KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Tayi shiru tana nazari maganar da zata fada masa amman kuma tayi shiru saboda ganin rashin dacewarta abinda zata fada masa da abinda tayi yake burgesa da jikin da yake kallo na mazan banza amman sai tace tayi kokari sosai ta kuma burgeni,” yayi dan murmushi “da alama kin fara son kallon india ta dubi abincin dake gabansa “kaci abinci mana ya dauki spoon ya cigaba da cin abinci yayi shiru ta fahimcesa idan yana cin abinci baya magana irin dibiyar yayanta kenan yanzu ma tunda ya fara bai ce mata komai ba sai kallonta da yake kawai yana murmushi,”bayan ya kammala basu jima da zama ba aka kira sallahr magarib dan haka ya fita zuwa massalacin dake kasan unguwarsu daga nan kuma ya tsaya tare da wani mutumi wanda anan massalacin yasan sa malam bala bai dawo gida ba dai tara saura yana shigowa kuma kamar kullum ya rufe koina ya samu hally zaune a falo ya zauna kusa daita yana dubanta itama shi take kallo tana jin sallar soyayyarsa na fizgarta ta dan yi murmushi “ka shigo gida kenan .?”

“Eh ina kike son naje  my princess? shima ya mayar mata da tambayar bani inda zani daga gida sai aiki sai massalaci wani mutun mai suna malam bala yace na gaisheki mutumin yana da kirki sosai ,”ina amsawa  wata zan kaiki ki gaishe da iyalinsa kema dai kisan wasu acikin unguwar nan ta amsa da lallai kuwa da ka kyauta ni gida ma nake son zuwa gurin ammi nayi kewarta sosai aunty shafiq ma tunda suka zo da yaya sau daya bata sake zuwa ba wai bazata gane gidan ba “to bari inshaallahu duk zan kaiki cikin satin nan idan na samu lokaci ,ya  karasa mgnr yana kai hannunsa ya shafa gefen fuskarta zuwa wuyanta sannan ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta yayi mata magana cikin rada ,nan take ta fahimci manufarsa wata irin kunya ta rufeta gbdy ta rasa inda zata saka kanta  da dariya kema kina bukatar mikinki .”

“Nan take ta gitsine fuska “Aa ta fada saboda kada ya kara nata kunya “Kunya dai kunya dai ni na rasa wace irin kunya ce haka kike daita batayi magana ba illa mikewa datayi  da niyyar shiga daki dan ta shirya kafin shigowarsa .ya rike hannunta cikin kallonta “ina zuwa muna hira ?ta dawo ta zauna kusa dashi ya jawota jikknsa ya kwantar daita yana kallon fuskarta yace ina son mu dan yi kallo kafin mu kwanta ya kika gani ?”.
“Tô kunna bari naje yanzu zan fito zan dan watsa ruwa ne a jikina bana son dare yayi sosai ban yi wanka ba “hakan yayi kyau ina jiran ki na siyo miki abun dadi ya fada yana sakar mata hannu ta tashi ta bar falon zuwa dakinta , a daren sunyi kallo sannan sun kwana cikin jin dadi fiyye da jiya yayinda bangaren oga jaguwa yayi  kuwa yayi kwanan wahala sakamakon tunanin abar qaunarsa da shaawarta tun lokacin da tace zata kirasa back yake dakon kiranta amman har karfe biyun dare daya kasa runtsawa shiru  bata kira shi ba ,sai ya dauki wayarsa da niyyar zai kirata sai mummunar zuciyarsa ta hanashi tare dayi masa gargadi mai karfi .

Ya janyo tautausan bargo ya lullube rabin jikinsa yana tunaninta , idan kwakwaluwarsa ta hasko masa bakinsu hade dana juna  sai yaji zirrr a sansar jikinsa idan ta hasko masa closing dinsu yana romancing dinta shima sai yaji tsigar jikinsa sun mike yar-yar  gbdy ya takure jikinsa guri daya yana jinta gbdy  ajikinsa numfashi ma da kyar ya dinga fitarwa ga wani faduwar gaba da yake ji akanta ranar dai bai wani samu isashensa bacci washegari kuwa bai tashi da wuri ba sai   gurin karfe goma shabiyu da rana  ya tashi  ya shiga wanka bai dade da fitowa  ba anas ya turo kofar dakinsa  ya shigo alokacin ya gama shirya kansa cikin wasu hadaddun  kananan kaya farar  riga da wando light blue yayin da takalmin dake rufe dakafafunsa ya zamo canvers ne  farare sol ya dan dago ya kallesa ta cikin mirrow murmushin gefen baki jaguwa ya sakar masa  “lover man har ka karaso ai na dauka sai irin biyun din zaka shigo ?”kai dai ka sani  dasa ido  kaima kayi kokari ka zama kamar din a  dinga misali da kai “haba dai Ana’s ina zan iya abinda kake yi kawai  na zauna ina fadawa mace ina sonta ai kauyanci ne  da sharme wallahi jiya maganarka dariya tayita bani wai muradin raina  imagin ma wa yarinya karama kamar hally ya fada yana sake murmushi sannan ya dauki kwalbar turare ya feshe ilahirin jikinsa “zaka sa nayi maka mummunar addua akan soyayya fa ,”ka dade bakayi ba idan ma kayi na shiga damuwa kai  ne aciki muje ka rakani wata yar unguwa ya dauki agogon diamond fari sol  ya daura a tsintsiyar hannunsa ya fara tafiya “muje ko !”
Ya biyosa abaya suna taku a hankali suna zolayar junansu har suka karaso  babban falon gidan inda suka iske sauran abokansu zaune suna zukar tabar wiwi “zamu dan fita amman yanzu but bazamu dade ba zamu dawo kowannenku ya zauna a shiryensa akwai mahimmin aikin da zamu tautauna akansa yana gama fadar haka ya sa kai batare daya tsaya yaji abinda zasu fada ba anas ya biyo bayansa zuwa haraban gidan suka bar zuciyarsu da kunci da watsi Watsin inda zasu tsaki kamil yaja da karfi “kuna ganin lokaci bai yi ba da zamu fara aiwatar da nufinmu ba ?lokaci yayi mana wallahi idan nace muku closing dinsu yana min dadi nayiwa allah karya ka duba ko operation zamu fita hankalinsa na kan anas baya kowa gargadi mai karfi sai Ana’s a komai sai ya nuna bambamci komai Ana’s dai anas jubi ya fada cikin tsananin bacin rai “ku matso kuji suka matso a tare jabir yayi maganar sirri a tsakaninsu a tare suka kwashe da wata magaukaciyar  dariya “gasky wannan shawarar tayi daga yau zamu fara aiwatar da nufinmu shigowar eku ne ya katse masu maganarsu ya tsaya yana tambayarsu ko akwai abinda zasu bukata zai fita kowannensu yace bai bukatar komai dan haka ya juya ya fice .”

A hankali suke tafiya acikin mota suna cigaba da hira har suka karaso bakin get din hospital din  tanwer suka shigo kai tsaye cikin haraban hospital din kasancewar makeken get din a bude yake “me kuma zamuyi a hospital?kasa ido mana kaga ikon allah ,
“hope ba wani ne cikin yanuwa bashi da lafiya ba ?
idan wani ne me zai kawo mu nan bayan ga sadiq wata nazo gani ya karasa maganar yana kokarin  parking din motarsa a inda aka tanada domin ajiye motoci ya soma kokarin fitowa yana duba agogon dake daure a hannunsa daya  da rabi adaidai yana gama fitowa lokacin tanwer suka jero tare da doctor muyis da fadela abokiyar aikinta yayinda doctor muyis ke  faman yi mata naci da magiya .”
suka tsaya a bakin motar tanwer fadela na cewa “haba tanwer ki tausaya masa  mana ki dan samar masa gurbi azuciyarki ko babu yawa ne a soyayya baa son ka zurfafa kiyayya “barta kawai fadela só take ta kasheni , tanwer tayi murmushi “haba fadela  wallahi a halin yanzu  bazan iya wahalar da kowa a soyayya ba  ,kai kuma dr allah bazai sa na kashe mutun ba .”da wahalar da zuciyata da kike ai gara ki kasheni zan fi bukatar mutuwa akan wannan rayuwar ko ba haka fadela? “aa bazaa yi haka ba dr ta dai amince cikin sauki da dadin rai mu sha biki ba sai an kai ga haka ba ,ta fada tana juyawa ni zan wuce ana jirana naso ma muje tare da tanwer ne amman yanzu ina cewa muje zata fara dojewa ita dai ban san abinda mutane suka mata ba da bata son shiga cikinsu ? ta nufi gurin motarta tana magana ta bude ta shiga gidan baya ta zauna tanwer taji wani abu acikin maganar fadela wasu kuma sun bi iska  tayi murmushi  har fararen hakoranta suka bayyana tana kokarin sake cewa wani abu kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya harde hannayensa a qirjinsa  rikitattun idanunshi akanta yana kare mata kallo ,kasa magana tayi nan take kuma ta sanyawa jikinta natsuwa ta shiga hankalinta hatta murmushin dake  kwance akan fuskarta ta dauke qirjinta ya shiga bugawa da karfi tamkar zai fasa qirjinta ya fito waje cigaba da kallonta jaguwa yayi fuskar nan nashi babu annuri sam “ya kika yi shiru madam dina inshaallahu ki fadi min  abinda kike son nayi ki soni ,wallahi  ni magana dake ma kadai yanasani farinciki , bata kallesa ba ta furta “dan allah dr muyis kayi shiru na shiga rudani né fadela data shiga motarta kam batasan wainar daake toyawa ba sai dai ta dan leko ta side din da take zaune domin tayi musu sallama direbanta yaja suka wuce .
a hankali  jaguwa ya soma taku cikin isa da izza hannuwansa duka zube cikin aljihunsa yana kokarin karasowa inda take ai nan take zuciyarta ta shiga karkarwa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button