KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ta karasa ta zauna gefensa tana riko hannunsa cikin nata ta fara massaging a hankali ya kalleta a sukwane sunyi mugun daf da juna dan tana kara motsa jikinta sai dai tayi masauki ajikinsa.”
ya zare hannunsa cikin nata ya mike daga kusa daita yana cewa “me ya kawoki?.”ya furta cikin wani irin salo dake kashe mata garkuwa jiki sannan ya karasa inda karamin fridge dinsa yake ya bude ya dauki goran ruwan roba mai sanyi yana kokarin juyowa sukayi karo daita tayi baya zata fadi bai san sanda yayi wurgi da goran hannunsa yayi kokarin tarota zuwa jikinsa amman ina tuni har hannunta ya tokare kasa zuciyarta na rawa ta saki qara mara sauti ya zagaye kugunta da hannunsa daya ya mikar daita tsaye ta makalesa tsam ajikinta tana sauke numfashi . “ki dinga bi a hankali kada kijiwa kanki ciwo kijawa mumy da dady hasara ya fada hucin numfashinsa ya sauka a wuyanta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa kuma bugawar da zuciyarta keyi ya qaru zuciyarta ta sake nitso a shaukin soyayyarsa “muga hannun ,allah yasa bakiji ciwo ba ?taji ya fada bata ankara ba taji ya kamo hannun ya sanya cikin nashi ya soma murzawa a hankali .”
duk wata kafa dake dauke da gashi ajikinta sai da suka mike muryarta cike shaukinsa tace banji ciwo ba fa”. kamar wanda ta farka a mafarki yaji sautin muryarta dan bai ma san susucewar da yayi akanta ba .”nan take ya dawo haiyacinsa ya zareta ajikinsa yana tsotsa keya sannan ya dauki goran ruwan daya yi wurgi dashi ya bude ya kafa a bakinsa shiru tayi tana dubansa har ya sha mai isarsa ya ajiye sauran yana cewa “ya kamata kiyi abinda ya kawoki ki wuce “shiru tayi tana dubansa yanayinta da alamun basu ji dadin furucinsa ba kusan minti shabiyar suna tsaye babu wanda ya cewa dan’ uwansa uffan jaguwa yayi jarumtar magana “Ina da babban lokaci zan iya wucewa ? ya fada tare da juyawa ya fara daga kafafunsa naunayen ajiyar zuciyata sauke da karfi .“ina da magana ta karshe da nake son nayi da kai shine ma dalilin zuwana “menene ? .”
yayi mgnr hade da juyowa ya fuskanceta qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi tayi taku biyu ta dawo gabansa suna fuskantar juna har suna iya jiyo bugun zuciyar juna “nasan wani abu tattare da kai wanda babu wanda ya sani “menene shi ?.”
Ya gyara tsayuwarsa ya rungume hannuwansa duka a faffadan qirjinsa yana kallon kwayar idanunta .
“Wannan fuskar taka da bata daukar raini itace hoton da kowani jami’in tsaro yake nema amatsayin azzalumin dan fashi wanda bashi da tausayi amman ta ciki sam ba haka kake ba kai din me tsananin tausayi ne da kirki tattare da nuna kulawa da…….”“Tanwer….”!
“Dakata na fahimci haka ne a yanzu da kuma ranar da mota ta bugeni ka taimaka min an sani mota ka rike kaina da hannunwanka duka cike da tausayawa kana kokarin tare jinin dake zu…”
“Tanwer bake ba ko dawa hakan ta faru haka zanyi .”nan take yanayinta ya sauya idanunta suka ciko da ruwan hawaye “amman me yasa sauran mutane banga hawaye a idanunsu ba sai kai ?
Shiru yayi tare da kawar da kanshi yana kallon wani gefe “na shiga wani hali alokacin danaga wannan abu a hankali ahankali sai na daina ganin komai amman na tabbatar alokacin ban mutu ba zuciyata tana cike da Kwarin gwiwa bud’e idanuna domin kawai ta ganka.”ta karashe mgnr ta juyo da fuskarsa gareta tai shiru tana kallonsa cike da tsananin qaunarsa mara misaltuwa ,shi din ma ita yake kallo cike da tausayawa da soyayyarta .“adnan !” ta kira sunansa bai amsa ba ya ware idanunshi sosai akanta tasan tunda yayi haka ba amsawa zaiyi ba dan haka ta cigaba da maganarta “har yanzu zuciyata ta kasa hakura da kai ina sonka adnan.”Kallonta ya cigaba da yi yana jin yadda soyayyarta ke nukurkusan jikinsa tana bin jijiyon da duk wani abu dake aiki ajikinsa“.

Ya numfasa kana ya motsa lip’s dinsa “ya kamata ki fahimci wani abu nayi tsanmanin kin fahimci maganata a ranar da muka hadu da dad dinki a hospital na fada miki ke yanzu matsayin kanwa ce agareni ki daukieni matsayin yayanki ,ban taba furta miki ina sonki ba koda sau daya ne , nayi tunanin mu abokai ne a yanzu me yasa sai muyita dogon bayani akan halakarmu ?”
“Kada ki dauka duk abinda nake miki a matsayin soyayya ne tausayawa ne kawai wani mugun kallo tayi masa a karshe kuma tayi murmushin yake wanda yafi kuka ciwo “sau nawa kake son nayi maka baraza da hawayen idanuna adnan ?”.
“So kake a yayinda ruwan sama ya sauka ka ganni aciki yana dukana ina rokonka ina kuka akanka sannan zaka fahimci abinda nake son kamin na taba ce maka muyi abota?”.Ko na taba rike hannunka a matsayin muyi abota ?”.
“Duk abinda na aikata nayi ne bisa ina sonka a karo na sau babu adadi na mallaka maka kaina kayi yadda kake so dani ba dan komai ba sai dan son da nake maka , “wallahi abinda nake ji akanka na gaske ne ,” kallonta ya cigaba da yi gabansa na faduwa da matsanancin karfin gaske .
“Ban taba tmbayarka abinda kake ji akaina ba ,ban taba tambayar ka kana sona ba ko baka sona ba ni dai abinda nasani shine ina sonka kuma zan cigaba da sonka har karshen numfashinsa .”Ta karasa maganr tana danne kukanta “adnan ahmed nasan bazan samu amsa abinda nake son jin daga bakinka ba ni zan wuce ta juya ta soma tafiya har tayi taku biyu ya riko tafin hannunt ckin nashi yana murzawa a hankali ,”

bata juyo ba adalin hawayenta dake zuba “
Jinin jikinsa ke gudu fiyye da kaida shi kansa yasan baya kyauta mata amman shi yana da dalilinsa domin kuwa duk runtsi yasan iyayenta bazasu yarda su bashi ita ba shiyasa ma yake son maida soyayyar da suke wa juna zuwa abota ko hakan zai sa zuciyarsu ta samu sausauci “Ka sakar min hannu ta fada muryarta a raunane “ki kwace idan kina da karfi yasa dayan hannunsa yana shafa hannunta cikin karfin hali ta fixge hannunta daga rikon da yayi mata kuka ya kwace mata sosai ta durkusa kasa tana rera kuka cikin matsanancin bakinciki yanzu yayi mata adalci Kenan daya dauke soyayyarta a matsayin abota? jin ya ‘bata yasa ta mike da sauri ta soma tafiya da niyyar barin dakin amman ina cikin zafin mana caraf ya kamo faffadan kugunta daya wadatu da mazaunai wanda suka dan bayyana saboda rigar dake jikinta tabi jikinta ta kwanta sosai taku ta kara cike da jin haushi ta sake rage tazarar dake tsakaninsu ya lumshe rikitattun idanunshi ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam cikin shaukin qaunarta .”

a hankali ya kai bakinta daidai saitin kunneta yana hura mata iskan bakinsa my sweetheart my life ina matukar ji dake tanwer idan ban mallakeki ba dole na kare rayuwata a wahalacce“. ya fada acikin zuciyarsa yana sakar mata numfashinsa wanda ya sake haddasawa tsigar jikinta mikewa jin tana shiga wani yanayi yasa ta fara kicin kicin kwacewa amman ina ta kasa dan bakaramin runguma yayi mata ba har mayafin abayar data nade kanta dashi ya zame “tanwer!
Ya kira sunanta bata amsa ba dan gbdy ta kasa kwakkwaran motsi “please ki daina kukan nan but kema sau nawa zan fada miki soyayya har ta kai mu ga aure ba abu ne mai sauki ba ?ya fada yana shafa sumar kanta zuwa gadon bayanta bazan iya abinda kike so ba ,banason a dalilina wani abu ya sameki adduata da fatana ki samu miji wanda yafi adnan ki aura dan har abada bazan iya fuskatar mahaifinki da batun ya aura min ke ba .” yana magana yana shafa duk inda yaci karo dashi a sansar jikinta “ki bar rayuwar adnan please kiyi rayuwarki da wani babu shi ”
“Bazan iya ba allah ne ya jarabeni da sonka ina maka son da idan babu kai acikin rayuwata zan kare ne cikin garari da tashin hankali .”murmushin gefe baki yayi “na gode da hallacin soyayyar da kika min , na gode sosai kuma nasan qaunace tasa kika dinga mallaka min kanki ,na gode na gode ya kamata kiyi haramar tafiya nima fita zanyi ya riko hannunta suka fara tafiya taja ta tsaya ya juyo yana tsareta da rikitattun idanunshi ta fixge hannunta ta saka masa kuka ya kalleta fuskarsa da alamun tambaya “babu inda zani muddin baka fada min cewar zaka aureni ba “. yanayinta ya fahimtar dashi har cikin zuciyarta abinda take nufi gsky ne ransa yayi mugun baci ganin ta kasa fahimtarsa “bar nan yanzu ya fad’a yana cizan lip’s dinsa “am not going anywhere ina nan har sai nasan matsayina acikin zuciyarka “me yasa kike da taurin kai ? ya tmbyeta yana furzar da iska mai zafi “babu wani taurin kai gskiya da ka boye a zuciyarka nake son sani zaka aure ni yes or no simpl “to bazan aureki ba dan haka karki sake zuwa inda nake”. yana gama fadar hk yaja hannunta suka fito daga dakin zuwa falo ya iske anas zaune yana jiransa “muje ko !”. yayi gaba rike tsintsiyar hannunta bai tsaya koina daita ba sai a inda tayi parking din motarta yana tsaye ta shiga har motarta ta fice daga haraban gidan yana tsaye yana kallonta ya lumshe idanunsa lokaci daya kuma ya budesu “oh my goodness god ya furta a can kasa ransa ta yadda idan ba bakinsa ka kalla ba zaka fahimci abinda yace ba murmushi ya dan subuce masa “kai tanwer ba dai rigima da taurin kai ba dan ma allah yasa ta same sa tsayayyaye da karfa karfa zatai masa ta mallakesa ta karfin tsiya ,sam ya manta da yace anas ya biyosa sai da yaji yana cewa “majnun ina zamu ka tasoni?
Bai ce uffan ba ya nufi gurin motar anas suka shiga suka bar gidan kai tsaye hanyar da zata kaisu gidan malam mudi yace su nufa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button