KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Magana ya fada mata d’an haka ta maida kanta ga kallon kofa fuskarta ta sauya launi sai taji batayi masa tambayar abinda shima ya lura dashi kenan ya dai dan samata ido yana kallonta ganin ta juya tana kallonsa ya dauke idanu shi ya cigaba da yin shiru kamar mai bacci ta mike a hankali ta nufi kitchen dan rana ta fara shadaya da rabi tayi zuciyarta babu dadi duk abinda yayi mata bata bashi laifi ba kanta ta bawa domin kuwa ita ta masa laifi T unanin yadda zata shawo kanshi ta nuna mishi qaunar da yake muradi daga gareta itace halalinsa halaka malak dole yana da bukatarta, ita kanta zuwa yanzu tana da bukatarsa amman bata jin zata iya kai masa kanta bazata iya wannan rashin kunyar ba sai daga yanzu a shirye take duk lokacin dayazo zata faranta masa rai ta nuna masa itama tana kwadayinsa domin ta tabbatar hakan zai dawo masa da walwalarsa .”
da damuwarsa bata wuce nuna koinkuka da take masa ba har ta isa bakin barandar da zata kaita kitchen ta dan juyo ta dan saci kallon fuskarsa,
idanuwanshi tsaye kyam abayanta ita yake kallon ,suna hada ido ya kawar da kai cikin nuna rashin kallonta .
Ta tsaya tana kare masa kallo ta tuna maganarsa kuma ta gasgantashi laifinta kunya tabbas ba karya yayi ba dole akwai muradina a tattare dashi ya zama dole ta cire kunya da tsoro ta bashi hakinsa sai dai ita kunyar ba zata barta ta kai masa kanta ba koda kuwa rike hannunsa ne tayi murmushi ta fice ta shiga kitchen tana tunani rayuwarsu da suka gudanar , to abu ne duk an hada da yarinyata sai hakuri dan ita din duka shekarunta basu wuce sha bakwai ba dole daman a samu irin haka bugu da kari bata da waye wa irin na matan daya saba muamula dasu .
Tana tsaka da aiki taji alamun tsayuwar mutun ta juyo bayanta shi ta gani tsaye yana kallonta ta juya sosai ta kallesa sai taga ya shafa sumar kanshi tare da kiran sunanta “hally !
Ta amsa hade da bashi duka hankalinta tana tsamanin akwai abinda zai sanar mata ya tsura mata idanunshi yana kallonta “jikina yana bani kamar kina fushi dani ?
“Fushi kuma da kai da akai yi me zanyi fushi da kai ?ya dan tsotsa kai kawai ya juya tayi murmushi kafin yayi nisa tace “am mai kake son a girka maka ?bai juyo ba yace “komai ma .”
Ta dan yi turus amsar shi bata mata dadi ba dan tun da ta soma girki abinda yake so take girka masa ta share ta cigaba da aiki ta taliya ta zaba ta girka domin ta fahimci yafi sonta ta hada komai sannan ta fita dan bata d’an lokaci baya falon amman da zamanta bai fi minti uku ba sai gashi ya fito daga dakinsa tana son ta faranta masa rai amamn ta rasa ta ina zata fara da me ma zata fara wani abu yazo mata rai dan haka tayi hanzarin daidaita natsuwarta “tun dana tare ko sai daya banga an gyara dakinka ba ko baka bukatar a gyara maka ne ?
Ya dan dubi kofar dakin ya kawar da kai yace “shi dakin ne baya bukatar a gyara shi ba mai shi na amsar daya bata sam bata mata dadi ba amman kuma saboda me bai bata amsar data dace daita ba“?
“Ko me yasa dakin baya bukata ?
Saboda babu wani abu da akeyi ajikinsa komai daidai ne very nit .”
Ta rausayar masa da kwayar idanuwanta cikin tsigar harara tace “ to amman dai naki ko baa komai acikinsa bai kamata a wayi gari batare da an gyara shi ba “shi dai wannnan dakin baya bukata gyara ya fada cikin son abar maganar dan tunda ta nuna bata bukatarsa shima zai barta bazai dameta ba yadda ya share ya bar maganar haka itama ta share a ranta tace wannan dabarar bata yi ba uhm wane ma zatayi duk wanda ta dauko zatayi baya karbarta yadda ya kamata tsam ta mike ta koma kitchen ta sauke abinci ta shirya yadda ya kamata a food flaks ta fito dashi akan faranti ta ajiye shi a table ,duk da tasan ba yanzu zai bukata ba amman sai data tsokano magana “ga abinci fa har yayi .
Bai bata amsa ba jaguwa ya shigo sai dai ya zube akan kujera kamar bai ganta ba ya dauke kanshi suna gaisawa dashi ta mike ta koma dakinta ta dauko mayafi ta yafa tazo suka gaisa kallo daya yayi mata da amsa war ma ba a wadace ba, ganin haka taji gabanta ya fadi tasan ba haka ya saba mata ba duk yadda akayi tayi laifi tunda ba yau tasan shi ba shekara d shekaru tasan halinsa muddin ba wani laifi tayi ba bazai mata haka ba ko Ada can idan suna son su gane ammi ta fada masa sunyi laifi daga amsa gaisuwarsa suke fahimtar ta fad’a masa .
Hira ce ta barka a tsakninsu ita dai tana jinsu sai dai tabi duk wanda yayi magana da kallo gbdy ta rasa abinda tayiwa yayanta da yau yayi mata haka gbdy Ana’s shima ko kallonta bai yi ba sai ma sako labarin film din daya kalla yayi ta mike ta basu guri tana tashi taji ya sauya hira tana zaune a daki dake bata rufe kofar ba tana jiyo wata hirarsu wata kuma tana wucewa anan itama ta shiga hira da zuciyarta yadda zata samo kan mijita dan ta lura tsiraicin da yarinyar film din dazu tayi ya burgeshi ya matukar daukar hankalinsa akanta ,dole ta kawar da tsoronsa da fargaba da take ji tunda da kanshi yaso su kasance tare itace kawar dashi rike hannunta idan yayi zarewa take ya zama dole tayi wani abu .”

shiru tayi tana tunanin kayan da yarinyar ta saka cikin film kaya ne matsasu masu nuna siffar jiki Kuma ko shafiq ta sha fad’a mata alokacin ana shirin bikinta irin shigar daya kamata ta dinga yi kenan muddin yana gida amman kuma batayi amfani da abinda ta fada ba koda kwanciyar barci zatayi ta nuna mata irin kayan da zatasa amman sai taki koda ta saka sai saka kayan da zasu rufesu wannan yana nufin da bataji maganarta ba kuma dole da laifin hada matsayinsa datayi da yayanta ta tashi ta ta bude wordrob din kayanta idanunta ya sauka a inda ta jera kayan bacci ta fara dubansu daya bayan daya wacce zata saka mashi yau, duk wanda suke gurin da zarar ta kalla sai ta sauke ajiyar zuciya ta jinjina kai tana hango girman abinda zai biyo baya .”
Har ta gama bataga wacce zata iya dauriyar sawa ba tayi tsaye jikinta à sanyaye wannan ita kadai ce hanyar da zakibi ki jawo hanakalin mijnki gareki dan Samar masa farinciki wata zuciyar ta kawo mata nata agajin.

Akwai kananun kayan daya siyo mata atarewarta gidan bata jima da fara dubasu ba taci karo da irin kayan da yarinyar film ta saka sari ne mai sharara ta tsura wa matar dake jin kwalin ido shigar iri daya ce dana wannann matar ta film kayan ya rufe mata jiki amman fa koina ya fito ya nuna kodan da ruwa ajikinta ne batasani ba .
Ta dan yi murmushi domin hangota datayi aciki kayan ta ajiyeta gefe yau zata ajiye kunyarta da tsoronsa ta saka mashi wannnan kayan ta rufe komai ta shiga bayi jin har an fara kiran sallar azahar tayi alwala alokacin har sun fita ta gabatar da sallar bayan ta idar shiru basu dawo ba abincin ma basu ci ba haka tayita jin haushi amman koma menene laifinta take gani taci nata har bayan laasar bai dawo ba ita kuwa tana zaune zaman jiransa zuciyarta na sake bata hadin kai wajen zugata tai wanka ta fito ta dauki lokaci a gaban mirrow tana kwaliya ta dauko wannnan kaya daya bata wahala gurin shiryata ajikinta amman da kallon foster din jikin hoton ta samu ta saka har zata hakura da sawa ta jajirce .”
kayan sun zauna mata dam ajikinta mazaunanta suka fito sai motsawa suke ga dukiyar fulani nan sun yi dam dam tayi juyi agaban mirrow ta dubi kanta sosai kunya ta kamata anya kuwa zata iya wannan fitsarar jikinta ya fara sanyi lokacin datayi tafiya kadan agaban mirrow tana juyowa tana kallon bayanta yadda yake wani motsi tana da alwala dama kuma abincin dare shi zai koma na dare tunda flask din mai daukar zafi ne .”
Aka yi sallar magriba har zuwa ishai duk bata ga shigowarsa ba dan haka ta koma falo ta zauna zaman jiransa sai dai ta cire after dress din ta bar kanta da rigar data sanya sai dai ta rufe kofar idan taga alamun su biyu ne ta mayar da after dress din idan kuma shi kadai ne ta bar kanta haka dan zuciyar ta narke ita kanta tana bukatar mijinta har kusan tara tana zaune tana maimaita kallon film din daya kalla da safe gurin jarumar kawai tafiye kallo ita da take mace ma ta burgeta inaga nmj da yake cike da shaawa tabbas dole ta burge anas naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana godewa allah daya bata gabbai masu kyau abinda mijinta yake kwadayin gani .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button