KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

jaguwa ya tsura masa ido kawai yana kallonsa tare da nazarinsa a hankali ya kai hannu yana shafa fuskar anas yana cigaba da kallon fuskarsa da yake kallon alamun dariya a tattare daita muryarsa a kasalance yace “Ana’s dariya ko ? yay saurin girgiza masa kai alamun a’a “no karka ce min haka mana dariyar ne a fuskarka “dole yasa dariya ta bayyana a fuskar anas,jaguwa ya juya zai bar gurin yayi saurin riko hannunsa ya fixge hannunsa a fusace yana cewa “dole kayi min dariya tunda ga mahaukaci a gabanka ka samu ,please ka saurareni ba dariya bane ,bazan iya sauraron ka ba, zo dai ka wuce gida na sallameka wata dariya ta subucewa Ana’s yana cewa “maganar tsara aiki fa ?an yafe maka kuma an sallameka bye ya fada yana zubewa akan gado ya kwanta flat yana fitar da numfashi sama sama ya runtse idanunshi sosai yana ciwo mai tsanani aransa anas bai yi magana dan yasan taurin kansa ba saurararsa zai yi ba dan haka ya dauki faranti zuba tukar sigari da kwalin ya fita zuwa falonsa ya ajiye karamin faranti ya fice da kwalin sai dai bai bar gidan gbdy ba ya samu guri ya zauna a falo cikinsu anas basu nuna masa komai ba aka cigaba da hira dashi .”

Bangaren tanwer kuwa da Kuka ta karaso gida ta bude murfin ta fito daga cikin mota bata tsaya rufewa ba ta shigo babban falon gidansu ta zauna a hannun kujera tana kuka kamar wata karamar yarinya kuka take sosai har mumy da masu aiki suka fito lokacin ita ruky tana daki tana sallah ganinta yasa masu aiki suka juya suka koma kitchen mum ta isa inda take tare da dafa kanta “me ya faru tanwer ? kuka ta cigaba batare data bata amsa ba “tanwer taso mu shiga ciki ki fada min me ya faru dake kike kuka haka ? hannunta mumy ta riko suka shiga dakinta ta zaunar daita a bakin gadonta a lokacin kukan nata ya fara tsayawa “me ya sameki haka kike wannan uban kuka ? duk yadda mumy tayi daita ta fada mata dalilin kukan taki ta fada mata duk da mumy ta fara zargin ita da adnan ne domin idan bashi bane babu abinda zai sa diyarta kuka irin haka “adnan ne ko !?.

Tayi shiru har sai da mumy ta sake maimata tambayarta sannan ta gyada mata kai tayi shiru tana nazarinta sannan ta numfasa ta soma rarrashinta tare da mata nasiha akan rayuwar duniya”kiyi hakuri tanwer rayuwar nan sai mutun ya jajirce mata ya koyi hakuri da juriya hade da dakiya akan duk wani abinda zai samesa karki manta komai qaddara ne rabonka bazai taba wuceka ba ,wallahi duk abinda kika ga bai zo hannunki ba to barabonki bane amman muddin rabonki ne kina zaune zai zo ya sameki , sai abu na gaba banason nasan abinda ya hadaku amman idan kin san kece mai laifi kiyi kokari kikirasa ki bashi hakuri amman idan kin san shine mai laifi ki rabu dashi idan ya huce zai nemiki idan yana sonki “tabbas nasihar mumynta ya shigeta sosai nan take ta yankewa zuciyarta zata jajurcewa rayuwa zata koyi hakuri zata koyi yadda zata danne damuwarta akan adnan sannan bazata sake furta masa tana son shi gara ta fadawa wani akansa
Tayi shiru tana tunanin abinda ya faru yau laifin waye acikin ita dashi ..”?tayiwa kanta tmbyr tana kallon mumy dake zaune a gabanta kamar zata mata numfashi .”

“Ki kwanta ki dan huta ko zaki ci abinci ne akawo miki ?bana jin yunwa mumy ta fada a shagwabe,ban yarda ba dan nasan tun breakfast ne acikinki baki  ci komai ba ko ba haka?haka ne mumy amman a koshe nake ,saboda kun samu matsala da adnan ba ?mumy tayi maganr tana shafa fuskarta “no mumy ba haka bane kawai cikina ne a cushe ,yana daga cikin dabiyarki yanzu idan kin samu problem da adnan sai kiki cin abinci kefa likita ce kinfini sanin illarsa ,bari naje na kawo miki ko kadan ne kici kinji mamana ta gyada mata mai kawai ba dan tana jin yunwa ba sai dan kawai ta kwantar mata da hankali.
mumy ta mike tsaye tana sakar mata murmushi ta fice daga dakin bata jima da fita ba ta dawo hannunta rike da tire tanwe ta mike da sauri ta amsa tiren a hannunta “sannu mumy that’s why I love more than anything ina sonki mamana ta fad’a tana ajiye tire “nima ina sonki kici abinci ina zuwa ta sake juyawa ta fita tanwer tayi shiru ta kasa bude abincin bare tayi tunanin ci gbdy  abinda ya faru tsakaninta da adnan    ya tsaya mata arai ta rasa waye mai laifi acikinsu dole ba dan tana so ba tabawa kanta laifi ,nice mai laifi tunda na kirasa sister dinsa da Aunty’s dinsa da useless alhalin shi misali ya bani
ta fada hawaye na zubo mata akan kuncinta ,kenan nice ya kamata na kira na bashi hakuri ?ta aikawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar .”

Jiki a sanyaye ta yunkura ta mike ta tashi tsaye tana goge hawayen dake tsiyaya daga cikin kwarnin idanunta ,ta dauki tiren abincin da mumy ta kawo mata ta fito zuwa parlour inda ta iske ruky zaune tana buga game a wayarta tana ganinta ta bar abinda take ta fuskanceta tana cewa “amaryar a gidan adnan yaushe kika dawo ?tanwer ta sakar mata murmushin yake tana boye damuwarta sannan tace “ban wani jima da dawowa ba akwai labari ne ?
“Sosai kuwa idan kin huta kizo kiji , amman dai yau kin dawo da wuri ,eh babu wani aiki dayawa ne ta bata amsa tana shigewa kitchen ,ruky tabi bayanta da kallo aranta tace “ko me ya sameta duk tayi wani iri da alamun ma kamar kuka tayi ?allah dai ka iya mana abinda bazamu iya ba, allah karka barmu da zabinmu ka zabamana abinda yafi alkhairi a rayuwarmu, tanwer ta ajiye tiren ta fito ta dauki handbag dinta ta koma dakinta .”

ta zauna a tsakiyar gadonta ta fito da wayarta tana kallo tana jin mummunar faduwar gaba dake tattare da tsinkewar zuciya mai tsanani wankakkiyar zuciyarta ce ke bata shawarar ta kirasa ta bashi hakuri yayinda wata zuciyar ke kwabarta tana tuna mata gargadinsa gareta “my advice to you stop call me or chart me again ,and I don’t won’t to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi nan take idanunta suka ciko da ruwan hawaye jikinta ya dauki zafi ta koma ta jingina bayanta da abun gado hawaye na bin gefen idanunta “me zanyi yanzu ? tayiwa kanta tmby zuciyarta na rawa sosai ta shiga tunanin yadda zata yi “me zai hana ki kira anas tunda kina da numbersa gyara zamanta tayi sosai ta soma neman layinsa kira daya ya dauka yana kiran sunanta .”

“Tanwer !
“Na’am anas ina yini ?
“Lafiya tanwer ya aiki da fama da jama’a ?alhamdulillah ta bashi amsa muryata a sanyaye ,
shiru ne ya biyo baya na kusan second biyar tana son tmbyrsa jaguwa tana jin tsoron ko yana kusa dashi tajawa kanta bala’i dashi karon kanshi jin tayi shiru yace “yaakayi tanwer ?,adnan fa ? tayi mgnr muryarta na rawa “yana dakinsa jin haka yasa ta sauke wani wahalallen numfashi da ajiyar zuciya atare ,me yake yi anas ?gskya ban sani ba ya dai kwanata yanzu ma nake son na koma dakin na tashesa dan bai yi sallah ba .”
“Okay daman na kira ne dan allah ka bashi hakuri akan abinda nayi masa nasan ya fad’a maka komai daya faru ,yayi hakuri kuskure ne bazan sake ba amman shima ka fad’a masa komai zai min bana son yayi min a gaban kowa gara yayi min daga ni sai shi ko kasheni zai yi yayi na yarda bazai dameni ba amman a bayyana nasi banaso Ana’s ta karasa maganar tana fashe masa da kuka .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button