KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Kai haba dai kai kuwa karka yi wani tunanin dabam akansu nifa bana ganin laifinsu ko kadan sai namu,duk kai ne ka jawo komai daga lokacin da’aka boye musu maganr aurena na fahimci basu ji dadi hakan ba shima dalilin sauyawarsu gbdy ,kuma ko ni ne haka zanji  babu dadi araina.”
”  duk da haka bai kamata idan ma haka ne ai bai kamata su rike abun  acikin zuciyarsu har haka ba .”lumshe ido anas yayi “babu komai zan sake basu hakuri kai ma ka basu hakuri mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba babu jin haushin juna babu kyashi ko hassada a junanmu sannan ya dauko wayar jaguwa dake ringing ya mika masa sunan da ya gani ne yasa ya ajiye wayar ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa yana kurba a hankali.”
kallon mamaki  Ana’s ya zuba masa sannan ya dauki wayar yana duba screen din wayar  nan yaga sunan tanwer yana yawo ya waiga ya kalli jaguwa  “ban fahimci kin daukar wayarta da kayi ba?  batare daya kallesa ba yace “bashi da amfani ne shiyasa  naki dauka “ya kamata kayi hakuri adnan haka ,komai na rayuwa fa mai wucewa ne wallahi this duniya is noting adnan yau idan mune gobe bamu bane yarinyar nan tayi nadama dan allah ka yafe mata tana sonka dayawa bazata iya rabuwa da kai ba yana da kyau kasan darajan soyayya me ye laifin wanda ke sonka ?.

“Babu !.
Ya bashi amsa atakaice “to why adnan kaima fa baka kyauta mata ba ,dan bai dace abinda kayi mata a gaban mutane ba ,kamata rashin mutunci a gaban saurayin da bata so sannan ka hadata da kalmar useless ai kowa ma kayi haka zai iya haukace maka .”jaguwa ya saki wani murmushi da ajiyar zuciya atare yana shafa gefen fuskarsa ko yanzu fuskarta ke masa yawo acikin kwakwa luwarsa ,ita kadai ce ta samu wannan matsayin acikin arayuwarsa, dan bai iya mantata duk abinda yake tana nan makale a ransa tana yawo a jinin jikinsa  tun yana mamakin matsayin da take dashi a zuciyarsa har ya zo ya daina.”
Sai daya numfasa kana ya motsa lip’s dinsa “kenan ta kiraka ta fada maka na kirata da useless?”.sosai kuwa dan abun ya dame ta matuka tana min bayani tana kuka “idan har ta fada maka daidai a maganata babu inda nace mata useless ,i said that who is doing that they will be thinking that is useless that’s ol ,duk da haka dai bai dace ka fadi haka ba ,a natse Ana’s ya dinga rarrashinsa yana bashi hakuri ya yafewa tanwer sannan ya amince da soyayyarta shi kuwa sai murmushi yake yake wa anas yana jijiga kafarsa daya .”

Ana’s ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa “ka hakura ta kiranka komai ya wuce ?”Kira kuma na  sau nawa ai tun jiya take kirana ban dauka ba dan banga amfanin kiran ba bare na dauka ,dazu da safe ma naga shigowar sakonta ya karbi wayarsa yana nuna masa sakonta ,”Assalamu alaikum ,Good morning how are you doing my love”how was your night ? hope you had a great night?let us thank allah for the gift of another day and please forgive me and forget what I did to you  ” girgiza kai kawai anas yayi yana cewa “kai  dai anyi mugu mai taurin zuciya ,
yanzu kai bakajin tausayin yarinyar nan ?ya girgiza kai batare daya kallesa ba .
“Kaga kuwa ni ina jin tausayinta wallahi har hawaye nake zubar mata dan tana mutuwar sonka ,kaso mai sonka adnan ka tausaya mai sonka ko da yake ai kana sonta soyayyarta ma ta musamman ce a zuciyarka ya fada ta tsigar tsoka , jaguwa ya waigo ya kallesa a natse sai dai bai ce masa komai ba hakan kuma ya nuna bazai ce din ba “allah dai ya shiryeka sarkin zuciya da taurin kai jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa ,bari  naje na sake bawa friend’s hakuri magana ta wuce banason ina tare da mutane naga na bata musu rai “jaguwa yace “sauka lafiya aminin kirki .”anas ya mike ya fita daga dakin shi kuma ya cigaba da aikinsa yana murmushi yana tuna tanwer “.

Suna zaune har lokacin a falon ya samu guri ya zauna yana fuskantarsu sunga shigowarsa da zamansa amman sukai masa banza tamkar basu san da zaman mutun agurin ba ya gyara zamansa ya kirasu “friends!” amman babu wanda ya juyo daga cikinsu ya kallesa bare yasa rai zasu amsa masa “please kuyi hakuri idan akwai wani laifi da nayi muku yasa kuka tsaneni yanzu ,ni dan adam ne ta yiwu nayi muku Kuskuren bisa rashin sani amman ni atunanina idan nayiwa daya daga cikinku laifi kamata yayi ku kirani ya fad’a min domin in gyara kuskurena ,dan idan ni ne bazan rikeku araina ba zan fada muku komai ya wuce mu cigaba da rayuwarmu cikin soyayya da walwala ,dan allah kuyi hakuri ku yafe min .”

shiru falon yayi babu wanda yace masa uffan ya mike daga inda yake zaune ya karaso ya zauna akan table din dake tsakiyar dakin ya riko hannun jubi domin a komai shi ke fara daukar zafi “kayi hakuri abokina duk da wallahi ban san nayi muku laifi  ba  amman ita rayuwa haka take wani abu Kalilan zai iya kawo fitinar da zai shiga tsakaninka da kowa ya fad’a yana kallonsu daya bayan daya a tare suka sakar masa murmushi wanda da gani na yake ne “karka damu komai ya wuce inji cewar jubi “na gode Kwarai da gaske amman dan allah me nayi maku ?ina son sanin abinda nayi muku saboda na kiyaye dan gaba “me ye amfanin aita tada magana anas bashi da wani amfani allah dai ya yafemu gbdy jubi na rufe baki anas ya mike ya juya yana masu godiya sai ganin jaguwa yayi tsaye ya rungume duk hannunwansa a qirjinsa fuskarsa da alamun annurin farinciki dan yaji dadi kwarai da suka fahimcesa .”
“Ya ka tsaya ka karaso ka zauna ka karasa bayyana murmushin farinciki dake ranka?inji cewar kamil .
jubi yace “ai dole kaga farinciki a fuskarsa tunda anas ne bakaga dazu fushi yayi ya tashi ya bar gurin saboda an taba zuciyarsa ba ,” ya karasa maganar yana fakar idanun jaguwa ya zabgawa anas harara dan shi hakurin dole yayi da yafiyar dole saboda ganin tsayuwar jaguwa daya gani ,kuma idan suna son cima burinsu akan anas lallai sai sunbi komai a hankali.”

“ai dole na tashi na bar maku guri tunda naga abun naku har da wulakanci so kuke ku tarwatsa min zuciya, ga ciwa aminina mutunci ga tabo jinina ai abun yayi min yawa suka sa dariya gbdynsu  a hankali ya cigaba da mgn yana takowa ya tsaya a tsakiyar falon “rayuwarmu a tun farko a tsare take babu wanda ke jin haushin wani hakan kuma yana min dadi ,wannan yace ayi kaza wannan yace ayi wannnan kuma duk muna bin tsarin juna babu mutsu ko jayya a yanzu ma yana da kyau mu cigaba a yadda muka dauko dan babu cin amana a tsakaninmu .”
“ban hana kowa aure acikinku ba ,wallahi duk wanda yake bukatar aure acikinku ya nemo mata zan tsaya masa da iyakacin karfina na taimakeku
sai dai idan abun ya gagareni idan kuma hakan ta kasance zan shigo da wasu ciki ayi komai cikin sauki da nasara .”

Yayi shiru yana kallonsu daya bayan daya yana nazarinsu alhamdulillah ya fahimci duk sun sauko daga mummunar fushin da suka jubi ya kallesa yana murmushi wanda bai kai har cikin zuciyarsa ba sannan bai jin zai canza daga idar da nufin sa,wani irin zafi yake ji acikin zuciyarsa “tunda ya basu damar aure yace mahaifiyarsa ta haifo masu mata kamar yadda ta haifawa Ana’s wannan shine maganar dake kwance akan harshensa sai dai yasan matsawar yayi ganganci ta fito daga bakinsa allah ne kadai yasan maseefun dazasu faru .”
A natse jaguwa ya dinga jansu da hira yana bawa kansu shawarar har suka shigo da wata hirar cikin nishadi kowannensu na tofa albarkacin bakinsa shi dai anas yanata taka tsantsan da abinda zai fada dan hararar da suke fakar idanun jaguwa suna masa ya tsaya masa arai sallah ne kawai ke ta dasu har biyar tayi anas ya mike alamun zai wuce jaguwa ya kallesa “har zaka wuce ?ya gyada masa kai zanje na dauko hallay a gidan ammi mu wuce gida ,okay gobe ka shigo da wuri saboda fitar sconpio ya gyada kai sannan yayi musu sallama .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button