KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

tanwer kuwa gida ta nufa ranta a dagule ji take kamar ta kashe kanta ta huta saboda muguwar tsanar da jaguwa yayi mata abinda batasani ba shi kansa yana mutuwar sonta fiyye da soyayyarta da take masa shi dakiya ya fita da kuma ganin tunda ba samun aurenta zaiyi ba meye amfanin batawa kansa lokaci da zai yi.”
A falonsu ta zube tana kuka tana cika tana batsewa mumy ta fito daga kitchen tana dubanta sai data gama nazarinta sannan tace”lafiya Tanwer? hawaye tanwer ta goge tace “gaskiya mumy na gaji da wannan rayuwar dame zanji mumy adnan yaki amincewa da soyayya duk akan tsoron abinda zai faru ,dukkanin alamamomi sun nuna min yana son auren amman yana gudun ya afka soyayyata kuki amincewa da aurenmu me yasa mumy ?“Sau daya kawai mumy ku bani abinda nake so nayi muku alkwarin da yarda allah zan canza adnan wallahi zan kashe kaina kowa ya huta idan baku amince ba ta karashe mgnr tana kuka .”

Numfashi mumy ta sauke cikin rarrashi tace “haba mamana ki daina furta wannan kalmar karki manta duk mutumin daya kashe kansa ya mutu kafuri dan haka kar na sake jin kin furta zaki kashe kanki ke kadai fa garemu shi fa wata killa suna dayawa agurin iyayensa ita soyayya tana bukatar juria da hakuri tare da dakiyar zuciya ,adnan duk ya fiki ita shiyasa yake walahar dake ,kema ki gwada hakan zaki ga yadda komai zai sauya miki .”
Ajiyar zuciya tanwer ta sauke tace”haka ne mumy nasan yana da dakiya sosai amman ni nayi kokarin nayi hakan na kasa Kiyi min addua mumy ko zan samu sausauci mumy ta zauna gefenta ta dinga tausarta tana bata baki amman tanwer taki sakin ranta ta mike ta shige dakinta ta zube akan gado ta rushe da wani kuka mai ban tausayi “.


Tafiya su jaguwa suke acikin mota suna maganar tanwer “damuwar tanwer ta fara damuna anas na gaji da kuncin da take ciki duk akaina ta hana kanta kwanciyar hanakli nima ta hanani kullum tana cikin damuwa bata walwala wallahi tana mugun bani tausayi duk wani burinta akaina ne amman na gaza samar mata farinciki da kawar da damuwarta “.ya dai kamata ka rungume qaddarar rayuwarka adnan,kayi tuanani mai kyau tana sonka kuma da gskya domin kuwa zata iya sadaukar da rayuwarta a irin son da take maka da wannan hirar suka isa gidan mlm mudi inda suka iske malam mudi tare da matarsa zaune a falo sukai sallama sannnan suka karasa shiga cikin babban falon .
mlm mudi suka hada baki da matarsa suka amsa sallamarsu jaguwa cike da sakin fuska .”
A tare jaguwa da anas suka zauna akan kujera suna gaishe da malam mudi da matarsa mama usaina, suka amsa “anas ya amarya fatan tana lafiya?“Tana lafiya mama tana gaishe ki idan an kwana biyu zan kawo miki ita inshaallahu tayi miki yini ,ai kuwa da ka kyauta ta mike sanye cikin doguwar riga ta shiga kitchen ta bude fridge ta dauko drinks mai sanyi da cup guda uku ta dawo ta ajiye akan center table ta tsiyaya drinks ako wani cup ta fara mikawa anas “mai mata zan fara bawa tayi mgnr cike da zolaya sannan ta mikawa jaguwa anas yayi murmushi “ai dai kagani ko aure akoina daraja garesa ka kokarta kayi ko ka samu wannan darajar jaguwa ya watsa masa harara “dan malam ka rufewa mutane baki kai ma yaushe ka tashi a matsayina?”koma dai menene dai na fika tunda nayi ko ba haka ba ?mama usaina tai murmushi irin nasu na manya ta karasa gaban mlm mudi ta mika masa nasa drinks tana cewa “gsky haka ne kai ma dai adnan ya dace ka ajiye iyali haka”.

shiru yayi bai ce mata komai ba haka zalika bai kai cup din bakinsa ba tunanin maganar daya fadawa tanwer ta shiga dawo masa “bazan aureki ba dan haka karki sake zuwa inda nake “mama usaina ta matso kusa dashi ta tsaya ina ma zai amince data bashi auren diyarta fatima “ai yaki ne akwai diyar minister of health dake mutuwar sonshi ai kamar kwanaki na fada miki to har yanzu yaki bata hadin kai sai yawo yake da hankalinta ita kuma kamar mayya taki hakura dashi yanzu kafin mu baro gida sai data zo amman wallahi da kuka suka rabu .”
“Ba laifinta bane anas ,shi haka so yake idan kana son abu baka iya hakura dashi sai idan wahala kagani kasan ance wahala kadai ke isar mai rai ,wasu fa duk wahalar da zasu a sha soyayya basa iya hakura sai idan namiji ne yayi musu jan ido ya fito a mutun sak ya fada musu baya sonsu sannan su hakura .
“Mama ai ni na furta mata bazan aurenta ba to me yasa taki rabuwa dani ?yyi mgnr Kmr zaiyi kuka ta zauna kusa dashi “kai me yasa bazaka aureta ba ?karka manta matsayinta zai iya taimaka maka .
“Bani da kwarin gwiwa ne mama , bazan iya auren diyar kowa ba da irin rayuwar da muke ,kai yanzu ka gwamaci ka auri aikinka?
“Amman mama gabadaya soyayya bata lokaci ne saboda ni ina jin haka ajikina ,gaskiya gbdy kai matsoraci ne tsoro kake ji kana jin tsoron wani ya shigo rayuwarka domin ka rayu tare dashi wannan tsoro ne ka fahimta ba jarumta bane .”
Shiru yayi yana tunani tun daga ranar da suka hadu da tanwer har zuwa ranar daya satota har zuwa moment din da sukayi spent “ka furta abinda yake ranka idan kuma kasan baka sonta kana iya mata abinda zai sa ta rabu da kai amman idan har kana sonta sosai to ka hanzarta furta mata tun kafin ta gayyaceka daurin aurenta .” tana gama fadar haka ta mike ta juya ta shige ciki ta barsu domin su gana da mijinta murmushi mlm mudi yayi yace “yana da kyau ka dauki shawarta masu irin wannan alqallar suna ajiye iyali koda ta baci ba fata muke ba babu ruwan iyalinka aciki daga wannan maganar suka shiga wata inda jaguwa ya zayyanowa mlm mudi abinda ya faru a wannin da suka gabata a tsakaninsa da alhj tajudeeni yanzu me ya kamata muyi ?”.
“Zamu fara aiki cikin satin nan duk wasu masu alqallar muyagun kwayoyi zamu farmakesu mu kwace sannan mu dankasu ga hukuma inji cewar anas “aikin kam zamu fara amman damkasu hannun hukuma bai taso ba dan duk bakinsu daya ne tunda akwai kudi daake cire musu duk karshen wata ,za dai mu kamasu mu hukuntasu mu dauki vedio mu bawa yanjarida sannan mu yada.”
“Haka ma yayi daidai amman ya zaayi a karbi killo arbain din da zai shigo hannun alhji tajudeeni ?zan dana masa tarko ,zan tura masa wasu ta karkashin kasa suje suyi aikin yanzu da idanunshi suke a rufe bazai kawo komai aransa ba zai nuna isarsa tunda nace babu wanda zai yi sai kaga yana samun wadan zasuyi da gudu zai yi amanna shima da zarar tarkona ya kamashi zamu yadasa a duniya,duniya tasan ko su waye ,idan duniya ta sani alumma zatai caaaa akan maganar anan kuma karfi da ikon fada aji bazai yi musu amfani ba Kaga dole gwanati ta shiga ciki lamarin tasa a gurfanar dasu a gaban kotu “gsky kai din mai basera ne sun dan jima suna tauraunawa anan sukayi magrib wanda a daidai wannan lokacin
tanwer na can tayi kuka kamar ranta zai fita har idanunta sun kumbura ganin lokacin sallah na wucewa ta tashi ta shiga bayinta tayi alwalar tay sallar magrib domin an idar da sallah a massalaci cikin unguwarsu bata jima ba aka tada ishai tare da matsalacin unguwar sukai , ta jero addua ta shafa ta koma ta kwanta lamo tana tunanin rayuwarta ko ta abinci batayi ba hankalinta sosai atashe yake .
Sai da su jaguwa sukai sallahr ishai aka kawo musu abinci mai rai da lafiya anas bai ci ba dan yasan madam dinsa ta girma masa lafiyayyen abinci jaguwa ne kawai yaci byn jaguwa ya gama ci suka masu sallama suka wuce .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button