suka mikar dashi hawaye yake amman kana ganinsa kasan yana cikin farinciki ya rungume jaguwa ajikinsa yana kuka “na gode abokina kuma danuwana na gode da wannan karamci .”
Binsu tayi da idanuwa kamar itama zata sanya kuka “please ka daina zubar da hawaye murmushi ya dace da ango ya dagoshi ya ciro hanky ya goge masa hawaye kana ya zaunar dashi shima ya zauna a kusa dashi yana tsokanarshi ,”kyalesa ai kafi shi tunda kafishi tunani mai kyau maganar ammi tasashi jin kunya ya sunkuyar da kanshi yayi qasa da kanshi zuciyarsa cike da samun natsuwa.

“Halima taji ammi na kiran sunanta da sauri ta maida hankalinta waje tana amsawa sallamar hally ce ta katsesu ta karasa gaban ammi ganinta kunya ta sake kama anas ganin yadda kunya ke dawainiya da anas yasa ammi mikewa tsam ta basu guri tasan adnan zai hadasu ya fayace mata komai ammi na tashi jaguwa ya nuna mata guri kusa dashi yana tambayar “hally ko kina da wanda kike so ?tambayar ta dan rikitata amman tayi karfin halin cewa aa bani da ko…..”maganar ta makale mata saboda hada ido da sukayi da anas nan ya zayyono mata niyyarsu ya karashe maganar me kika gani ?
“babu komai yaya na amince tunda kana ciki dan nasan zaka tsaya min a komai nawa bazaka barni nayi kuka ba ta karasa maganar muryarta na rawa”
“Wannan haka bazan taba barin kiyi kuka ba muddin ina raye ya mike tsaye yana dauke hawayen idanunshi kujerar ta saura daga anas sai hally ya kama hannun anas dana hallay ya hade guri daya sannan ya daura nashi a saman hannunsu na gode miki kanwata da baki zuba min kasa a ido ba nayi matukar murna da kika amince da zabina inshaallahu zakiyi rayuwar farinciki a gidan aurenki kamar yadda shafiq take yi sannan ya juya ya kalli anas .
“Anas ga amanar rayuwata kai kasani kannena sune rayuwata kuma farincikina saboda bani da kowa sai su da mahaifiyata ka rike min ita kamar yadda nake rike daita karka satayi kuka matsayar ka cutar min daita kasan abinda zan iya yi akanta ka rike amana anas duk da nasan kai din mai amana ne amman shi zaman aure dabam ne ya karasa fadar mgnr yana murmushi mai hade da hawaye bancin amminsa ce ta yanke wannan hukunci da duk amanar dake tsakaninsu bazai iya daukar hally ya bashi ba domin rayuwarsu tana cikin garari da hatsari.”

Duk yadda anas yaso ya daure kamar yadda jaguwa yayi ya kasa idanunshi suka cika da ruwan hawaye saboda a zahiri yake hango damuwa a fuskar amininsa badan rashin yarda dashi ba sai d’an qaunar da yake wa yaruwarsa da kuma irin hatsari dake tattare dasu amman dake bai son hally ta fahimci akwai wata a kasa yayi saurin dukar da kanshi ya kife akan hannun jaguwa hawayensa na dinga a hankali yaji tumin hawayensa dan haka cikin dabara jaguwa ya danne nashi ya kai hannunsa daya yana gogewa hallay hawayenta muryar anas a raunane yace “inshaallahu bazan cutar maka daita ba ,zan bata dukkanin kulawa fiyye ma da wanda ta samu agurinka .
“Kefe hally zaki kular min da wannan marayan? ya fada yana kallonta itama kanta na duke sannan ya zare hannunsa wanda ya bawa anas damar wasa da hannunta yana yamutsa tafin hannunta dake cikin nashi da sauri tace “Nayi alkwari inshaallahu bazan baka kunya ba yaya .
Jaguwa ya sauke ajiyar zuciya alokacin da hally ta zare hannunta hakan ya bawa jaguwa damar zama a tskaiyarsu a hanakli ya canza hira wanda hakan ya bawa ammin da hasera dawowa falon aka cigaba da hirar dasu har sadiq ya dawo daga aiki shima aka cigaba dashi anan suka yi sallah suka ci abinci sannna jaguwa ya samu damar kebewa da sadiq yayi masa bayanin hukunci da ammi ta yanke shima dai goyon baya yayi “shikenan sai ka sheidawa ita yarinyr da kake so zaa zo neman aurenta sai ka turo min adress dinta ni kuma zan turawa malm mudi yaje inason a saka sati biyu ayi komai agama “kai fa yaya gaky naso ka fara yi kafin ni ? idan zata jira har kayi shikenan idan bazata iya ba ta samu wani “ karka damu Sadiq aure fa lokaci ne kayi naka Allah yasanya alkhairi bashi da yadda iya tunda abinda yayansa ya zarta kenna sukyi sallma da juna .

Acikin mota zaune kawai anas yake amman shi kadai yasan irin dadi da farinciki da yake ciki shi kuwa wani aikin alkhairi yayi da allah zai bashi auren hally ?ya tambayi zuciyarsa jaguwa ya juyo ya kallesa “ latest ango Kenna yanzu dai tunani da kukan aure ya kare tunda zakayi aure “uhm wallhi bakaji farincikin da nake ba babu abinda zan iya saka maka dashi ka gama min komai abokina amman kai ya kamata ka fadawa su jubi ko?
“Zasu sani amman ba yanzu ba sai lokaci yazo daf,kana nufin sai ana gobe daurin aure ?eh tô zai iya kasancewa haka anas yayi murmshi yana dafa kafadan jaguwa “wallahi ina cikin farinciki mara misaltuwa yau,ka maida hankali fa kana tare da uba,siriki kuma babban yaya…..”ya karshe maganar yana dariya shima anas dariya yake “tô ni yanzu wa zai je min neman aure?jaguwa ya juyo ya kallesa sannan ya maida hankalinsa kan tuki yana cewa “Meye amfani na ai nine uban amarya kuma uban ango suka sake kwashewa da wata dariyar suna tabafawa “naso ayi auren da naka abinda sadiq yayita naci kenan kuyi naku ni idan da rabo nima zanyi ne ni wallahi gani nake kamar zamu saka yaran mutane a matsalane “.
“ kai kake ganin haka komai dan sauki da nazari ne munyi aure sai mu bar abinda mukeyi shikenan ,”kai kake ganin shikenan ya fada yana karya kwana “allah shikenan adnan babu fa wanda yasan ainihin fuskarmu byn tanwer ita kuwa nasan ko kasheta zaa yi bazata fada ba “.haka dai ka fada mutun fa abun tsoro né nifa da kai kadai na yarda wata mace meye meye duk aikin banza ne basa gabana dan zasu iya yaudararka kasan mata suna matukar qaunar aitime idan suka rasa wannan aitime din na namiji shikenan zasu iya komai ciki har da juya masa baya “amman tanwe na matukar qaunarka bazatai haka ba da wannan tautaunawa suka karasa gida.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button