KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Da misalin karfe takwas na dare hally na zaune a falo su jaguwa suka shigo tun daga baradan da zata kawosu cikin ainihin falon gidan take jiyo hirarsu har da yar dariya amman suna shigowa duk sukayi shiru sai sallama da suka hada baki sukayi ta amsa cikin kulawa sannan ta tsugunna ta gaishe da jaguwa ya amsa cikin kulawa “sannu auta ya kuma kikaji da zaman kadaici.?”
Ta saki ranta tana mugun qaunar yayanta sosai jikinta ne ya bata Ana’s ita yake kallo dan hk ta sunkuyar da kanta murmushi yayi yace “kinata jiran dawowata ko?”Ya fada cikin zolayarahi ta fahimcesa daren da yayi yake son kare kanshi duk kuma da yasan babu wani mataki da zata dauka tace “tunda dai kana lafiya ai shikenan ya zauna kusa daita yana murmushi “na raka yayanki ne wata yar unguwa har zai wuce gida nace yazo yayi miki bayani domin ban taba yi dare kamar haka ba nasan hakan kuma bazai miki dádi ba shiyasa nace lallai yazo ya zamar min sheida .”
Ta kawar da kanta Ana’s kenan ai ko zan fara daukr zafi akan haka ba yanzu ba a fili kuwa murmushi tayi tace “kada ka damu nasan bazakayi dare dan son ranka ba “.Jaguwa ya ji dadin yadda tayi yace “tô ni bari na wuce gida sai ka fito gobe kenan?”
Ana’s ya dan zamo daga kan kujerar da yake zaune ya fuskanceta sosai “tô shikenan sai gobe amman karka manta da shawarar mama usaina ya fice yana cewa “Au bama rakiya lallai anas ?bai bashi amsa ba ganin ya rigada ya fice ya dan juyo sosai ya dube hally dake kan kujera daya da suke zaune kuma ta zaman mutun daya suna manne da juna kallon da yake mata duk da kanta a kasa yake tana jin fitar numfashinsa gbdy ta kasa sakewa tana murza yatsun hannunta ya kamo hannuwanta ya saka acikin nashi a hankali ya furta “halima da gaske kuwa kina min irin son da nake miki ?”.
Tayi shiru tana juya maganar “ina miki so fiyye da wanda yayanki yake miki “ya zai hada son da yake mata da wanda danuwanta yake mata da suka fito ciki daya idan kuwa har haka ne to bakaramin soyayya yake mata ba ta kuma san tunda ya fadi haka shine hakikanin gaskiyars mussaman ta fahimci abinda ya fad’a din shine acikin ranshi ,
ta dubeshi tana son ya sakar mata hannunta da yake faman aikin murzawa domin murzasu da yake yana sakar mata wani irin kasala da shock acikin jikinta ta dan kawar da hannunta dan tsaidashi ya dago habarta ya kalli cikin kwayar idanunta “ina sauraronki kina sona Ko bakya sona ?“Ina maka so daidai da irin wanda nakewa yayana “tana yin shiru a ya sakar mata hannu ya tashi daga inda yake ya nufi dining table bai mata umarnin suci abinci tare ba kamar yadda suke akwakin da sukayi tare”.
ya hau cin abinsa shi kadai zuciyarsa na masa zafi hakan kuma bai dago ya kalleta ba gbdy sai kuma taji rashin dadi acikin zuciyarta bata san me yake son tayi masa ba wanda zai faranta masa ranshi ba ,babu abinda yafi daga mishi hankali kamr yaddda bata bashi amsar tambayr farko da yayi mata ba , ai ita a tunaninta ko bata bashi amsa ba zuwa yanzu ya kamata ya fahimci tana son shi ta tashi ta isa garesa “Lafiya ko kace dani muci abincin tare ko nayi laifi ne?”.
Ya dan gyara zamansa “bismillah zauna mana ,ai gani nayi na kai wani lokaci banyi tsamanin bakici ba yanayin da yayi mgnr acikin ranta tasan akwai wani abu aranshi ta zauna tasa spoon ta fara yafitar abincin domin daman ba wani damunta abincin yayi ba tana ci tana kallonsa kamar yadda yasaba dauko magana ko satar kallonta sam yau bai yi ba abincinsa kawai yake ci ta dan ji babu dadi tace “wai duk akan ban baka amsar irin son da nake maka bane shine kake fushi dani?
Bai dago ya kalleta ba ya cigaba da cin abincin da yake “kayi hakuri amman kasan dai zuwa yanzu ina jin wani abu akanka koda kuwa ban furta maka ba ” ya mike tsaye “na shiga ciki ya kamata ki samu kici abinci sosai sannan kije ki kwanta ta bishi da kallo har ya shige cikin daki ta kasa cin abinci sosai tunani take to wai ya zata mishi ? ta yaya zan faranta masa ta tashi itama ta hada kan kayan abincin ta shiga dakin daya shiga yana kwance akan gado yaja bargo amman idanunshi biyu ganinta yasa ya rufe idanunshi bathroom ta shiga ta wanke hannu tare da yin abinda ya kamata sannan ta dawo dakin ta kashe fitila ta haye gadon ta kwanta taja nata bargon taji bai lalubota kamar kullum daya saba janyota ya manta ajikinsa ya rufeta da faffadan qirjinsa ba sai ma sautin muryarsa taji “ina tsamanin bai kamata mu kwana guri daya ba tunda matsayina guda dana yayanki.”?Tayi shiru har yaje karshe maganarsa bata kulashi ba tayi kamr bata ji abinda ya fad’aba.
bai kuma maimata wa ba shima sai yanzu ta gane manufarshi tayi murmushi kawai tayi addua bacci ya dauketa da asuba ma kowa ta kanshi yayi babu wanda ya tashi wani bai tasheba kamar yadda ya saba sai dai bai jima da tashi ba ta farka .”
Tun safe da tanwer ta tashi tayi sallah bata fito ba tana kwance a dakinta wani irin faduwa gaba ke shigarta a duk sanda zuciyarta ta hasko mata fuskar masoyinta , jikinta sai rawa yake a haka ta wuni har dare mumy ta shigo dakin yafi sau biyar tana rarrashinta dan ita yanzu tausayi take bata babu yadda batayi daita akan ta fito ko abinci taci amman taki sai kuka take haka mumy ta hakura ta fito ta koma dakinta tayi tagumi cike da zullumi da tunanin madafar dafawa ita .”
zuciyarta tanwer ta dinga raya mata ta tashi taje ta samu dad dinta da kanta domin ta fad’a masa matsalolin da zata shiga idan yaki amincewa da aurenta da adnan ,dad dinki zai iya yarda idan kika fada masa da kanki ,wata zuciyar tace bazai biyewa son zuciyarki ya daukeki ya bawa dan fashi ba kawai dan son cika miki burin ki , yayinda wata zuciyar ta karfafa mata gwiwar zai amince tsam ta mike ta fice daga dakinta falon yayi shiru babu karar komai sai na na’urar A.C dake aiki sai kuma kukan tsuntsayen da suke shawagi a sararin lambun dake kusa da falon.
Turus tayi ganin dad dinta zaune akan kujera shi kadai ya zuba mata idanu ya daga kai ya kalli agogo karfe goma na dare da mintuna sun wuce ya mayar da kallonsa gareta “mamana zo ki zauna ya fad’a yana mata murmushi , a hankali tanwer ta isa ta zube kasa daf da kafafunsa ta sunkuyar da kanta kasa tana tsiyayayr da hawaye “banga alamun kin ci abinci ba?”
“Bana jin zan iya cin abinci dady radadin dake cikin zuciyata magance shi shine abincina da ruwan shana , muddin ina cikin halin da nake ciki yanzu dady bana tunanin zan dangwama rayuwa kamar kowa kuma cikin koshin lafiya bana ma tsammanin zan shige wasu wa’adi batare dana koma ga ubangijina ba dady ka taimakeni..”
Tai shiru kuka ya kwace mata “Tanwer har kullum ina tunatar dake matsayinki sannnan da halin balain da zaki shiga idan kika bari aure ya shiga tsakaninki da wannnan yaron ,aurenki dashi nakasu ne a rayuwarki, zai gurgunta miki rayuwa da mummunar qaddara, kullum kuma kina cikin tashin hankali da faduwar gaba , ina son kiyi duba da makomarsa shi fa ba kamar kowa bane sai dan fashi mai barna ,
ina hasko miki mummunar rayuwar da zakiyi idan kika aure shi karki manta ke fa kina da kyawawan halaiya yayinda shi bashi dashi ,ke mai ilimi ce shi kuma jahili ne aurensa shine zai kawo miki cikas a rayuwarki .”
“duk fa halin da yake ciki a yanzu nasani kema da duk halin da kike ciki ko zuwanki gidansa ma jiya da kikayi nasani ina jin zafi da radadin kasancewar ki dashi ban sabar miki da wahala ba amman kin jefa rayuwarki cikin mummunar rayuwa ,ban san ta fuskar da zan bullo miki ba bazan iya sabawa Kaina alkwarin dana yiwa kaina ba tanwer kiyi hakuri kawai ki bari idan Ibrahim ya dawo ki aure shi ,”
“wallahi shine yafi dacewa dake na tabbatar zai zame miki miji na gari ,zai baki kulawar fiyye da wanda kika taso ciki ,shi ba dan maye bane bare idan ya sha yazo ya dakeki, bazaki tagyaraba a hannunsa ba yana kan samun lafiya nan kusa zai dawo kuyi aure
ita gbdy ta manta da wani ibrahim a rayuwarta bama ta son ta tuna shi adnan kawai a gabanta “kayi hakuri dady ka aura ma adnan ni ka kuma mana fatan alkhairi arayuwarmu na zamo silar shiryarsa “Kiyi min biya tanwer ki daure ki samar da farinciki mai daurewa a tare dani .” ya ajiye maganar cikin wani irin yanayi ya tsura mata ido yana kallonta .