KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke “karki damu tanwer inshaallahu zan fada masa sakonki , kema ki cigaba da hakuri da wannan rigimammen abokin nawa abinda kuma yayi kishi ne ba komai ba “wallahi zan iya rike alqurani nayi rantsuwa dashi babu komai acikin raina akan dr muyis ,ba tun yau ba munyi maganar dashi dr muyis a abokin aikina na daukesa shi dai yana sona amman ni sam sam babu soyayyarsa acikin zuciyata adnan kawai zuciyata ke só amman yadda yazo yayi min agaban dr muyis ya bani haushi shiyasa nayi masa abinda nayi amman dan allah ka bashi hakuri bana son nayi abinda zan bata masa rai ,adnan yasan yadda nake sonshi wallahi da wani abu ma idan ance yayi min bazai ba i love him so much please let him try to understand naso nazo a yanzu amman yayi min gargadi kuma na tsorata da gargadinsa ta karasa maganar tana sheshekan kuka tanwer don’t cry please and kiyi zamanki zan fada masa sakonki idan ya huce zan kiraki a waya na fada miki yadda mukayi dashi sai ki kirasa kuyi magana “.

tayi shiru tana tsaida kukanta can tace “Ana’s kana ganin kuwa adnan nasona kuma zai aureni?gsky ni dai a tawa fahimtar yana sonki kuma yana da muradin aurenki amman dole sai kinyi hakuri da adnan tanwer amman dan so adnan na sonki zuciyarsa ce ke yaudararsa amman jikina yana bani lokacin yayi da zaki mallaki zuciyarsa gbdy abinda yayi ma dazu cikin so ne tanwer idan bai sonki bazai yi kishinki ba ke dai ki kara hakuri ki kuma yi addua abinda yafi zama alkhairi a tsakaninki dashi allah ya tabbatar mana sannan ki daina kula wannan dr din
Sun dan jima suna waya yana fada mata adnan na sonta murmushi jin dadi ne ya bayyana akan fuskarta take taji kashi saba’in acikin damuwarta ta kau a karshe sukayi sallama ,”


A hankali bacci ya dauke jaguwa daga kwanciyar da yayi duk da bacci yake amman hakan bai hana zuciyarsa suya ba har kusan karfe uku bai fito ba anas ya mike ya koma dakin ya dubosa stil bacci yake ya karasa inda akwatin kudi yake ya bude ya dauki daidai wanda zai bukata ya fita ya aiki sky yayi musu order abinci ya sake komawa dakin ya zauna ya kira layin hally kira biyu yayi mata sannan ta dauka muryata cike da mayen bacci ta gaishesa ya amsa yana cewa “my princess me kike ne ?tayi narai narai da idanunta tana sauke masa numfashinta akunnensa ya sauke numfashi “bacci kikeyi ne ?
Tace “eh! Okay tashi kije kiyi wanka kici abinci idan kin gama ki min flash ya katse kiran a lokacin da itama ta mike ta shiga bathroom.”

Karfe biyar daidai jaguwa ya farka daga baccinsa ya sauko daga kan gado yana mika sannan ya janyo towel ya shiga bayi wanka yayi hade da dauro alwala ya fito yana goge jikinsa da karamin towel yana tsaye ana’s ya shigo fushi ne sosai cike da zuciyarsa da fuskarshi ganin zai saka kaya yasa ya fice ya bashi guri ya koma parlors bai jima da zama ba sky ya dawo yayi knowking ya bashi umarnin shigowa izinin shigowa anas ya bashi , sky ya shigo cikin parlour hannunsa rike da ledodi cike da girmamawa ya rusuna yana kokarin ajiye ledodi .
Anas ya yunkura anas yayi yana duba ledodin “ya baka ajiyewa su kamil nasu ba ko sun fita ne ?no suna anan falo ,okay ka dauki nasu ka wuce dashi sky cike da girmamawa ya dauki leda uku ya fita shi kuma ya dauki nasu ledodi Ya nufi bedroom din jaguwa kallo daya yayi masa ya dauke kansa yana taje sumar kanshi da cum a zuciyarsa yana mai jin haushi tanwer yana gamawa ya nufi hanyar fita anas ya biyosa yana kiran sunansa “adnan ga abinci fa ,bana ci ya fada a takaice yana cigaba da tafiya
bai tsaya akoina ba sai falonsa “haba muradin tanwer karmuyi haka da kai please jaguwa ya zauna akan kujera ya a wurga masa harara “allah ya tsareni da wannan useless girl din “uhmmm banaso karka sake kiranta da useless dan baita bace idan ita useless ce kai fa me zaa kiraka dashi ?tsayawa yayi yana kallonsa a hankali ya sauke numfashi anas
ya bude ledar abinci ya fito da takeaway ya tura masa abinci gabansa “kaci abinci !”.

ya lumshe rikitattun idanuntmsa saboda yunwa da fushi,amman bai tunanin bacin ran da yake ciki zai barshi yaci wani abinci “dan girman anas ka dauke abincin nan a gabana abinda nafi bukata daga gareta yanzu shine dariya shi kawai nake son gani a kwance a fuskarka domin na tabbatar da na haukace gbdy “Kayi hakuri dan girman allah da darajan iyayenka ka sanyawa zuciyarka natsuwa kaci wani abu yayi maganr in a serious way “idan baka ci abincin nan ba wallahi yau babu inda zani anan zan kwana na bar hally ita kadai ya karasa maganar Kmr zaiyi kuka .”
Jin abinda yace kuma yasan zai aikata akansa dan haka ahankali ya soma dibar abincin yana kaiwa bakinsa,sai idan duk lomar da zai yi sai tanwer ta fado masa a rai hade da bugun zuciya sai kuma ya dade bai sake kai abinci bakinsa ba daman kuma haka yanayin cin abinsa yake baya sauri “.
shiru anas yayi yana kallonsa har sanda ya ajiye spoon ya mika masa ruwa ya kallesa “amman kai bakaci abincin ba mo me yasa?zanci nafi son naga kasamu natsuwa “yadda anas ya takuresa yaci haka shima yasashi yaci anas yaso yayi masa maganar tanwer amman dai yayi tunanin ya bari zuwa gobe ko anjima anas na gamawa suka mike atare jaguwa ya karasa ya kwashi wayoyinsa suka fito ya na gaba anas biye dashi har zuwa falo inda su jubi suke .”

Ya tsaya ya jingina jikinsa da bangon falon yanayin tsayuwarsa ya fahimtar dasu jubi magana zai yi mai mahimanci dan hk suka tsura masa idanunsu tattare da hankalinsu suna jira daga garesa wanda adaidai wannan lokacin tuni anas ya fita kiran sauran yaran kusan atare suka shigo falon jaguwa ya kallesu daya byn daya sannan ya fara magana a tsanake “aiki né kamar koda yaushe ga sambo sama’ila ,sai dai bazamu samu damar zuwa ba zan tura ka scorpion jibi yayi mgnr yana dubansa sannan yayi taku uku ya karasa inda system dinsa yake ya zauna tare da kunnawa “zan tura maka address din inda zaka samesa acikin apapa oil and gas alhj madu gwani
shi kadai ne acikin apapa bashi da na biyunsa mutumin maiduguri ne baki ne dogo mai jiki zan tura maka hotonsa da komai nashi tru what’s app dinka kayi aiki da baseera ,akwai hanyoyi masu sauki da zaka fita koda wata matsala zata faru bama fata yana masa bayani yana kallon system dinsa yana operating tunanin tanwer na zuwan masa.”

shiru yayi yana kokari ture tunaninta daga zuciyarsa amman ya kasa daga karshe dai ya tabbatarwa da kansa bazai iya raba zuciyarsa da tunaninta ba ya janyo system a gabansa ya cigaba da aikin tunaninta hakan ya fahimtar dasu ya gama bayaninsa daya byn daya suka kama gabansu ,”anas ya matso kusa dashi yana mika masa hannu “zan wuce gida dan allah ka kara hakuri adnan rayuwar nan ma guda nawa take ?ina son zuciyarka ta koyi yadda ake yafiya da sauri .
ko gezau bai yi ba bare ya dago ya kallesa ko ya mika masa hannu Kmr yadda ya mika masa “ka yafe min idan na bata maka rai banason kana fushi dani dan sai naji duniyar duk ta Isheni wannan maganar tasa yasa jaguwa ya dan sauko da idanunshi ya dubesa yana dan sakar masa fuska ,dan allah ka saki fuskar nan taka “shikenan nayi “yayi mgn yana murmushin gefen baki “to ko kai fa wallahi har raina yayi sanyi gobe zan kai hally gurin ammi wata killa bazan samu shigowa da wuri ba ya gyada masa kai kawai alamun yaji suka yi sallama ya kama hanyar zuwa gida .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button