KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️37

……..”Ke  aganinki  har yanzu na dace dake  ?me yasa bazaki fahimci illar abinda kike son yiwa rayuwarki ba  ?yayi mata tambayar kamar bai ji dadin maganar data fada masa ba  ,ya lumshe rikitattun idanunshi  tamkar  tana gabansa  saboda sanyin dadin dake kai kawo a sansar jikinsa ,yayinda har lokacin  hannunsa ke  aikin shafa faffadan qirjinsa “eh kai kadai ne ka dace dani adnan  shiyasa ,kai ne zabina , na baka yardata da amincewata da kai kawai zan iya rayuwa ,
Murmushin gefen baki yayi sannan ya d’an motsa lip’s  dinsa kamar zai yi  magana sai kuma yayi shiru  ya kasa furta komai ,ya cigaba da lumlumshe idanunshi  yadda yake murmshin farinciki haka yaransa dake tsaye a gefensa suna dabansa suke tayasa murmushi .”

wani irin yanayi ya shiga    mai wuyar misaltuwa sosai tsigar jikinsa ke mikewa  ,ta kwantar da murya sosai tana fada masa zantuttuka masu sanyi da ratsa sansar jiki ,sosai ta dinga zayyane masa muraran qaunar da take masa ,a hankali ya fara jin jikinsa yana samun sauyi tamkar ana  masa wanka  da ruwan sanyi ,cikin mintuna da basu wuce goma ba komai nasa ya sake  sauyawa  maganarta ba iya gangar jikinsa kawai ta tsaya ba har  kunnuwansa sun daina fahimtar maganar kowa sai nata ,suna cikin  haka ya jiyo sautin muryar mahaifiyarta tana kiran sunanta “habibi I will call you back ” ta fada tana katse kiran .”

ya dan lashi lip’s dinsa na  kasa yana mai maimaita sabon sunan data kirasa dashi  a saman lip’s dinsa “habibi! ta yadda babu mai ji “Oh my god tanwer  allah yasa karki zautar dani ,gbdy hakurina ya kusan karewa akanki ,ya  ajiye wayar hannunsa akan table din gabansa ya had’e hannunwansa guri d’aya ya tsarkesu yana sake lumshe rikitattun idanunshi anas ya sauke numfashi tare da d’auke bakin bindiga akan alhaji tahir ya kai goshinsa batare daya ce komai ba  ,a natse jaguwa ya d’auki kwalban wine da d’an yatsantsa ya mike tsaye a rikice  cikin tsananin tashin hankali duk suka dukar da kansu kasa kar kwalbar ta subuce a yatsansa ya samesu ,ya soma  tafiya a hankali dan kar kwalbar ta subuce ta fadi ,duk suka d’ago kansu suka juya suna dubansa yana yawo acikin lambum cike da matsanancin mamakinsa  dan basu ta’ba ganinsa cikin wannan yanayin mai tattare da shaukin soyayya  ba .”

sun sha jin ana’s na fad’a masa cewar ya fad’a soyayyarta  amman sai ya karyata hakan  ,yau dai  ga zahiri sun gani da idanuwansu bai  kuma isa  ya  karyata  hakan ba,ahankali ya juyo still da kwalbar a d’an yatsan hannunsa yana gama juyowa kwalbar ta fad’i akan table dake tsakiyarsu gabadayansu suka ja da baya da sauri sukayi ta kansu shi kuwa dafe goshinsa  yayi yana runtse idanunshi  ya koma mazauninsa ya zauna dafe da  keyarsa da hannunwansa duka yana fesar da numfashi bai ma lura da halin da suke ciki ba ,anas ya cire bindiga a goshinsa dan tun daya dafe goshinsa da bindiga bai cire ya kalli jaguwa  daga diramar soyayyarsa ba sai yanzu ,ya waigo  inda yake zaune yana murmushi yayi  masa kallon tsaf gbdy baya cikin haiyacinsa,
suka shiga kallon juna  ,gano yanayin baya cikin haiyacinsa yasa suka sake tattara hankalinsu garesa suna kallonsa har nazifi .”

ganin yadda gbdy  jaguwa  ya susuce  tare da lulawa duniyar tunanin soyayya yasa anas ya maida hankalinsa sosai a kan nazifi “za,a d’aukeka yanzu a fitar da kai yau daga gidan  nan ,zaka koma gidanka  ka cigaba rayuwarka da lamuran gabanka kamar yadda ka saba ,kasa aranka  cewar babu wani baraza da za’a sake yi maka ko kawowa zuciyarka farmakin boye an gama da wannan matsalar “ya karasa maganar yana kiran sunan eku !.
“Yes boss ya amsa masa cike da girmamawa da yake da haka suke kiran gbdynsu ,”ka tasa keyar wannan mutumin  ka mai dashi inda ka d,aukosa har zuwa lokacin da shi wannan zai dawo haiyacinsa asan yadda za’a yi dashi anas yayi maganar yana nuna alhj tahir dake rakube  wanda ruwan sama dake sauka  ahankali ya gama jika masa kayansa da jaguwa  wanda bai san a duniyar da yake ciki  ba ,
Batare da bata lokaci ba eku ya tasa keyar alhji tahir gaba suka nufi bangaren bq ya bude dakin daya kasance nashi né shi kadai  ya turasa ya janyo kofar ya rufe sannan ya kulle kofar da mukulli ya juya . “

Nazifi ya dube anas fuskarsa cike da matsanancin farinciki yace “na gode sosai  ranka ya dade  allah yasa ku gama da duniya lafiya ,allah kuma ya jikan iyayenku  idan sun  riga mu gidan gsky idan kuma suna raye ,allah ya kara musu lafiya mai amfani “Ameen suka had’a  baki gbdy ,amman  ranka ya dade wayata dake dauke da sheidu akan dady fa ?”Karka damu a yanzu zamu kwashe komai dake ciki mu baka wayarka ,sheidu zai cigaba da kasancewa agurinmu  ne kawai , gyada kai nazifi  yayi dan ya yarda dasu dari bisa dari a dan zaman da yayi tare dasu ya amince bazasu yaudaresa ba tunda ga kamanin  alhji tahir nan   ya canza ba sai an fada masa ba a inda aka ajiyesa muguwar wahala yake sha  .”wanda shi bai sani ba ba iya alhj tahir ne kawai ke cikin wannan halin baka’i zaune acikin gidan ba suna dayawa .”

a hankali ya  dan juya yana satar kallon jaguwa da shaukin soyayya ke dibarsa yana son yayi masa sallama da karin godiya akan taimakon da yayi masa mman babu halin yin haka , ya juyo da hankalinsa ya fuskanci ana’s yana cewa “ranka ya dade ina da wata yar tambaya da zanyi maka idan bazaka damu ba ?karka damu kayi tambayarka Ana’s ya fada yana bawa sky umarnin ya kwashe komai daya danganci sheida akan alhj tahir acikin wayar nazifi ya kawowa nazifi wayar ,ya juya da sauri ya bar gurin domin aiwatar da abinda aka sakashi.”

“Tambayata shine ku din su waye domin ya kamata nasanin kafin na bar gidan nan dan ina komawa  gida dole yan’uwa da abokan arzikina zasu so suji komai daya faru dani ,sannan zasu so suji su wadan ni mutane ne  suka taimaka min  jami’an tsaro ne ko kuwa akasin haka?”kada  kayi mafarkin fad’awa kowa komai daya faru da kai dan bama son asani shiyasa ma muka rabaka da sheidar hannunka, bama bukatar kowa yasan su wayemu dan duk aikin da zakayi dan allah bai dace wasu su sani ba .
nazifi yayi shiru yana sauraransa yana nazarin maganarsa só yake ya gano gaskiyar su din su waye ga bindigu kala dabam dabam agabansu  kamar jami’an tsaro kamar kuma yan fashi da makami a shigowarsa gida yaga abubuwa dabam dabam duk da  a killace yake amman ya kan leka ta window  dakin daaka masa masauki idan yaji motsi, mutane dabam dabam suna shigowa gidan  idan kuma dare yayi yana jin Ihun mutane suna kuka da neman dauki wanda ya rasa dalilin haka  ,sannan yanzu haka gashi agabansu amman bashi da dalilin sake antaya masa wata tambayar yaja bakinsa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button