KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Dady duk wani biyayyarka bazan fasa ba tunda bani da wanda yafika amman matsawar ba adnan na aura ba karka yi tsamanin zan samu farincki agidan aurena domin kuwa aurena da Ib bazai kawo farinciki a rayuwata ba a bincikena na gano mahaifinsa shine yasa akawo maka farmaki har adnan ya samu damar tafiya dani .”
“nasani nasan shine “
“tunda kasani banga amafnin rike alkwari ba ya kamata bangon alkwarinku ya ruguje yadda adnan yake mai laifi haka mahaifin Ibarahim yake baka jin tsoro nayi zuria dashi su dauko halinsa wallahi babu farincikin da zanyi dady kowa ma fa mai laifi ne inda zaa yi kwakkwarar bincike hatta shima ibarahim din mai laifi ne tunada yana biye biyen matan banza amman saboda shi mai galihu ne ka gwamaci kabashi aurena sau nawa yana kokarin keta min haddi acikin gidan nan kodan ban taba fitowa na fad’a maku ba tana kaiwa nan ta tashi da sauri ta bar gurin ta shige dakinta tana matsanancin kuka dady yayi tsai da ransa yana bin maganganunta dake dake yayi shiru yabi kofar dakinta da kallo tabbas tana dan gskiya wai ma me yasa bazan hakura na barta ta auresa ba “saboda bai dace bane da rayuwarta ai gara rayuwar zina data dan fashi agurinsa zina tsakaninka da mahalincika ne shi fa daukar bindiga ya tara rudani dayawa “?
yayi shiru yana saka maganganu acikin ranshi tsananin tausayinta ya kamashi amman bazai taba biye mata ba .duk maganrsu acikin kunne mumy sukayi shi ta mike tsam ta fito ta wuce dady ta nufi dakin tanwer cikin sanyin jiki ta kalleta tanwer ta dago kanta ta kalleta shabe shabe da hawaye bisa kuncinta “ki kwantar da hankalinki mamana ki tashi kiyi adduar inada yakinin zaki samu sausauci
saboda ina ji ajikina zaki auri adnan fatana allah yasa aurensa ya zame miki alkhairi arayuwarki ta
karasa maganar tana kuka “kiyi hakuri mumy nasan saboda ni kike kuka ko ?” inshallahu zan canza, ta girgiza mata Kai tare da riko tafin hannunta cikin nata cike da tausaya mata .”

Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️36

……….Sai da sukayi kuka mai isarsu sannan mumy ta zare hannunta acikin na tanwer tana kokarin fita daga dakin tana goge hawaye tana tunanin yadda zata sake fuskantar mijinta da wannan matsalar , Tanwer tayi shiru zaune tana kallon bayan mumy cike da matsanancin tausayawa har mumy ta karasa ficewa daga dakin idanunta na kallon kofa yayinda
wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tare da wani azababben ciwo kai mai tsanani .”
saukowa tayi daga kan katifa jikinta a matukar sanyaye ta zauna akan kujera kushin guda daya dake dakin hawaye na cigaba da zubo mata ,har ga allah yadda take d’aga hankalin mahaifiyarta abun baya mata dadi amman ya ta iya da qaddarar soyayyar data caki zuciyarta ta hana gangar jikinta da ruhinta sukuni? “wai me yasa bazata hakura da adnan ba ta hutawa ranta tare da dawo da farinciki da kwanciyar hankalin iyayenta ?”wadan nan tambayoyin ta dingawa zuciyarta sai dai nan take zuciyarta ta shiga hasko mata moment dinsu dashi tana kwance ajikinsa shi kuma yana shafa laulausar sumar kanta ita kuma tasa hannunta ta sakalo wuyansa ta cusa hannunta cikin tauttausan sumar kanshi dake kwance a keyarsa tana tafiya da hannunta acikin sumarsa nan take ta fara jin wasu abubuwa suna mata yawo a sansar jiki suna zaga jinin jikinta yarrrrrrrr taji gbdy tsigar jikinta
sun mike taji ina bazata iya hakura da dashi ba arayuwata ,da zata iya da tayi ko dan kwanciyar hankalin iyayenta .”

Kai tsaye mumy hanyar dakin dady ta nufa dan lokacin ya tashi a parlour ya koma dakinsa cikin tsananin zullumi da damuwa mara iyaka ,har cikin uwar dakansa ta sameshi zaune abakin gadonsa yana nazarin rayuwa da maganganun tanwer ,ta samu guri ta zauna akan kujerar dake fuskancesa sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci ranta a bace yake idanunta sunyi jawur alamun kuka, muryarta na rawa ta soma magana “na sake dawo wa gareka a karo na sau babu adadi , na bika na baka hakuri na durkusa maka da gwiwowina na baka hakuri ,nayi kuka duk akan cikar burin tanwer kaki ka fahimceni har ta kai ga ta sameka da kanka amman still kaki “a gaskiya a halin da muke ciki yanzu yakamata kayi wani abu akai dan gara muyi hakuri mu aura mata yaron nan ko acikin satin nan ne tunda taji kuma taga zata iya rayuwa dashi a aura mata shi kawai a wuce gurin , ita shiriya fa ta allah ce ina ji ajikina zai gyaru ya zamo mutumin kirki “.
dauke idanunshi yayi akanka ya mayar wani gefe zuciyarsa na zafi da tafarfasa dan ya gaji da jin wadan nan zantukan daga bakinta ,ganin yayi shiru yaki cewa komai sai ma dauke kanshi da yayi ya tunzurata dan haka ta cigaba da magana a fusace “wallahi idan wani abu ya samu yarinyata bazan yarda ba dan ita kadai gareni kai kuwa ko yanzu ka bukaci sake haihuwa zakayi nifa?“.
Yayi tsaki yana kallonta “kar allah yasa ki yarda amman wallahi bazan yi abinda ke da ‘yarki kuke bukata dani ba ,domin shi fa wannan d’an fashin ba daina fashinsa zaiyi ba , da na bashi aurenta gara ta mutu na san mutuwa tayi na binneta da hannuna ,ke yanzu da kike cewa bazaki yarda ba wannan maganr data fito daga bakinki ba abun kunya bane agurinki ace surukinki dan fashi da makami ne ?
Tayi shiru tana zubar da hawayen bakinciki “ke kuwa uwar arziki ce zainba?wallahi ina dauting cewar kina da hankali bare aje batun hangen nesa.” a matukar firgice mumy ta dago idanunta tana kallonsa “yes ki kalleni da kyau bazan canza magnta ba,domin kuwa akwai ciwo a kwalkwaluwarki dan duk mai cikakken hankali bazai so hada zuria da wannan tsinannan yaron nan ba wanda tsakanina dashi allah ya isa ne “. yayi maganar yana tsaida idanunshi akanta sannan ya numfasa kana ya cigaba da magana cikin tsananin bacin rai“bazan dauki diyata na bawa dan fashi ba dan “kafin ya karasa maganar ta katse shi tare da mikewa tsaye cikin tsananin fushi tana girgiza kai “ban taba tsamanin haka daga gareka ba ,yanzu har na dawo wannan matsayin “? ni zaka kalla kace ni uwar arziki kuwa“? wallahi ka bani kunya abubakar banyi tunanin haka daga gareka ba wallahi nayi danasani aurenka a rayuwata yau nice mai ciwo a kwakwaluwata ?.”tayi masa tambayar tana zubar da ruwan hawaye .
Dady yayi shiru kawai yana kallonta domin shima bai tsammaci wannnan maganr daga bakinta ba akan just common criminal take data sanin aurensa ? to ma me yayi zafi akan gsky dan haka shima ransa ya qara baci sai dai bai ce daita komai ba dan yasan idan ya cigaba da magana babu mamaki a kokarinsa na ganin ta fahimcesa abun zai zamo rikici da zai kaisu ga jin zafin juna .”

“Idan ma baka bashi aurenta a matsayinsa na dan fashi ba ai ka bawa d’an wanda ya zamo shugaba agaresu?still shiru yayi yana kallonta da sauraronta “me ye bambamcinsu da Ibrahim ?akwai bamba ci sosai a tsakaninsu domin kuwa shi Ibrahim rayayye ne da’aka fitar daga cikin matacce dan shi ba gurbatacce bane ,shi din mutumin kirki ne kuma kema ki sani sai dai yanzu idanunki sun rufe akan cikar burin diyarki kiki fadar gsky ,idan Ibrahim ya zamo siriki agareki zakiyi Alfahari dashi da alfaharin hada zuria dashi ,shi fa wannan gurbataccen ? da wani ido zaki kalli kawaye da mutane gari dashi ?“Wannan tabo ne da har abada bazai gogu ba ,wallahi wannan abun kunya kike yi zainba ke da ya kamata mu hada karfi da karfi mu yake tanwer shine zaki goya mata baya dan kuga bayana to wallahi baku isa ba , kuma ba kece zakiyi da kinsanin aurena ba nine ya dace nayi danasani dana aureki kika zamo silar haifar min diyar da take kokarin kunnawa zuciyata wuta “. yana gama fadar haka ya fita fuuuuuuu ya bar mata dakin ..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button