KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Karfe shida daidai a kofar gidan ammi tayi ma anas ya shigo a natse ya gaishe da ammi ,hally tana ganinsa ta mike tsam ta soma shirin tafiya ta dauki bakar ledar da ammi ta bata wanda yake cike da kayan sawa wanda ta dinka masu ita da shafiq sai wata leda dake dauke da magungun Kara ni!ima sukayi mata sallama hasera har bakin mota ta
rakasu suka shiga mota suka kama hanyar zuwa gida da zarar yaga tayi shiru zai tsokanota ita kuwa kewar amminta take dan ji tayi kamar karta koma gidanta ta cigaba da zama tare da amminta.
Ana’s yayita kokarin kawar mata da tunaninta da hirar soyayyarsa mai cike da zolayar da ban dariya wanda yayi nasarar share dukkanin wata damuwar anas .
Suna shiga gida ta shiga gida dakinta ta ajiye kayan data zo dasu sannan ta cire mayafinta ta fito ta shiga kitchen ya biyo bayanta ya rike kugunta yana cewa “kada ki daura komai ki hutawarki zanyi mana order abinci hakan daya fad’a yasa ta ajiye abun kunna gas ta biyosa suka fito daga kitchen yana manne daita “sannu duk kin gaji ko?”.
“Babu wani gajiya ina dai son hutawa ne .”yayi murmushi “ai gani indai hutawa kike son yi sai muyi tare ai zaki fi jin dadi yayi mgnr tana daura gabarsa a wuyanta ta hararesa tana cewa “kai ko”.
“Ni ko me ? kodan na fiyye sonki dayawa haka allah yayi ni ni mai son hally ne kuma hakan abun alfahari ne agurina ta dan yi murmushi ya zareta ajikinsa ya fita bai shigo ba sai byn sallahr ishai wannan shine kaidarsa tunda ta tare a gidan baya shigowa sai yayi ishai ,a fadarsa tace mata ana karatu a masalacin dan haka yake zama har a idar da ishai sannan ya shigo, sai byn takwas da rabi ya shigo masu da lafiyayyen abinci byn sun ci suka makale juna suna kallo wannan daren ma sun more junansu cikin tsabanin so da kulawa .”
washegari bai tashi da wuri ba saboda gajiyar sex sai gurin karfe goma ya tashi da wani matsanancin ciwo kai ya dafe goshinsa da hannunsa daya bai tasheta ba ya shiga bayi ya fara sakarwa kanshi ruwa kafin yayi wanka a daddafe ya fito ruwa na kwance a sansar jikinsa still tana kwance cikin bargo tana baccinta hankali kwance ,ya goge jikinsa yana ciza lips dinsa ya shafa lotion ajikinsa yana sake jin yadda kansa ke mugun sara masa wardrobe dinsa ya nufa idanushi na kanta yana kallonta ya shirya cikin kananan kaya ya karaso ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana sauke numfashi a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta yana jin kamar ya cigaba da mata numfashi ta huta .”
bakinsa ya kai daidai idanunta yayi kiss a hankali ta bude idanunta dake cike da bacci dishi dishi take kallonsa wani murmushi ya sakar mata yana dage mata gira “zan fita my princess sai dai wata killa zan dade yau ban dawo gida ba ki kular min da kanki .
Ahankali ta motsa lip’s dinta “a dawo lafiya allah ya tsare min kai ,kai ma ka kular min da kanka please matsota yayi sosai Kmr zai shige jikinta dan baya gajiya daita ,suka dan zubawa juna ido ko kyaftawa basayi ahankali ta maida idanunta ta rufe saboda baccin dake cikinsu shima naunayen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike yana duba time agogon dake daure a hannunsa ya karasa inda ya ajiye wayarsa ya dauka yana kokarin sakata aljihunsa kira ya shigo ya daga “me kake yi ne har yanzu ?”.
Da kyar ya bude baki yace gani nan fitowa yanzu “me ya faru naji muryarka haka jin muryarka ya daga min hankali?”.
Ya nufi kofar fita yana cewa “wallahi da ciwon kai na tashi mai tsanani ban kwanta dashi ba amman na tashi dashi “oh sorry my dear ina hally take ?tana bacci ya fada yana shiga dakinsa ya zuge mirrow dinsa wata karamar kofa ta bayyana ya shiga ya dauki bindiga pestol ya soke ajikinsa “kana jina?
“Eh ina jinka ya bashi amsa yana runtse idanunshi “karka fito kayi zamanka a gida ka huta tunda baka da Lfy idan scopion ya dawo daga aiki zan zo da kaina muje hospital a duba min kai wannan ciwon kan yayi yawa “okay !”
“Ni kaina na fara tunanin ganin likita,okay shikenan
Amman ka bar wayarka a kunne bana son na kira naji akashe anas yace “to! ajiye bindigar yayi ya fito ya maida kofar ya rufe ya dawo falo ya kwanta dafe da goshinsa gurin karfe shabiyu saura hally ta tashi ta fara gyara dakinta sannan ta fito zuwa falo domin ta gyara turus tayi sakamakon ganinsa kwance dafe da goshinsa ,da sauri ta karaso gurinsa ta durkusa agabansa ta riko dayan hannunsa cikin nata tana murzawa wani zafi taji ya ratsata .”
Bude idanunshi yayi da kyar yana kallonta “kace zaka fita kuma zaka jima baka dawo ba ?ya lunshe mata ido “kaina ke ciwo bazan iya fita ba “sannu !.”
Ta fada tana dafe masa goshi “ka sha magani ma kuwa ?ya girgiza mata kai alamun a’a ta mike da sauri ta nufi dakinta tana cewa “me yasa zaka zauna baka sha magani ?.”
Yana kwance ta dawo hannunta rike da magani ta shiga kitchen ta dauko ruwan mara sanyi ta fito ta mika masa magani tana rike da goran ruwan ya amsa ya kai bakinsa ta mika masa ruwa tana masa sannu da kyar ya sha magani dan bai son shan magani sannu tayita jera masa tana jin kamar ta maida ciwon kanta ya tashi ya tafi inda zashi ya koma ya kwanta ita kuma ta cigaba da aikinta .”
Da misalin karfe daya daidai na rana sconpio suka fito tare da jaguwa zuwa haraban gidan suna magana kasa kasa wanda duk nacinka baka isa kajiyo me suke cewa ba ,jaguwa ya dafa kafadansa yana kallon shigar jikinsa , manya kaya ne sanye ajikinsa su bama su haske can ba haka zalika ba masu dotti ba , kansa har da rawani wuyansa zagaye da manyan carbi tamkar dai irin shirin da malaman darika suke kafafunsa rufe cikin black shoe’s ,
yadda kafafunsa suke rufe da bakaken takalmin haka jikinsa suke sanye da bakaken kaya rigarsa ce kawai multcolour amman hatta jeans din jikinsa baki ne gefe da gefen west dinsa na makale da bindigar pestol kai tsaye inda machinan aikinsu suke jere jaguwa ya nufa dashi ya damka masa key yana cewa “ka hau wannan .” ya hau wanda jaguwa ya nuna masa yana kokarin ta dashi yaji ya cigaba da magana “ka kula sosai scorpion banason kuskure a aiki sannan ka kula da abun kunnenka daga yadda yake din nan zan dinga jin komai dake tafiya haka zalika zan dinga ganinka ina maka fatan nasara yana rufe bakinsa scorpion ya nufi get yana tsaye agurin mai gadi ya bude masa karamin get ya fita sannan ya juya ya koma ciki hannuwansa duka goye a bayansa.”
Scorpion na fita cid ya kira headquarters na polisawa kai tsaye aka dauka da “hello ! “kana ina dcp ? Okay to kayi hanzari ku isa address din dana tura maka , yanzu haka yaronsa ya fita kuma shi kadansa kamar yadda na sheida maka naji suna tautaunawa, yana sanye cikin fararen kaya shirin malunta “dan allah karka bari mu rasa wannnan damar at least ko mutun daya muyi nasarar kama wa acikinsu .”
“karka damu zamuyi iyakar kokarin mu sannan ka tabbatar duk abinda ka gani ka daukar mana komai da komai akansa da yaransa a wayarka domin itace hujarmu ,da zarar ya shigo hannu sai mun tona masa asiri a idanun duniya ,shi kuma yaronsa idan ya shigo hannumu yaki bamu damar muyi binkice akan mai gidansa harbesa kawai zanyi mu huta.”
cid na katse kiran dcp ya shiga kiran yaransa daya bayan daya kafin kace me sun hadu a wani daki na musamman nan ya shiga basu umarni daman kuma a shiryensu suke kusan atare suka fito suka shiga motocinsu suka fita yayinda scorpion ya isa inda me gidansa ya aikesa cikin nasara ya samu guri nesa kadan da inda aka aikesa yayi parking bisa umarnin ogansa ya sauka akan mashin din ya soma tafiya a natse tamkar mutumin kirki yana jin jaguwa nace masa “karka kuskura ka waiga bayanka cigaba da tafiya kawai domin waigawarka zai sa polisawa dake aiki agurin suyi suspecting dinka sannnan ka fara neman taimako gurin mutanen dake kai kawo agurin .”