KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️38

……tafiya kawai yake fuskarshi babu annuri kana kallonsa zaka fahimci zallar ‘bacin ran dake tattare dashi ,ran nan nashi yayi baki yayi kololuwar ‘baci yana gama karasowa inda take tsaye bai kalli dr muyis ba ya kai kyakkyawa hannunsa ya rike tsintsiyar hannunta gam cikin nashi yana tsareta
da rikitattun idanunshi masu matukar firgitawa da hargitsawa mutun lissafi , a qalla ya dauki minti goma yana tsaye yana kallonta zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ,yana tunanin abinda ya kamata yay mata ,wata zuciyar ta bashi shawarar
ya hau dukanta yana yaryarfa mata maruka ko hakan zai sa yaji saukin zugin da zuciyarsa ke yi ,yayinda wata zuciyar ke gargadinsa ba dan jin tsoron abinda zai faru ba sai dan kasancewarta yarinya .
wasu minti goma suka shud’e yana tsaye yana kallon kyakkyawar fuskarsa , kafin daga baya ya jata zuwa gefe wanda tazaransu da dr muyis bai fi taku hudu ba kuma tana da tabbacin duk abinda jaguwa zai fada mata tabbas zai ji ,ita a tunaninta ma gurin da yayi parking din motarsa zai kai ta ko cikin motarsa sai taga sabanin haka, ganin zai soma magana cikin zafin rai tace “muje daga can ta nuna masa nesa da inda suke komai zai fada mata babu me ji ,amman da yake ransa a bace yake uwa uba kuma ga tsabar taurin kai sai cewa yayi “bazaa je
ba anan nayi niyyar magana banga uban daya isa yasa na kara taku daya daga nan ba tukun ma me kike yi tare da wannan mutumin ? qirjinta yayi mugun dokawa da matsanancin karfi har ta kasa bude bakinta,hakan ne ya bashi damar cigaba da magana “bakin san Idan mutane suna ganinki da maza kala dabam dabam ba zasu dauka kmr baki da kamun kai ne ba? “wallahi mutane zasu daukeki useless idan kika cigaba da kulaye kulayen maza “stil shiru tayi ta kasa magana duk da bakinta abinda yake son yi kenan ta tsaida shi daga abinda yake fad’a .”

hannunta dake cikin nashi ya sake matsewa sosai yana sake tambayarta cikin zafin rai “me yasa kika tsaya dashi ?”Ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace “ban sani ba kai ne dai kake ganin kamar bani da kamun kai ,amman kowa agurin nan yasan ni wacece,sai abu na gaba ,adnan am not useless your sister’s your aunty’s I wont put your mother coz I use’s to respect mum, but your sisters are useless , your Aunty’s are useless even the children that you wont to born they wil be useless inshaallahu, in allah yaso ya yarda sune useless banice useless ba idan kaga dama karka kara zuwa inda nake ko yanzu ai ban kiraka ba kona kiraka ne da zaka fada min mgnr banza .”?
Shiru yay yana kallon karamin bakinta da take motsawa a hankali tamkar ba daga cikin zafafan magana ke fitowa ba yana jin wani irin zafi daga cikin kasan zuciyarsa idan yace bai ji zafi da ciwon maganarta ba yayiwa kansa karya “ita kuwa wani sanyi dadi ne mai tattare da farinciki ya lullubeta alokacin daya, duk da taji zafin kalamansa amman kishinta daya nuna qarara yayi mata dadi kamar tayi masa dariya mai hade da kukan zafin furucinsa amman tsoronsa ya hanata ,yanayinsa kawai zaka kallo ya tabbatar maka da abinda ke dawainiya dashi gbdy Kishinsa ya fallasa abinda ke cikin zuciyarsa ,yana mugu mugun qaunarta amman tsabar miskilanci da jin kai ya hanashi fallasa muradinsa .”

“Tanwer I want to ask you a question tayi shiru tana kawar da fuskarta gefe ya kai hannunsa ya dawo da fuskarta garesa “why did you abused my sisters and my aunts ,Since when me and you meet each other which day did i abused you da zaki sako sister’s dina cikin magana?adnan ka kirani da …..”shiiiiii !
Yay saurin katseta qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske “abinda nake so dake wannan ya zamo shine karonki na farko kuma ya zamo na karshe da zaki sake kula wannan mutumin koda kuwa gaisuwa ce bana só idan ..”
“Idan na sake kulasa fa me zakayi?” tayi masa tambayar cikin karfin hali tana kallon tsakiyar idanunshi at the same time kuma qirjinta na luguden bugu ” wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa “tmbyta abinda zanyi kike ko kuma zaki Kibi  umarnina ?”bazanbi umarninka ba tunda ba aurena kayi ba ,baka aureni ba kaga ai bazaka hanani kula duk wanda raina yake so ba ,ko kai mijina ne ?ta sake jifa masa tambayar datasa zuciyarsa shiga tashin hankali ,magangunanta fa
sun doki zuciyarsa da kunnuwansa sosai sannan sun shiga kai kawo acikin kwakwaluwarsa sai yaji kamar ta sake kunno masa wutar kishinsa ne da yake ta kokarin dannewa acikin zuciyarsa ransa a matukar bace yace “kema a she kamar sauran mata kike da rashin mutunci ?kamar ta girgiza masa kanta alamun aa sai kuma ta fasa tunda tasan tayi rashin mutunci “ko da yake bai kamata nayi mamaki manyan maganganunji ba ,idan dai tsiwa da rashin kunya da rashin mutunci ne gidan nazo ko ba haka ba ?”
“Ban sani ba Karka sake kirana da wadan kalmomin bana..”Bata kai karshen maganarta ba ya dalle mata baki da dayan hanunsa da sauri ta dafe bakinta saboda azabar da taji ya ratsata nan take idanunta ya canza kala ta dan juya bayanta nan taga dr muyis tsaye ya kafesu da idanu yana Kallonsu yanayinsa
da alamun tashin hankali dukkanin alamu sun nuna yaji abinda ke tafiya ,daga can gefe kuma anas ta hango ya harde kafafunsa ya tallabe habarsa da hannunsa daya shima yana kallonsu ,numfashi ta sauke sannan ta dawo da kallonta garesa ta tsura masa idanunta cike da kwalla saboda har lokacin tana jin zafi a abakinta .”

Shi din ma kwayar Idanunshi suna kanta yana jin wani irin tuttukin bakinciki acikin ransa “ba laifinki bane tanwer samu kikayi nazo gurinki shiyasa kika samu damar yimin rashin kunya da wulakanci”ya girgiza kai yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa “I don’t know that you are in responsible girl like this tanwer, kullum kina yaudarar kanki da kanki da sunan kina sona idan babu ni arayuwarki bazaki iya rayuwa ba amman kullum kina makale da wasu mazan kina shirmen banza dasu Alhamdulillahi for Almighty Allah who created me and you quickly show me the type and the kind of a girl you are ,sakarwa maza fuska, basu damar suga murmushinki a árha ,do you think that’s life,wallahi what you’re doing is a big shame for you ,my advice to you stop calling me or chart me again ,and I don’t won’t to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi “yana gama fadar haka ya sakar mata hannu da karfi yana jan tsaki sannan ya juya a matukar fusace ya soma tafiya cikin zafin rai kamar zai tashi sama .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button