KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Babu shakka izarka ce zatayi silar karshenka kai da alhalinka ya fada yana gyara zamansa,” kaci duniyarka da tsinke na wani lokaci yana gama fadar haka ya mike a hanzarce zai wuce har yayi taku uku yaji an tsarke masa kafafu da tsarka cak yaja ya tsaya qirjinsa na wani irin dokawa da matsanancin karfi shi kuwa ajuwon sauran kadan dariya ta subuce masa ganin yadda mai gidansa ya diririce sai dai yayi sauri ya danneta domin shi kansa ba tsira zaiyi ba idan wani abu ya samesa “kamar yadda ka kasance hatsabibi haka muma muka kasance sai dai mu hatsabibancinmu na kyautatawa alumma ne bana son rai ba ,kafin kayi silar karshensa ka fara ta kaina amman shi kam yafi karfinka domin kuwa yana da karfin da zai tarwatsaka duk kuma inda ka shiga acikin duniya sai ya tabbatar dana nemoka ya shekeka da hanunsa yana gama maganr ya saki sarkar ta zube kasa agigice alhj tajudeeni yabi sarkar da kallo cike da mamaki zuciyarsa na karkarwa .”
A hankali anas ya tako ya tsaya a gabansa da sauri yaja baya qirjinsa na dokawa da matsanancin karfin gaske “tsawon shekaru ina rike da bindiga ban taba sheke kowa ba idan baka bi rayuwarka a sannu ba zan fara ta kanka domin shine sakamakon ka. “ko kuma ni in ratayesa ba ya mutu adalcin da zan iya masa kenan yaji wata muryar daga bayansa agigice ya juya bayansa cikin mutun ukun dake zaune ne tsaye abayansa yana masa mazurai hannunsa rike da bindiga “idan kuma zaka iya ganin bayansa to kayi idan ba haka ba ka binne abinda ke ranka domin kuwa bazaka iya ja damu ba ka bar takamar banza ka tsaya matsayinka ko kuma ka tsaya anan na har abada inji cewar jabir “.

“babu amfanin iri irinku da ba’a amfana daku a kasarku sannan baku da adalci da kishin kasarku mutuwa ce tafi dacewa da kai domin kai kadai duniya ke son ganin mutuwarka dan haka ka kula da rayuwarka kamil ya karasa maganar yana daura masa bakin bindiga a daidai saitin qirjinsa inda kadan ya rage zuciyar alhji tajudeeni bata buga ba dan firgici.”
gbdy suka zagayesa suka sakashi a tsakiya jikinsa banda tsuma babu abinda yake wani gumi ya shiga tsatsafo masa a goshinsa da kan hancinsa “lallai yau ya dauko ruwan dafa kansa sannan ya hadu da gamonsa bai taba cin karo da rudani da firgici irin wannnan ba ,yau tazo masa da rikincin da bai taba tsintar kanshi aciki ba, iya girmansa daya samu karfin iko bai taba cin karo da tsagiran tantira irinsu ba sai yau .

“Ina karfin ikon naka yake? “ashe baka da ikon komai da karfi ka sanyo kafafunka cikin gidana? kamar yadda kake ganin kana da kwakwaluwa da baseera kashe wanda baka so,ko halaka wanda baka so ,ko batar da wanda baka son gani kasani tamu ta zarta naka ,idan kuma ka tsaya akan cewar karfin ikon da kake dashi zai kareka akoina to kayi babban kuskure domin zaka kasance mai yawon shiga rudani kuma babu abinda karfin ikon naka zai maka kamar yadda kake gani a yanzu saboda an fika da kaifin baseera .”
“Idan kuma da zuciyarka kawai ka dogara kasani nasararka ragaggiya ce saboda ita zuciya abinda yayi mata dadi kawai take aiyanawa a yanzu ma zan iya kasheka waye zai sani ? jaguwa ya tambayesa yana goge bakin bindigarsa tare da yi masa kallon kaskanci alhj tajudeeni yayi shiru jikinsa na wani irin karkarwa “Kasani mutane ire irenku basa amfanar da kansu da komai agaban irinmu idan kaje ka tambayi amininka zai maka qarin bayani akaina yanzu yanzu ka kama hanya ka fice min da gani ban san ganinka jeka…” ya fada tare da juyawa ya nufi ciki gbdy duk suka dare suka barshi tsaye cike da tsananin tashin hankali ya juya ya soma tafiya da kyar zuciyarsa na tafarfasa “. da sauri ajuwon ya biyo bayansa har suka kai bakin get ,bai tsaya jiran a bude masa murfin kofa ba ya bude ya shiga ya zauna yana huci .”

kwalkwaluwarsa ta toshe kansa ya cunkushe ya dinga zurfafa tunaninsa duk abinda suka fada babu wanda yafi tsaya masa a zuciya kamar ta mutumin da yaji ajuwon yace shine anas dashi kanshi jaguwa maganganunsu sunfi cakar masa zuciya da kwakwaluwa, ya rufe idanunshi ya jingina bayansa yana jujuya maganganunsu yana yin filla filla dasu yana neman wa kansa abinda zai musu ya halakasu “sam sam bazan barsu ba ,bazasu sha a banza ba ,sai na gina musu wani rami da zasu afka aciki amman bazan barsu ba har sai naga bayansu daya bayan daya har ya karasa office da wannan tunani ya karasa zuciyarsa kamar zata buga“.
Bayan tafiyar alhji tajudeeni jaguwa ya sauya kaya ya zauna ya janyo pillow ya rungume a qirjinsa yana nazarin maganar alhj tajudeeni yana son yatantance tabbacin abinda zai iya yi acikin maganganunsa wani bangaren na zuciyarsa yaji ya yarda alhji tajudeeni zai iya yin wani abu domin yaga bayansu yayinda wani zuciyar ke karfafa masa gwiwar cewar babu abinda zai yi nan take yayi accept da maganar kyakkyawar zuciyarsa babu
abinda zai yi .”
A natse anas ya turo kofar dakinsa ya shigo bai san ya shigo sai da ya dafashi sannan ya waigo yana sauke numfashi “karka takura kanka da tunani fa bazai iya komai ba zuciyarsa zataita tunanin abinda zai yi mana amman bazai iya komai ba ,wannnan gaskiy ne bazai iya ba amman duk da haka zamu sa hankalinmu akanshi shiyasa kullum da kake cewa mu ajiye makamammu nake cewa da kai aa nasan gaskiya kake fada min amman a yanzu bazan yarda da ita ba “ ya kamata ka yarda mu bari zan yi iyakar kokarina mu canza gbdynmu kuma inshaallahu zanyi nasara “ka kasa fahimtata ne anas barin wannan aiki yana da matukar hatsari sai muyi matukar shiri wanda bazai ruguje mana ba sannan ma idan zamu bari ya karasa mgnr yana cewa “ ya kake jin kan naka yanzu? ya fad’a ta hnayar katse maganar gbdy “har cikin kwayar idanuna nake ji ciwon kan amman maganr wancan banzar mutumin tasa na nemi ciwon kan na rasa jaguwa yayi murmushin gefen baki yana kokarin bude baki yaji ana knowking din kofa yasan cikin yaransa ne ya bada umarnin shigowa eku ya shigo rike da wayoyinsa daya na ringing aciki .
ya mika masa wacce take ringing din ya amsa yana dubawa number ya gani babu suna yana yawo akan screen din wayar shi kuma eku ya juya ya fice daga dakin ya dafe kanshi batare daya daga wayar ba anas ya matso kusa dashi “ka daga mana ko kiran ba mai mahimanci bane ? “number babu suna ! ya fad’a yana lumshe ido knowking suka sake ji anas yace “waye ?
“Nice !
Da saurin ya bude idanunshi sakamakon jin sautin muryarta ya kalli anas shima din kallonsa yake “na fad’a mata karta sake zuwa gidan nan me kuma ya kawota ?“Oho ai ka hadu da gamonka dan wannan yarinyar wallahi bazata koro ba kamar sauran matan daka saba kora ,ta zame maka karfen kafa mutu ka raba ya fad’a yana masa dariya kafin yayi wani hanzari har ta murda handle din kofar ta shigo ta tsaya tana dubansa da lulu eye’s dinta sanye take cikin doguwar rigar abaya yellow wanda akayiwa ado da flower ‘s baki haka yar cikinta baki ne ,hand bag da takalmi har ma da agogon dake daure a tsintsiyar hannunta baki ne tayi kyau matuka gbdy kamshin turarenta ya hade danashi ya gauraye dakin kamar ya tashi ya sureta yayi bedroom dinsa daita.”

kallonsa ta cigaba da yi wanda ya rigada ya saba da irin wannan kallon nata in dai tana tare dashi tô fa dukkanin idanunta na kanshi ya fahimci kallonsa ba qaramin jefata cikin nishadi yake ba .
bai damu da yadda ta tsare shi da idanunta ba saboda hasalima jin dadin hakan yake dan yana sa shi jin farinciki ,yanzu ma hakan ce ta kasance domin kuwa ya nemi dukkanin damuwarsa ya rasa .”
Anas ya kallesa ya girgiza kai yana dubansa dan yasan babu macen data isa ya tsaya yana kallonta haka sai ita data cire tuta .”
ya mike tsam zai fita daga dakin sai lokacin tanwer ta dauke idanunta akan jaguwa ta maida kanshi “anas ina yini ?
“Lafiya lau tanwer ya kwana biyu ?
“Lafiya gsky mun jima bamu ga juna ba tun a asibiti fa gashi har na warke “ ,alhamdulillah mun godewa allah dan da wani abu ya sameki ban san yadda wannan abokin nawa zai yi react ba ina ganin ma zare mana zai yi yayi maganr cikin zolaya yana murmushi yana kallon jaguwa murmushi tayi “ai sai yana sona ne zai zare muku inda wani abu ya faru dani “kinga ni nayi waje bazaa yi tone tone dani ba ya sa kai ya fice daga dakin ya rufo musu kofa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button