KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bai yi magana ba ya kebe kansa gefe guda ya zaro daya daga cikin carbuna wuyansa ya soma ja yana motsa bakinsa a hankali yana mikawa mutanen dake kai kawo agurin hannunsa ,nan take mutane suka shiga mamaki ganinsa domin dai baa bara a kofar get din maaikatar hasalima korar masu bara ake agurin amman cikin ikon allah sai gashi shi ko kallonsa da tsigar kora babu wanda yayi ,wasu daga cikin mutane suka fara bashi sadaka yayinda wasu ke wucesa suna ganin wani sadaka zasu bashi bayan shi din ba nakkasashe bane kawai malunta ce tayi masa yawa ,wasu ma ko kallosa basayi ba .
wata mata ya hango sanye cikin doguwar rigar after dress yanayinta tsam bahausheciya tana daf da wucesa ya biyota da sauri yana rokonta “dan allah ki taimaka min da abinda zan ci saboda allah rabona da abinci tun jiya “ta tsaya tana kare masa kallo sannan ta dauke kanta tana duba Jakarta dagowa tayi tana yatsina fuska “nayi niyyar baka amman gsky bani da canji dubu daya ne “ta fada tana kokarin wucesa ya biyo da sauri yana cewa “ina da canji ,ban gane kana da canji ba sai kace dole sai na baka sadaka?” dan allah matsa ka bani guri , ku zauna kuna bara duk zuciyarka ta muta , kalleka fa da kafafunka da komai amman ka zauna kana bara ta wucesa shi daman so yake ya samu yayi kusa da office din zai shiga kuma yayi saa ,a qalla ya kusan mintuna talatin tsaye a kusa da office din alhj madu sannan yajiyo sautin muryar jaguwa ta cikin abun kunnesa “ lokaci yayi da zaka shiga.”
tsam scorpion ya soma tafiya ya nufi kofar office din alhj madu ,cikin saa yayi attacking din PA dinsa shi kadai zaune ta hanyar daura masa bakin bindiga yana cire rawanin kamshi yayi cilli dashi yana tmbyrsa alhj madu ,kai tsaye ya nufi office din alhji madu dashi , a daidai wannan lokacin polisawa suka karaso suka raba kansu kashi kashi kamar yadda mai gidansu ya tsara masu.”
Suna shiga office din alhj madu ya dago a matukar firgice yana kallon kofar shigowa dan haka nan yaji faduwar gaba da ana murda handle din kofar ,
gabansa ya cigaba da faduwa tare yin mutuwar zaune akan kujera scorpion ya tura PA cikin bayi ya kulle sannan yayi facing dinsa yana saita kansa da bindiga jikinsa na rawa yace “karka kasheni ka fada min abinda kake bukata zan baka ? “kai ma ai ka rigada kasan abinda ya kawoni ?
“Ba….babu kudi a…..”
“Gasu can ya nuna masa katuwar jakar ghana most go dake ajiye a kasa sakamakon ganin scorpion a gabansa yana gyara bindiga yana mazurai fuskarsa babu alamun wasa ,jikin alhj madu ban da karkarwa babu abinda yake domin baa taba kawo masa hari ba sai yau ,scorpion ya isa ya bude jakar daloli kudi ya gani makil aciki suna kyali,ya maida zip din jakar ya rufe ya cire manya kayan jikinsa da carbuna wuyansa ya watsar ,ainihin kayansa suka bayyana ya fito da bakar hula aljihun wondonsa ya saka, ya dan durkusa ya ciro safar hannu a gefe da gefe safar kafafunsa ya zira a hannuwansa sannan ya dauki jakar kudin ya janyo kofar ya kulle shima acikin office dinsa sannan ya fito ya soma tafiya a natse .”
polisawan da suke zagaye da gurin gbdy a hankalce suke sai dai sam basu ga wani mai irin shigar da cid ya fada musu ba dan haka dcp yayi kokarin afkawa cikin office din alhj madu da sauri à daidai lokacin da scorpion ke kokarin fitowa sukayi karo da juna har abun kunne scorpion ya cire ya fadi kasa kamar gillamar walkiya jaguwa yaga wulgawar wani da bai san ko waye ba sannan ya daina ganin komai dake faruwa ai kuwa hankalinsa yayi matukar tashi ya zabura ya mike tsaye daga zaune da yake a gaban system qirjinsa na bugawa ya rike kugunsa da hannu daya stil idanushi na kallon computer.”
dcp bai tsaya yabi ta kansa ba ya wucesa da sauri yana cewa “so …sorry.” scorpion yayi saurin yin kasa ya dauki abun kunnensa amman kuma bai yi azancin maida shi kunnesa ba ya cigaba da tafiya cikin sauri rike dashi yana tunanin inda ya yasan wannan fuskar da sukayi karo yanzu ,da wannan tunanin ya karasa ficewa ,dcp na gama shiga office din ya soma jiyo sautin muryar alhj madu yana ihun barawo!!!.
Da sauri dcp yace “yana ina sawunsa muka biyo ?”yanzu yanzu ya fita sanye da bakaken kaya hannunsa rike da ghana ..” ai bai tsaya ya gama jin abinda zai fada ba ya juya da sauri dan tuni kwakwaluwarsa ta hasko masa fuskar mutumin da sukayi karo dashi da zai shigo da wani saurin yake tafiya yana kiran layukan yaransa dake da connecting da wayarsa yana kwatanta masu kamanin scorpion da shigar jikinsa .”
Tun daga nesa suka hango tahowarsa “gashi nan babu tantama shine wannan barawon “daya daga cikin polisawa ya fad’a ahankali ,dan haka suka sake shiri domin farmakansa har ya karasa inda ya ajiye mashin dinsa idanunsu na tsaye kyam akansa yayinda dcp ke tahowa ta baya cikin hanzari ,
scorpion ya hau mashin dinsa tare da ajiye ghana most go a gaban mashin dinsa ya manna abun kunnensa ,nan take jaguwa ya sauke naunayen ajiyar zuciya amman kuma sai yaji wani mummunar faduwar gaba sakamakon mutumin daya hango ta bayansa yana kokarin isa inda yake , har scorpion ya kunna mashin dinsa yaga mutumin da sukayi karo dashi ya bayyana a gabansa bai tsaya wata wata ba ya saita kansa da bindiga sannan ya kai dayan hannunsa ya kashe mashin din ya zare key yana dubansa akaskance .”
shima scorpion kallonsa yake a matukar firgice gabansa na faduwa yayinda polisawa suka fara fitowa daya bayan daya daga maboyarsu suka zagayesa take jikinsa ya kama rawa sai lokaci ya gane waye a gabansa dcp ne agabansa ya kalli gabas da yamma sune ta koina babu inda zai gudu dan haka yayi sounder ya sauko daga kan mashin din tun kafin abashi umarni ya daga hannuwansa duka sama wani wawan tsaki jaguwa yaja yana furta “oh scorpion …….”
Wanda hakan ya janyo hankalinsu jabir zuwa garesa da sauri suka mike suka nufi karamin falon da yake suna kiran sunansa ,shima kokarin fitowa yake hannunsa dauke da computer ya fito a bakin kofa sukaci karo “an kama scorpion “what?”
Suka hada baki gurin fadar haka hankalinsu a matukar tashe ,babban falo suka dawo jaguwa ya ajiye computer suna kallon abinda ke faruwa ,
damke hannunwansa cikin juna jaguwa yayi jikinsa na daukar zafi ,yana kallon polisawa suka tasa keyar scorpion zuwa cikin motarsu byn sun saka masa handcuff ,mutun biyu suka sakashi a tsakiyarsu sauran suka zauna a baya tare da jakar kudi .”
Kai kawo jaguwa ya fara acikin falon dafe da goshinsa yana tunanin mafuta kwakwaluwarsa tashiga tunanin mai zurfi “ya ma akayi suka san da fitar scorpion?yayi wa kansa tmby “Kenan har yanzu suna bibiyarsa?a hankali ya juyo jikinsa na zafi ya tsurawa computer idanunshi , hankalinsa a matukar tashe yake kallon bakin scorpion dake motsi a hankali , sosai ya matso yana son ya fahimci abinda yake fad’a ai kuwa take ya fahimta “boss karka barni haka shine kawai abinda yake fad’a yana sake maimaitawa kana kallonsa kasan yana cikin firgici mai tattare da tashin hankali,”
“Bazan barka ba scorpion duk yadda zan fitar da kai zanyi koda kuwa zan rasa komai nawa da rayuwata né amman zan fito da kai ,yana kallonsa ya lumshe idanunshi alamun ya gamsu da maganarsa,cikin kankanin lokaci suka isa headquarters dashi scorpion ya fito daga cikin mota zuciyarsa cike da kwarin gwiwa,haka suma polisawa suka firfito fuskokinsu kwance da nasara kamo daya daga cikin yaran jaguwa aka nufi wani bangare da scorpion aka ajiyesa wasu polisawa guda biyu suka fara seaching dinsa suka rabashi da wayarsa da bindigarsa da abun kunne wanda hakan ne yasa jaguwa ya daina ganin halin da yake ciki ,yaja tsaki yana kiran aikin banza kawai “.