KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Kallonta yayi cike da jin  wani irin matsanancin damuwa, tunda yake a rayuwarsa basu tab’a fuskantar irin wannan tashin hankalin ba , wayarsa ce ta soma sowa alamun kira ya shigo, jikinsa na rawa haka hannunsa ya tashi daga gefen gadon ya tura hannu ya shiga laluben wayarsa, lokaci guda ya ciro yasa ta a kunne. “Waalkassalam”ya fada da alama daga can bangaren an mai sallama.
“Owk gani nan gangarowa k’asa yanzu” Yana fad’a ya kashe wayar ya maida cikin aljihu. “Anganta?!”hajiya zainab  ta mai tambayar tare da d’ago idannunta wadanda sukai rau-rau kamar na wacce ta jima tana jinya.
Wannan shine iya abunda take iya fad’a tun a lokacin da aka fita da Tanweer bata iya cewa kowa komai, haka duk wanda yazo jaje ‘yan uwa da abokan arziki bata iya saurarsu  kusan ma  bata gane mutane saboda tsananin tashin hankali da take ciki.

Girgiza mata Kai yayi alamun a’a  “Ki jira naje na  dawo Insha Allahu za’a ganta zainab, amma dan Allah ki daure kisa wani abu a cikin ki  plz”ya karashe maganar cikin rarrashi yana kallon kwayar idonta.

   Dauke idannunta tayi  wad’an da suka cika taf da ruwan  hawaye. “Dan Allah kutaimaka ku dawo mun da ‘yata Tanweer, please ka taimaka mun dan Allah Alhaji nasan ba abunda yafi k’arfinka kune governatin na…”.
“Shhhhh! Nace kiyi shiru za’a ganta ki kara hakuri yanzu kiyi ko’kari kici abincin da’aka kawo  kan ya huce plz, I will be back soon”. Yana rufe baki ya fice yana k’ada Kai cike da takaicin abunda yake faruwa dasu.
Bin kulolin da Salamatu ta shigo ta ajiye mata d’azu na abinci tayi, tana Jin yunwar sai dai bazata iya ciba a yanzu inba ganin tillon ‘yar’ta tayi ba.

Suna zaune a babban falon Alh.Abubakar ya shiga da sauri wanda hakan yasa dukkansu tashi ciki hanzari, k’arasawa yayi inda suke tsaye cikin hanzari ya soma mika musu hannu  cikin sauri suke gaisuwa  fuskarshi ba yabo babu fallasa ya koma ya zauna tare da musu alamu da hannunsa da su zauna.
“Tuntuni nake sa idon ganin ku Inspector ina fatan  ansama wani information kan yarinyar nan?”. Yayi tambayar yana kallon Inspector hassan wanda kansa ke kallon k’asa batare da ya dago yace komai ba.
Ganin haka yasa Alh.Abubakar dan tsuke fuska tare da gyara zamansa kamar zai tashi , ya cigaba da fad’in. “Lafiya Inspector naga kunyi shiru dukkanku don’t tell me ba wani improvement”ya k’arasa maganar fuskarsa cike da damuwa q’irjinsa na wani irin bugu kamar zai fita ba k’aramun dauriya yake ba yana jin rad’ad’in rashin tilon ‘yar tasa, tabbas ya fahimci shirun nasu ba alkairi bane d’an runtse idannunsa yayi inda ya soma tsinkayar maganar Inspector.

“I am very sorry sir, gabad’aya investigation d’inmu  ya  nuna an bugar da wasu daga cikin ma’aikatan  dake aiki a cikin gidan  kafin a samu nasarar  shigowa gashi duk wata na’ura da CCTV Footage an datse kamar yadda muka sheida maka a tun farko da…”.

“Dakata Inspector! Ni damuwa ta a yanzu ‘yata dan haka ina rok’onku dan Allah ku hanzarta nemo min yarinyata kafin su cutar min daita, How comes za’ace ansace ‘yata tilo a wannan k’asar da nake da babban matsayi? ya zama dole a binciko   ta  cikin kankanin lokaci, taya muna  ba da tsaro ga al’umma  ace gunmu da iyalanmu  babu?” Alh. Abubakar ke jero wad’an nan tambayoyi wad’anda kana  saurara  zaka fahimci  ‘bacin  rai da damuwa  a   tattare  dashi  , Inspector  kansa shi da  SP sun tsorata da yanayinsa, d’ago jajayen idannunsa yayi wad’anda da ba ja bane amma yanzu sun rikid’e zuwa ja ya kallesu.
“Zan k’ara baka second chance wajen nemo mun farin cikina, zan kira minister da commissioner of police na sanar dasu if you fail this time I will make sure to disqualify you from all duties dan hakan zai nuna baka iya aikin ka ba sam”ya karasa maganar lokacin daya tashi.

“Insha Allahu we will do our best bazan taba kasa yin aikina ba ka…”.
“Inspector kuje kawai, banson jin promises just fulfill your duties kawai, As you all know bazan iya rayuwa ba muddin wani abu ya sameta I need to act quickly yarinyata karamace tayi kankanta da kasancewa a hannun waɗan mutanen, she can’t be around such people I won’t let her stay long in there Insha Allahu goodbye and good luck for  all Inspector”. Yana gama  fad’in haka bai sauraresu ba ya sa kai ya barsu .

Kallon  juna  su kai cike da damuwa “muje” Inspector ya musu magana suka wuce dukansu ukun cikin hanzari Ko drink din da lokacin aka shigo musu dashi basu iya tsayawa sun sha ba .

“I.B why?”.
Nazifi yayi tambayar yana kallon Ibrahim wanda yake cike da matsanancin damuwa duk   jikinsa yayi zafi rau saboda zazzabi , tunda aka d’auke Tanweer yake kwance yana fama da zazzabi sosai.
“Amma kasan abunda kake ma kanka ba zaisa aga yarinyar nan bako?”. Ya Kuma fad’a yana kallon Ibarahim wanda idonsa ke runtse wasu hawaye masu d’umi ke faman bin k’uncin sa yana tsananin son Tanweer.
“I thought you are strong police officer but a yanzu ganin yanayin ka got me thinking otherwise why? Abune da yakamata ace ka bishi da k’arfin ka like a real man haunt them like lion that you are but…ya Rabbi”. Ya fada tare da kad’a kansa.

Shigowar Mahaifiyarsa Haj.bassera ne ya katse Nazifi dake zaune gefensa da Kayan gwaje-gawajensa na hospital kasancewarsa likita kwarare. “Yaci abincin kuwa?”. Ta tambaya lokacin data k’arasa shigowa idonta na kan Ibrahim.
Gigirza mata kai Nazifi yayi. “A’a Umma har yanzu dai yaki infact yaki mun magana tunda na shigo”. Cike da damuwa ummansa ta  girgiza kanta
“Haka yake ae tunda abun nan ya faru yak’i magana yaki cin abinci gaba daya, lamarin dai sai addu’a kawai” ta k’arasa maganar lokacin data kai hannunta jikinsa runtse ido yayi, yanzu ba zafi jikin normal sai dai damuwar ta abincin. “Umma Ki cigaba da bashi abincin may be zai ci, ni zan koma gun aiki”. Ya fada lokacin da yake had’a shirginsa.

“Owk a dawo Lafiya Allah Ubangiji ya tsare”. Ta fada tare da mai murmushi.
“Ameen Umma bye”. Ya fada lokacin daya dau suitcase din nashi ya fita ya barta zaune tana cigaba da k’okarin yadda  Ibrahim zai yarda yaci abinci tare da kwantar masa da hankali .
Yana fita babban falo ya tunkara jin muryar Abban Ibrahim a falon da alama waya yake, da sallama ya shiga cikin falon. Kallonsa Alh.Tahir yayi tare da saurin magana. ” can I call you later?”. Ya fada cikin sauri tare da ajiye wayar yana kallon Nazifi.
“Abb…”.
“Muje muje waje Nazifi we need to talk “. Alh.Tahir Ya fada lokacin da yayi gaba nazifi na binsa a baya cike da matsanancin damuwa. “Yauwa a nan zamu iya magana”. Alh.Tahir yayi maganar yana kallon fuskar nazifi wacce ke nuna damuwa.
“Haba Nazifi, Me yasa kake damun kanka bayan na fad’a maka so nake kawai ka keeping dinshi na d’an day’s har na samu abunda nake kallo ya yu…”. “Amma Abba me kake nema wanda zaisa kasa nayi ta kashe ma Ibrahim jiki da samai zazzabi haka bayan kafi kowa sanin yanzu ne yake buk’atar jarumtarsa wajen nemo Tan….”.
“Dakata Nazifi!”. Alh. Tahir ya fad’a cikin b’acin rai tare da d’aga mishi hannu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button