KUSKUREN BAYA 1 TO 48

yayi shiru yana kallon cikin lambun yana saka da war wara acikin zuciyarsa gargadin da anas yayiwa alhj tahir ne dazu ya shiga dawo masa daya bayan daya yana samun kyakkyawan mazauni acikin kwakwaluwarsa “lallai su din sunfi kama da yan fashi da makami abinda ma zuciyarsa yafi yarda dashi kenan sune sukayiwa mahaifin tanwer fashi sannan suka wuce daita na tsawonlokaci , idan ba haka bane a ina suka san alhji tahir ? me ye kuma hujjarsu nayi masa gargadi akansa? tambayar da yayiwa kansa kenan wanda bashi da mai basu amsarta .shiru ya cigaba dayi agurin yana sake yiwa tunaninsa dalla dalla lallai so yake ya gano wani abu a tattare dasu da zai bayyana masa gaskiya sai dai duk dogon tunaninsa da nazarinsa bai hango abinda zuciyarsa ke zarginsu akai ba dan kuwa babu ta inda sukayi kama da yan fashi ,idan kuma sun tabbata yan fashi ne to kuwa nasu fashin mai kyau ne da adalci “to ma ina tanwer din take ?tambayar da zuciyarsa ta sake aikawa kwakwaluwarsa kenan har ya bude baki da niyyar yi magana sai kuma ya fasa yaji kamar an saka superglue ya manne masa baki ne .”
cikin kankanin lokaci sky ya dawo hannunsa rike da wayar nazifi ya mikowa anas shi kuma yace ya mikawa nazifi ,ya karba yana sake yin godiya sannan anas ya bawa scorpion umarnin ya kai shi gida atare suka mike suka soma tafiya ,yayinda gbdynsu suka tsura wa jaguwa idanunsu suka cigaba da kallonsa eku sky suka kallesu sannan suka kalli jaguwa tare da kwashewa da wata dariya garin subawa juna hannu dan su kashe suka bugi table din gabansa nan take glas cup’s din dake ajiye akai suka tarwatse ,bugun table din ne ya dawo da hankalin jaguwa jikinsa ya kuma ankarar dashi halin da yake ciki “Am ranka ya dade daman haka idanunka suke ?” “Sosai ya sake dawo wa haiyacinsa yana dubansu fuskarsa tattare da alamun tambaya “lallai wannna soyayya hakika ta tabbata sosai jabir ya fad’a yana murmushin tsokana” da wa kenna?jaguwa ya tambayesa ya dan kallonsa idanushi still a lumshe tamkar wani mashayi “da kai mana idan ma ba kai ba wa za’a nunawa irin wannan soyayyar ? “uhm ka duba dan allah sai kace ita din ba diyar minister ba, idan tana yin wasu abubuwa sai ka dauka ita din ba diyar babban mutun bace ,amman kowa ya ganta yasan yar gidan manya ce jubi ya fad’a yana kwashewa da dariya.”
“Nata kuke gani shi fa ?gbdy ya canza tamkar ba jaguwa ba ,yau dai kowannenmu ya gano wani sirri atattare dai kai ba kuma ka isa ka mutsa mana ba ,mu dai zamu maka fatan alkhairi dan gaskiya jaguwa ka dace kaji dadi wallahi karka tsaya sanya ka duba yarinya irin wannan haka amman ta makale sai kai congratulations kamil ya fada yana mika masa hannu yana sakar masa murmushi amman kememe jaguwa yaki bashi hannu dan wani mugun haushinsu da haushin kansa yaji .”
“yanzu dai ku me kuke tunanin abun zai kasance ? jaguwa ya mike tsaye cike da jin haushi “kai dan allah kuyi min shiru karku dame ni da wata magnr soyayya” ya soma tafiya anas yabi bayansa da ido cikin jimami kawai yana kallonsa ko har sai yaushe zai fahimci halin da yake ciki ?yana gudar masa randa soyayya zata wujijigashi tayi waccajali dashi ,
yaso yadda ya samu damar nan yayi amfani daita “kaji abinda yace Ana’s wai kar mu damesa a zuwan ba gskiya bane ?”Haka zai ta nuna mana anas ya fada tare da kokarin mikewa tsaye “ina ma zanga wannan yarinyar dana fada mata ta rabu dashi da fita rayuwarsa wallahi zai fito da abinda ke ransa “bazata iya ba domin ba irinsu jaguwa mace
kewa irin wannan wasan ba , ko kun manta cewar shi din dokin tsare ne ya fada yana cigaba da tafiya ya nufi hanyar fita daga cikin lambum.”
kai tsaye jaguwa hanyar dakinsa ya nufa yana gyara kwalar rigarsa yayinda hoton fuskar tanwer ya shiga masa gezo acikin kwayar idanunshi ,tun daga kwayar idanunta karamin bakinta hip’s dinta har zuwa qirjinta dake cike bammm a nan ya tsaya yana kare musu kallo tamkar a zahiri , nan kuwa tunaninsa ne kawai ,a hankalin ya fara juyi acikin dakin tare da zaro tsarkar gold dake makale a wuyansa boye cikin rigarsa yana juyawa a hankali tamkar yadda yake zagaye dakin fuskarsa kunshe da murmushin farinciki yana sake zurfi acikin tunaninta.”
a natse ya daga kansa saman dakin yana kallon celling dakin “ina sonka adnan dina ban samu damar yin soyayya da kowa ba sai da kai ,dan allah kace kana sona ,ka canza sana’a zanyi confused din iyayena su bari na aureka sannan zan nemo maka sana’a bazan barka haka ba kalamanta suka dinga dawo masa daki daki suna haskaka zuciyarsa ,
a hankali ya jingina bayansa da bangon dakin tare da tokare kafarsa daya “bayan kamar minti goma ya sauke kafarsa yasa dan yatsantsa jikin bangon takin yana tafiya yana bin bango da yatsansa har lokacin murmshi ne kwance a fuskarsa ,yau yana cikin farincki mara misaltuwa ,na kiran da tanwer tayi masa ne ko kuwa naji albishirin dinta ne shi dai bai sani ba amman dai yana cikin farinciki da bai san dame zai misaltashi ba .”
“nima ina sonki tanwer son da ban taba tsammanin yiwa wani mahaluki irinsa ba ,ina jinki ajinina acikin bargona da tsokar jikina bazan iya rayuwa babu ke ba but just give me time ina bukatar lokaci zanyi wani abu akai ,wani irin sanyayyen dadi ke bin lungu da sako na sansar jikinsa ,jinin jikinsa ya ninka gudu akan yadda yake yi ,a natse ya karasa gaban mirrow ya tsaya ya tokare hannunsa da jikin bango yana kallon kansa ta cikin mirrow , yatsan dayan hannunsa ya kai cikin bakinsa yana cizawa a hankali a hankali yana jin kamar yatsunta yake cizawa “ina son fararen fure ko zaka dauko min ?ina sonka adnan na yarda da kai na kuma amince da kai ,ya tuna lokacin daya kai kangon gida da bai yi tsammani zata iya rayuwa acikinsa ba amman da budar bakinta tace “me zai hana adnan ?wallahi zan zauna dan fiyye min kowani gida muddin da kai zan rayu acikinsa karka wani damu zan zauna “. ya sauke naunayen ajiyar zuciya a daidai lokacin da ana’s ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya ya harde hannunwansa a qirji idanunsa akansa,jaguwa bai juyo ba sai ma kura masa ido da yayi ta cikin glas mirrow yana kallonsa kafin daga baya ya juyo gbdy ya fuskanci anas soyayyar tanwer na sake kanainayesa “yanzu me ka tsayar akan yarinyar nan tanwer?” I don’t know what to say but is like bazan iya cigaba da rike wasu abubuwa ba zan dai yi shawara da zuciyata nan kusa zan tsaida maka
yayi mgnr hannunsa na shafa faffadan qirjinsa ,
gyada kansa kawai anas yayi tare da sauke boyayen numfashi yace “please jaguwa ka hanzarta kayi abinda ya dace ka daina barazana da rayuwar yarinyar mutane ” .
Ajiyar zuciya ya sauke tare da tsura masa ido yana jin yadda zuciyarsa ke mugu mugun bugawa ya kira sunansa “anas look at me babu wasa acikin kwayar idanuna idan bazan yi wani abu akai ba kai kasan waye ne I won’t lie to you ,zanyi wani abu akai amman ban sa yaushe bane , yau né gobe ko anjima né bansani ba ya karasa maganar tare da yin shiru ya cigaba da kallon anas ,dakin dakin ya dauki shiru bayan ya rungume hannunyensa duka sannan ya janyo wayarsa da yaji tayi kara alamun shigowar sako ya shiga dubawa yana gamawa ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya soma magana a tsanake ” satin nan zamuyi aiki ma alhji bello yanzu sakonsu ya shigo da inda zaayi aikin sai dai bana jin acikin mu biyar din nan akwai wanda zashi zan tura sconpio domin aikin zai fi dacewa da mutun daya ne ,nan da 2 week kuma zamu shiga aikin akan masu safarar hodar iblis ,sannnan ina saka rai mlm mudi zai turo mana sako yau ko gobe domin musan ta yadda zamu bibiyi alhji tajudenni da duk wasu masu irin sana’arsa .”