KUSKUREN BAYA 1 TO 48

????️39
……Tunda ta fara magana yake kallon bakinta yana jin wani irin zallar’bacin rai mai tsanani ,dan idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa bai wuce yaga ana shiga rayuwar jaguwa ba ko ai bantashi , bai sake ce mata komai ba har sanda ta gama magnrta , sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci fuskarsa ta canza daga farinciki da yake ciki zuwa bakinciki ,tayi shiru ta zuba masa idanunta tana kallon fuskarsa da sam babu annuri kwance akai
a hankali ya dauke kansa daga kallonta .”
cigaba da kallonsa tayi tana jiran taji mai zai ce mata ,ganin yayi shiru yaki cewa komai yasa
ta gyara tsayuwarta tace “da fatan zaka fada masa sakona?.”bai kalleta ba ya furta “a’a bazan fada masa wannan sakon ba amman idan ke kinji zaki iya to Ki samesa da kanki ki fad’a masa watakilla ma zai fi fahimtarki akaina “. yana gama fadar haka bai tsaya jiran me zata sake cewa ba ya juya a natse ya nufi get din gidan, bayansa tabi da kallo yana taku a hankali shima kamar adnan din yake ta fada a kasan ranta ,komai nashi mai kyau da tsari to ya ma za’ayi abokansa ba zasu kasance kamarsa ba ?.”Jiki a sanyaye ta juya ta nufi cikin gidan tana nazarin yanayin daya shiga a lokacin da take masa magana akan adnan “kamar bai ji dadin maganarta ba ?tayiwa kanta tambayar ,tabe labbabta tayi tana cewa “kar allah yasa kaji babu dadi aranka tunda zaginsa nayi da zaka wani ‘bata rai taja tsaki tare da shigewa ciki .”
Ahankali anas ya bud’e motarsa ya shiga ya zauna da kamar ya kira hally ta fito suyi sallama sai ya fasa ya kira layin ta yana kokarin yiwa motar key har ya bar unguwar suna waya tana zuba masa shagwaba lokaci daya yaji ta yaye masa dukkanin damuwarsa ,bai tsaya akoina ba sai a kofar gidan jaguwa yayi hon mai gadi ya taso ya bude karamin hujin get, ganin shine ya soma kokarin bude masa babban get ya sanyo hancin motarsa cikin haraban gidan mai gadi na daga masa hannu ,ya karasa inda yake parking din motarsa yayi parking ya kashe motar ya fito yana gyara zaman rigarsa adaidai lokacin da mai gadi ya gama rufe get ya karaso gurinsa cike da girmamawa har zai rusuna masa Ana’s yayi saurin dakatar dashi yana cewa “haba baba sau nawa zance maka ka daina duka min ? ai ko baka haifeni ba kayi kani kusan na biyar dani please ka daina bana so ,ya fda yana mika masa hannusa ,gaishesa mai gadi yayi yana murmushin jin dadi dan ba yau bane karo na farko da anas din ke hanashi rusuna masa sabanin sauran ya amsa masa gaisuwar a mutunce kamar koda yaushe sannan ya nufi ciki gida yana shafa sumar kanshi ,binsa mai gadi yayi da kallo gabadaya rayuwarsa ta sake sauyawa ,kamala da natsuwa sun samu kyakkyawan zama ajikinsa har wata yar kiba yayi ta kwanciyar hankali .”
Zaune ya iske jaguwa zaune akan kujera a parlour ya daura kafafunsa saman table jikinsa sanye da jajayen kaya wando da riga yana operating laptop , cup din coffee na daga gefen laptop dinsa ,yayinda jabir ,
kamil da jubi suke zaune suna kallon wani film din soyayya mai suna kuchi kuchi hotahe, sai faman murmushi suke ,sallamrsa ce ta dawo da hankalinsu bakin kofar shigowa har shi jaguwa sai daya dago kanshi a natse daga kallon laptop da yake ya maida idanunshi kan anas dake tsaye yana dubansu alokacin murmushin farinciki bayyane akan fuskarsa yace “da dai kunje kunyi aure da wannan kallon da kukeyi ,a aure ne kawai zakuji gardin soyayyar gaskiya ba irin wannan na film ba wanda nishadi kawai zai dinga saka ku .” ya karasa maganarsa yana mikawa jubi dake kusa dashi hannu domin su gaisa still fuskarsa dauke da murmushin tsokana .”
jubi ya hade hannuwansu guri daya ya tsarke sosai yana cewa “kai ma ba wayonka ne ya baka auren ba , taimaka maka akayi aka baka ko kuma nace shishigi da nemana gindi zama da kutse acikin arayuwar wasu yasa akabaka aure if not da haka zaka mutu babu aure dan babu wacce zata aureka da irin rayuwar da kake ,ko ka manta kai din dan giya ne ? sannan kuma mane min mata ?.”
“Idan ka manta na tuna maka wane ne kai ,mu ka barmu a yadda muke din nan yafiye mana dadi da wata rayuwar aure can wanda babu komai acikinsa sai takura ,wani dadi kake ji a aure da mu bama ji ?.” ya tambayesa yana kafesa da jajayen idanunshi
“kwana kake da mace muma idan muna bukatar kwana da mace zamuyi ko ba haka ?”saurin maida idanu jaguwa yayi akan jubi wanda ke maganarsa hankali kwance yana duban sauran abokansu babu wata shakka ko fargaba daya nuna a fuskarsa .”
jubi ya cigaba da magana a zafafe “shasha yana da kyau ka dinga iya bakinka akan komai dan zakewarka tana dada yawa idan ba haka ba zaka tsinci kanka cikin nadama .”ya saki hannunsa ya fusace ya maida idanunshi kan kallon da yake wanda hakan yasa sauran basu samu damar furta abinda ke cikin ransu ba dan duk abinda suke son fad’a jubi ya rigada ya fad’a masa hakan kuma ya wanke zuciyarsu.”
hakan nan maganar jubi ta caki zuciyar jaguwa sosai har ya kasa dauke idanusnhi akansa bare ya cigaba da aikin da yake sai daya maimata maganar jubi kusan so uku acikin ransa kafin ya dauke idanusnhi ya kalli anas da yake tsaye kikam yana kallonsu jiki a sanyaye ,a kallon da yake masa ya fahimci jikinsa da kafafunsa rawa suke ,shi kansa cikin tsananin kaduwa da bugawar zuciya yake cigaba da kallonsa yayi sam bai ji dadin kalaman jubi garesa ba haka zalika yasan anas din ma bai ji dadi ba dan gabadaya yanayinsa ya sauya amman yasan babu matakin da zai dauka ,nemo jarumta Ana’s yayi ya sanyawa jikinsa.”
“Friend !”.
Ana’s ya kira jaguwa a natse yana sakar masa murmushin dole dan da zaa bude zuciyarsa bakinkirin zaa gani tsabar bacin rai ,jaguwa bai
amsa ba illa kallonsa da ya cigaba da yi ,shi kuma ya samu guri ya zauna a kusa dashi yana basarwa tamkar maganar jubi bata ta’bashi ba a kallon da yakewa jaguwa ya Karanci damuwarsa ,hargaginsa yake gani tamkar daminsa daya ga abinsa kuma yake shirin rasashi domin nuna masa bai ji haushi ya ba ya maida hankalinsa gasu jubi yace “kuyi hakuri frindes ban san maganata zata bata maku rai ba da banyi ba amman ni da wasa nake muku tunda nasan komai yana da lokaci shi aure kamar mutuwa ne idan ..” dan allah malam ka rufe mana baki kasani mana “. Kamil ya katseshi yana zaro masa ido kamar zai cinyesa tare da jan tsaki ,anas ya dan kallesu a firgice zuciyarsa na buguwa da karfi “.
“Tunda kayi aure ka karo sabon wulakanci akan wanda kake yi ,sai wasu abubuwa kake yi kamr akanka aka fara aure ko zinariya ka aura iyakcin abinda zakayi kenan bare ba zinariya bace mutun ce dai kamar kowa da zaka wani damu mutane .”
tsam jaguwa ya tashi daga shi har laptop da coffee dinsa ya soma tafiya tun kafin zuciyarsa ta tarwatse dan bazai dauki wannan rashin mutuncin akan jininsa ba ,idan kuma yace zai cigaba da zama to lallai zasaka bakinsa kuma hakan zai sa su yi korafi akan yayi side din anas ,shima Ana’s ya tashi tsam ya biyosa zuciyarsa ta tafarfasa sai dai yana ta kokarin tausarta.”
kusa atare suka shiga dakin jaguwa ya samu guri ya zauna a kujerar falonsa qirjinsa na zafi da ciwo shima Ana’s ya zauna a gefensa ,jaguwa bai kalli inda yake ba haka zalika bai ce masa komai ba dan bakaramin haushi ya bashi shi kansa anas ya fahimci haka dan haka ya motsa bakinsa “kayi hakuri ya fad’a yana kallonsa cikin tsananin damuwa .”
Jaguwa ya dan ciza lip’s dinsa na kasa da karfi “me yasa Ana’s ?”
“Me yasa kake yin abinda banaso ?”Am so sorry adnan bazan sake ba kuskure ne ya fad’a jiki a sanyaye yana gyara zamansa yana qawalo murmushin dole “tunda sun nuna basa son kana shige musu me yasa bazaka hakura ba ? .”
“Ko dole sai ka tsokanesu? shiru anas yayi yana dubansa “.ya kamata zuwa yanzu ka san yadda zaka dinga yin muamula dasu tunda sun nuna basa son kana masu irin wadan nan zantuttuka na tsokana please ka daina .” murmushi stil anas ya sake yi yana cewa “shikenan an daina inshaallahu “kai fa baka daukar tsanar da suke maka a kwanakin da mahimanci ,ni kuma na dauke shi da mahimancin daya zarta tunanin jama’a ,a nawa tunanin ma gani nake sun tsaneka ne tsana mai muni amman dai nasan yadda zanyi da…… “.