KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a hankali ajuwon yake direct din direba har suka karaso igando tun daga nesa ya nuna masa gidan suna gama isa bakin tangamemen get din gidan ya tsaya tare da yin hon ,mai gadi ya mike da sauri ya leka ta karamin hujin get ganin bai san motar ba ya rufe ya fito gbdy alokacin har ajuwon ya fito daga cikin mota ya mika masa hannu shima mai gadi ya mika masa hannu suka gaisa “dan allah ko jaguwa yana around“.?
“Eh yana nan sai dai bai sheida min cewar wani zai zo nemansa ba amman zaku iya kiransa idan yasan da zuwanku zai kirani,“no ka bari mu shiga da motar ciki sai kayi mana iso gurinsa “A’a bari dai na fara sheida masa idan ya amince babu matsala sai ku shigo din wa zance ?.
ajuwon da maganar mai gadi ta bata masa rai ya dai daure ya motsa bakinsa da kyar“kace masa ajuwon ne mu zo ne tare da alhji tajudeeni“to shikenan ka bani minti biyar zan dawo yanzu mai gadi ya juya da sauri ya koma ciki shi kuma ajuwon ya koma jikin mota ya tsaya rungume da hannunwansa alhji tajudeeni yayi wani glass din bangaren da yake zaune “tsayuwar me mukeyi anan ?.
“Wai sai ya nemi izininsa sannan zai bari mu shiga “ ya kalli get din gidan yanawa gidan wani irin kallon tsana sannan yace “wa dan fashin yake da wannan matsayin ?ai fa ya wuce duk wani tunanin mutane gagara badau ne dan dai bakasan shi bane shiyasa amman idan kana jin oba loud ,Ijile , jagu…..“.
tsakin da alhji tajudeeni yaja yasa yayi shiru yana kallon wani gefe yana dariyar mugunta a ransa yace “kadan ka gani yau dai matsayinku yazo inda bashi da amfani.”
mai gadi bai dauki lokaci ba ya dawo yana cewa “wai yace ku shigo amman banda motar ku “.
ajuwon ya sheidawa alhji tajudeeni abinda jaguwa ya fada nan ya sake shiga tashin hankali matuka har ya shigo cikin hadadden falon da’akayi musu masauki mamaki yake .parlour yayi shiru kamar yadda alhj tajudeeni da ajuwon sukayi sai dai idanunsu na aikin karewa falon kallo ne komai tsaf sannan kuma a tsaftacce a tsare ,ahankali suka fara jiyo kamshin dadaddan turare na kamfanin flower mai dadin kamshi a natse alhji tajudeeni ya waigo idanunshi zuwa dogon koridor dake gefensa da jaguwa idanunsa suka fara yin tozali cikin wando da rigar shan iska mai hannun singlet mai azabar kyau .”
anatse ya cigaba da taku cikin isar nan nashi yayinda abokansa ke biye dashi kowannensu cikin kanana kaya kallonsa yake har sanda ya karaso ya samu guri ya zauna ya daura kafarsa daya akan daya yana girgiza wa haka ma abokansa banda anas suka yiwa kansu gurin zama eku ya karaso gabansa cike da girmamawa ya ajiye wayoyinsa akan hannun kujerar da yake zaune sannna ya koma cikin yan’uwansa suka tsaya rungume da hannunwansu akirji .”
Shiru babu wanda yayi magana acikinsu hakan ya tabbatarwa alhji tajudeeni lallai yana da izar da aka fada masa yana daita ,kiran daya shigo wayoyinsa ne ya katse masa zance zucin da yake anas ne dan haka yayi hanzari ya daga dan tun safe bai ji sautin muryarsa ba kuma ya kirasa bai shiga ba “anas ina ka shiga ne nayita kiran wayarka bata shiga ?.”
“subhallah ya fada wanda hakan ya janyo hankular sauran abokansa gbd suka tattara hankalinsu da natsuwarsu garesa “okay allah ya baka lafiya hope kasha magani? Okay shikenan sai ka shigo yana gama wayar ya katse ya kai hannu ya zaro bindiga akarkashin kujerar da yake zaune ya rike yana kallonta yana shafawa still bai ce komai ba .”
da idanu yayiwa sky alamar ya kunna masa tv ya karasa da hanzari ya kunna ya dauko masa fear less mai sanyi ya ajiye akan karamin table ya janyo gabansa ya koma matsayarsa ya kame .
Jaguwa ya gyara zama ya fuskanci tv yayi kamar bai san da zaman wasu halittun mutane agurin ba har lokacin da anas ya karaso cikin shiga ta kamala ya mika musu hannu d’aya bayan d’aya sannan ya samu guri kusa da jaguwa ya zauna suka kalli juna ya kai hannu ya shafa wuyansa yaji zafi sosai alamun baya jin dadi “kaji abinda naji kuwa ajikinka anas ?jikinka kamar garwashin wuta sky kawo masa magani ya sha dan da alamun bai sha ba”.
Sky ya juya da sauri ya bar gurin “nan su jubi suka fahimci shine bashi da lafiya gbdynsu suka masa sannu ya amsa yana dafe kansa dake masa mugun sara sannan suka sake maida hankalinsu akan wayoyinsu yayinda alhji tajudeeni ya maida hankalinsa kacokan akansu duk ya qagu jaguwa bai masa mgn ba gbdy sai yaji ya munzanta agurin har yayi daya sanin zuwa ajuwon ya kai bakinsa daidai kunnensa yayi masa magana cikin rada “wannan daya shigo yanzu shine anas na hannun damarsa kai kawai ya gyada alamun ya fahimta .”sky ya dawo hannunsa rike da magani da ruwan roba ya mikawa anas cike da girmamawa anas ya mika hannunsa ya amsa yana masa godiya sannan ya sha, jaguwa ya sauke numfashi yana sake masa sannu idan bakaji sauki ba sai muje gurin sadiq ya duba min kai “inshaallahu ma zanji sauki daman rashin ban sha magani ba .”
Gyaran murya alhj tajudeeni yayi yace “jaguwa kake ko wa kana kallon mutane amman kayi kamar baka san da zama na ba sai faman uzurin gabanka kake ?jaguwa bai dago ya kallesa ba yace “kar nayi uzurin gabana acikin gidana abun ikona? “ ka kuwa san ko waye zaune a gabanka ? sai lokacin jaguwa ya dan dago ya kallesa a wulakance kana yayi murmushin irin nasu na goggun yan duniya yace “waye kai !?
“Ni kakewa wannan tambayar?idan baka sani ba shi wannan dake zaune shima bakasanshi ba ?
“Eh! “ya fada kai tsaye yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa tare da kafesa da idanunshi.
ganin yadda jaguwa ya hassala ya canza cikin kankanin lokaci ya dawo tamkar zaki yasa alhj tajudeeni ya sausauta muraya “ok shikenan daman ba wani abu bane ya kawoni sai akan maganar shigo min da magani “amman ai na fada ma wannan banzanyi ba …”
“ni kuma kai nake son kayi ya karasa maganar yana dubansa tare da kwabe fuska alamun bai isa yakiyi ba “ to bazan yi ba ya fada atakaice sannan ya gyara zama ya jingina jikinsa da kujerar dayake zaune yayi crossing leg’s dinsa ya rungume hannunwansa duka akirji yana dubansu a kaskance.
Alhj tajudeeni yayi shiru yana kallonsa yana nazarinsa kafin a hankali ya cigaba da magana “
hakika zillarka ta matukar burgeni sai dai ko bakayi wannan alqallar ba zamu samu wadan da zasuyi .”
“bazai yiwu ba wannan aikin ni kadai ne zan iya duk kuma wanda zaka sa ka tabbatar da sai ya shiga hannun hukuma idan kuma bai shiga ba ni nan zan maka fashinsu na kaiwa hukuma “tô meye bako aciki yansanda? yansanda karnunka farautarmu né su din tamkar dabbobi ne agurin mu ,kowa yasan bukatarsu da burinsu kudi ne kuma akwai su ,idan bakasani ba bari kaji dukkanin wata alqalla da mukeyi acikin garin nan yansanda suna da kaso mai tsoka aciki dan haka ko da kai ko babu kai zamuyi abinda mukayi niyya kuma babu wanda ya isa ya hana wannan kayan shigowa su iso gareni”. ya karasa maganar yana kallon jaguwa a dage domin sake tabbatar masa da bai isa ya hana aiwatar da nufinsu ba “.
“Lallai kun fargab da d’an zakin da bai shirya karawa da ku ba, babu shakka wannan niyyar taka bazai taba yiwuwa ba domin kuwa ina da yakinin allah bazai baku saa ba a duk lokacin da ubangiji ya baka wata kyakkyawa dama kayi amfani dashi gurin kyautatawa gobenka idan ba haka ba zaka riski gobenka a gurgunce ya karasa maganar a matukar fusace cikin yanayi na tashin hankali yana dukan hannun kujerar da yake zaune wani irin numfashi ya fesar mai zafi kana ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tare da lumshe idanun shi “anas ya matso daf da jaguwa ya riko hannunsa cikin nashi yana cewa“Wannan shine tajudeeni din ?
“Tajudeeni!?”
Alhj tajudeeni ya maimaita sunansa da anas ya furta without respect yana dubansa ahankali Jaguwa ya gyada masa kai alamun eh ! “wa ya fada maka ana tankawa marayan dan kuwkuyo idan yana haushi ?sam ba’ayi sai dai abarshi yayi haushi iya yinsa a karshe zuciyarsa ta buga “ya fada yana juyowa tare da nuna alhji tajudeeni da dan yatsantsa alamun gargadi .”
Shi kuwa alhji tajudeeni murmushin gefen baki yayi yana cewa “rayuwa tana cika muradai kala dabam dabam sai dai kuma ba kowa take yiwa haka ba dan wa……..“
“tashi ka bar nan sannan kar na sake ganinka bare karnunkanka idan ba haka ba za’a nemika kai dasu a rasa rasawa ta har abada dan haka maza mike tuni ajuwon ya mike tsaye jikinsa na rawa ya koma bakin kofa ya tsaya ya bar alhj tajudeeni zaune “ni kake yiwa kashedi ?
“Isa ce kuma dole kayi dan haka mike karka tsaya cika baki a zuwan kai wani jan wuya ne alhalin bashi bane kayi kokari kayi aiki da bayanaina kafin alhalinka su nemeka su rasa ya bud’e baki zai sake yin mgn ya katse shi ta hanyar cewa “karkace komai domin maganarka tana hassalani maza tashi ka bar nan yayi mgnr a matukar fusace yna nuna masa hanyar fita da dan yatsansa.”