KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Bayan kwana biyu jaguwa ya tura malam mudi gidansu zuhra nemanwa sadiq aurenta tare da saka rana a cewarsa sati biyu sai dai iyayenta suka nemi alfarma aqara musu sati biyu akai ya zamo sati hudu, malam mudi bai kira jaguwa ya sheida masa abinda sukace ba ya zartar da hukunci sannan ya sheida masa.Tun byn zuwan jaguwa da anas gidansu zuwansa biyu domin su gana da hally sosai ya samu karbawa ta musamman agurinta sai dai baya iya cewa daita komai sai dai ya tasata gaba da kallo yana kallon zukekiyar budurwa agabansa amatsayin matar da zai aura ba haka zai dauki lokaci mai tsawo sannan yayi mata sallama

Da misalin karfe takwas na dare hally tana zaune sakonsa ya shigo dan haka ta shirya ba wani kwaliya tayi ba simple make up tayi ta saka doguwar riga sai veil ta shiga bedroom din ammi kafin ya karaso ammi na kokarin zama akan bedside drawer kenan ammi taganta “kai masha allah yau kuma kwaliyar dare ce ko dai dana zai zo ne ?”gsky dana ya cire tuta abun ya min dadi daya samu karbuwa cikin muryar shagwaba hally tace “ammi Please ki daina cewa ina son shi ..”
“Gsky ban yarda ba wa zai samu kamar bin malik yace bai so ?ta fada tana dariya itama hally dariya tayi “kai ammi har da wani canza masa suna?kwarai kuwa kema ki dinga kiransa da haka “ uhm ammi mutumin ma da ko magana bayayi sai dai ya wani tsura wa mutane ido ni allah kallonsa ya fara damuna tayi mgnr Kmr zatayi kuka ,karki ga laifinsa bai saba bane shiyasa baki ga yayanki ba har yanzu ya kasa tsaida matar aure shi ai yamayi kokari ke zaki dinga jansa har ku saba kinji autata “.
“allah ammi Kmr yafi yaya shi fa kamar kurma ne ammi ta dauki pillow dake kusa daita ta jefa mata tai saurin matsawa ya sauka a kasa “kinganki auta Kmr bakya mgn nan kuwa manyan zance ne abaki “to gsky ni idan nayi shiru ai sai yayi mgn, ammmi ta sake yin murmushi tana cewa “shikenan zan fada masa ya dinga miki hirar soyayya tai saurin zaro ido waje “kai ammi ni ban sakaki ba ki rabu dashi mu tafi a haka ,ammi ta riko hannunta “karku tafi ahaka kiyi Kmr yadda nace idan yayi shiru kiyi masa hira nasanki da labaru masu maana tun yanzu ki sharya wanda zaki bashi a hankali a hankali zai saba “to shikenan ammin zanyi kokarin “allah yayi miki albaka muryarta a raunane tace “Ameen !
Shigowar sako ta sake ji ya shigo wayarta ta duba sunansa ta gani “gashi nan ma ya karaso bari na tafi “karki dade kinji auta “okay ammi sai na dawo “ta fada tana kokarin barin dakin ammi tabi bayanta da kallo tana murmushin jin dadi ita kanta diyarta na matukar burgeta kasancewar bata da rawar kai komai a natse take yinsa gashi kalekalen duniya basu dameta ba .

A haraban gidan ta hangosa a parking space hannunwansa rungume a qirjinsa kanshi a kasa yana jiran ta , fuskarta da dan murmushi ta karasa gurinsa tana cewa “a min afuwa ranka shi dade kallonta yayi da idanunshi batare da yace komai ba “muje daga ciki ko ta fada tana juyawa yabi bayanta da kallo komai nata yayi masa sosai tana da shape mai kyau irin matar da yake kwadayin samu kenan gashi allah zai cika masa burinsa a hankali ya soma daga kafafunsa ya biyota kusan atare suka shigo parlor ya zauna akan kujera ita kuma ta karasa ta shiga Kitchen ta dauti tire ta bude fridge ta dauko ruwa mai sanyi da maltina da glass cup ta daura akan karamin tire ta dawo inda yake ta ajiye akan center table ta matso dashi gabansa kana ta dauki remut din ac ta qara karfin ac sannan tayiwa kanta
gurin zama a kusa dashi tunda ya zauna idanunshi ke kanta kamar koda yaushe yana sake yabawa da natsuwarta ganin yau ma a kallonta zai kare bazai yi mgn ba ta waigo suka hada idanu murmushi ya bayyana akan fuskarta “kayi shirru kana ta kallona ? ta fada cikin tsananin jin kunya tare da sunkuyar da kanta kasa,stil dai kasa magana yayi saboda rashin Sabo shi kansa abun na damunsa yana son cewa wani abu amman sai yaji ya kasa .
a hankali ta Sake waigowa “ya anas !ta kira sunansa tana kafeshi da kyawawan idanunta masu matukar hargitsa duk wani lafiyayyen nmj bareshi da yake cikin tsanin bukatar kasancewa da mace ,cikin sanyayyar murya yace “na’am my princess hanakalinsa na kanta “ tai murmushin jin sunan daya kirata dashi “me yasa bakason magana ?ta jefa masa tambaya murmushi ne ya subuce masa yayinda dimples dinsa suka lotsa yace “ba komai “
Gyara zamanta tayi “ko kai ma kmar yayana ne bayason magana hasalima yawon magana na damunsa ? “gsky ba kmrsa bane na dan fi shi da kadan “ sannu a hankali suka fara hira ta tsiyaya masa maltina ta mika masa har goma na dare suna tare a karshe yace zai wuce gida yayi mata sallama ta rakosa har inda motarsa take ya shiga ya wuce sannan ta koma ciki .”
cikin kankanin lokaci wata shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin anas da hally duk wanda yasan anas idan ya gansa yanzu zai fahimci yana cikin farincki akwana a tashi babu wuya agurin allah har sati uku ta wuce wanda tuni an fara shirye shirye auren mutun biyu a gidansu jaguwa acikin satin jaguwa ya sheidawa sauran abokansa batun auren Ana’s sun sha manaki kwarai da gaske da jin abinda ya fada masu gbdy sai da suka bar abinda suke yi suka juyo suna kallonsa cike da mamaki suka hada baki suka ce “yaushe aka sa lokaci da har bikin yazo bamu sani ba sai yau ? anas yayi shiru yana jiran yaji me jaguwa zai ce “nima yadda kuka ji haka naji hukunci ammi ne itace tabashi mata “kana nufi a gidanku aka bashi mata? Inji cewar jubi jaguwa ya gyada masa kai alamun” Eh!
“Shine dan munafurci kwanakin baya nake tambayarka kace min a wani guri kasamu mata to meye idan ka fada mana kaje kayi shishigi ne aka tausaya aka baka mata? kamil ya fada yana Jan dogon tsaki .“Ku tsaya ku fahim….”dan allah malam ka mana shiru bama son jin komai ku cigaba da yi mana munafurci ai akwai ranar kin dillanci.
“kaga anas bana son ka sake cewa komai dasu kofa a bude take ga duk mai bukatar aure ban hanashi ba sannan ga dinkunanku ya ajiye musu babbar leda fara akan table din dake gabansu Kaya ne ya dinka musu gbdy kuma iri daya ,na anas ne kawai ya bambamta wannan alamari ya kunno wata wutar kiyayya atsakanin anas da sauran abokansu uku
Wani irin tafasa zuciyarsu keyi musu a qalla sun dibi mintuna kafin su soma contronling kansu sai dai gbdy kana kallonsu moond dinsu ya canza sabanin na dazu cikin tafasar zuciya suka mike suka bar gurin batare da sun dauki kayan ba “kagani ba daman nasan sai sun nuna rashin jin dadinsu ?
“shiyasa naki a fada masu tun farko,ni wallahi da kasani ka fada musu tun lokacin da yanzu basu yi fushi haka ba “kai har yanzu bakasan me ake cewa rayuwa ba ina da dalilin da yasa nayi haka barsu kawai fatan alkhairi a aurenka “.

“gsky na damu ina son zaman lfy banason wani tashin hankali su yanzu gane suke shishigi nake maka”Karka damu zanji dasu koda suka shiga daki suka kasa tsaye suka zaune wannan bamvamci da jaguwa ke nuna musu yana taba ransu atare suka tsaya rike da kugunsu gbdy suka fara tama yadda zasu shiga tsakanin anas da jaguwa .”
February 27 aka fara gudanar da biki da kamu aka fara washegari ya kama asabar akayi wankin amarya a wani katafaren hall dake cikin ikeja mario , bakaramin kyau amare da angwane sukayi ba jabir da jubi da kamil sun saki ransu sunyi barin kudi tamkar babu komai aransu hakan kuwa yayiwa anas dadi dan shi jaguwa gbdy a ankare yake dan haka bai wani saki jiki sosai ba ,da dan sauri ya fito haraban gurin sakamakon wayarsa dake ringing ya dauka da sauri tare da bude motarsa ya shiga “mun samu labarin an turo dan leken asiri gurin bikin da kukeyi ku ankare da kyau, domin jami’in sirri ne kuma yasan aikinsa burinsa bai wuce yaga ya kama masu laifi ba .
”okay ko zakaiya min discrebing dinsa? ya fada yana cizan lips dinsa “eh yana nan wani baki dogo mara kiba mai fashin goshi ko ta hanyar sa muku ido ma zaku iya ganesa “idan akwai wani bayani zan sake kiranka na sanar maka “okay thanks ya katse kiran ya fito a natse ya kulle motarsa ya koma ciki ya kirasu daya bayan ya fada musu ya karasa inda anas yake zaune da amaryarsa yayi masa magana a kunne cikin rada dan haka gbdy suka baza ido domin gane ko waye .
Mutun daya jaguwa ya gani me irin kwatance daaka bashi na jami’in sirri sai dai hankalinsa baa kansu yake ba yana gurin wasu ne daga dangin amaryar sadiq abokan yayan amaryar ne abinda ya bawa jaguwa mamaki shine gali mjin kanwarsa shafiq ne da wannan kwatancen “to daman shi din jami’in sirri ne ko me ?shi a iya saninsa da bincikensa kafin ya bashi auren kanwarsa dan canji ne “ Shiru yayi yana sake kare masa kallon tsab har sanda mutanen suka mike tsaye da sauri suka fita suma ko an akarar dasu ne akan wata alqallarsu dashi bai san ko wace iri bace yasa suka tashi bai bisu ba ya cigaba da kai kawo cikin mutane gbdy hankalinsa ya tattara shi gbdy akanshi can wayarsa ta sake kara ya sake fita yana amsa kira “a she ba gurinku aka turosa ba wasu masu safarar koken ya biyo ,ka bincikko min sunasan ina son nasan sunansa kuma bana son a dauki lokaci ,alright karka damu zan binciko min cikakken sunansa da komai nasa har ma da hotonsa zan turo maka yana gama jin abinda wanda ya kira ya fada ya katse kiran sannan a hankali suka watse suka bar mutane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button