KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“uhm bai zo ba “.
stil jaguwa cigaba da kallon bakin mai gadi yayi yana hura hanci batare da yace komai ba so yake ya gano wani abu atattare da mai gadi Kuma ya gano dan haka ya juya cikin tsananin fushi da zuciya ya soma daga kakafunsa bai yi magana ba sai daya shiga cikin dakinsa “wannan tsohon na fara tantama akansa.” anas ya fuskancesa sosai “kamar ya ka fara tantama akanshi ?”wannan tsohon fa bazai yi haka ba , zai yi Ana’s yanzu nan fa ka gama cewa mutane sun zama abun tsoro cin amana ne qarara ke zagayedamu bamu sani ba, idan ma zargi zamuyi wannan tsohon zamu zarga ba aliyu ba domin ya riga aliyu zama tare damu kuma shine ke yini a gidan nan 24 hour’s sabanin aliyu amman nasan me zanyi zan d’ana masa tarko lallai sai na san wani abu akansa ,idan shine yake bibiyata acikin gidan nan zan sani idan ma wani dabam zan sani wannan karon bazan bar kowaye yake da sa hannu cikin bibiyar rayuwata ba yana gama fadar haka ya shige bedroom dinsa shima Ana’s ya biyosa .”
Anas na tare da jaguwa har sanda ya dauki karamar wayarsa daya saka sabon sim ya boye number ya soma neman layin dcp bayan an dauka yaji ba muryarsa bace dan haka yace “Ina son nayi magana da dcp ,”ko zamu iya sanin me yasa kake son kayi magana dashi ?masaniya gareni game da mutuwar honorable abdulaziz ,anas najin haka ya tattara hankalinsa gbdy zuwa kansa dan sam bai yi tunanin ta nan zai bullo da tsarinsa ba , daga can office din jami’an tsaro aka tambaya sunansa yace “Amir ali.”
Wanda ya dauki wayar yace ka bada minti biyar zaa hadaka dashi .”
bayan wasu mintuna aka hadashi da dcp “hello ko zan iya sani da wa nake magana?ba lallai kasani ba amman ni nasanka da dade wa na kira ne na nasar maka cewar “mutuwar honorable abdulaziz abokansa guda biyar ne suka hadu suka kashesa suka binne gawarsa a gidan dayan daga cikinsu .”
shiru dcp yayi domin dai yasan da labarin a halin yanzu ma ana kan bincikensu akan haka sai dai ba’a rigada ansan inda gawarsa take ba “to shi yanzu me zai yi da wannan case din ? shi da yake son ganin bayan jaguwa da tawargarsa me zai sa ya sanya kanshi cikin binciken akan matacce ? dan haka a matukar a fusace yace “shshan banza ni me zanyi to akai da ka kirani ? “Me yasa bazaka kira babban headquarters na abuja ka sanar dasu ba tunda case ya koma hannunsu idan ka samu labarin inda babban dan fashi da makamin nan mai suna jaguwa yake ka gaugauta kirana zamu baka lokacin mu har ma mu hada maka da makudan kudade amman akan matsalar mataccen karka sake kiran mu a waya kit ya katse kiran yana gama fadar haka .”
Shiru jaguwa yayi yana tunani abun yi yana duban anas daya tasa shi gaba da kallo kamar shine dcp din kafin daga baya ya sake Kiran layin aka dauka tare da cewa “da me zan iya taimaka maka ?amir ali ne yake magana wanda ya kira yanzu ka sake hadani da dcp ,okay ka dan rike waya ya mike cikin hanzari ya sake shiga office din dcp alokacin yana tare da yaronsa suna tautaunawa akan scorpion”yallabai mutumin dazu ne yake son magana da kai “batare daya dago ya kallesa ba yace “kace masa bana nan okay sir .”ya dawo yana cewa kayi hakuri a she baya nan” shin ka san …”kafin jaguwa yace wani abu dansanda ya katse kiran ya koma mazauninsa ya cigaba da ayyukan gabansa .”
Dcp kuwa sai faman tsaki yake ja “aikin banza
kawai ko ina ruwana da batun mutuwar honorable abdulaziz, kaje can ka kai rahontonka ga masu bukatar bincike akan mutuwa , ni nan labarin yadda zan kama jaguwa nake nema ba wani mutuwa ba , yaronsa asp isa dake zaune a gabansa yace “yallabai me yasa zakayi haka ai da ka tsaya kaji a ina yasan batun inda aka binne gawarsa “kai bazan tsaya naji komai ba , da jin wannan maganartasa kasan wata qullaliya ce akasa ,amman kuma idan gaskiya ce zai yi matukar mana amfani “dan allah ka rufe mana baki babu ruwanka kaji da karamin matsayinka idan ka kai wannan matsayin sai kayi aiki fiyye da wanda mukeyi a yanzu .”
tsit asp isa yayi saboda ya fuskanci mai gidan nasa ya dau zafi da maganarsa dcp ya cigaba da Magana “wani bayani kuka samu a bakin yaron jaguwa “?har yanzu dai shiru sir yaki yace komai “kun matse shi sosai kuwa ? sosai kuwa yallabai daga jiya zuwa yau din nan ba karamin izaya muka masa ba gbdy mun canza masa kamani amman yaki bamu cikakken bayanai akan jaguwa sai ihun azaba yake .”
“Baku matse shi da kyau ba ,ku matseshi sosai karku masa da wasa idan yaki magana zuwa gobe kusashi a under ground idan shima yaki magana ku sanar min zan masa izayar da bakinsa zai bayyana mana sirrin komai na gidan jaguwa ai tunda ya shigo hannun magana ta kare sai munga bayansu daya bayan “.
“Okay sir !
Ya fada tare da mikewa tsaye cike da girmamawa
har ya kai bakin kofa dcp ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa” Asp isa!”Yes sir ya fad’a tare da juyowa ya Kame agabansa “Kusa ido sosai akan scorpion domin su din barayi ne masu matukar wayo da dabaru kala kala da zasu iya komai domin kubatar da kansu dan haka ku maida hankali sosai ku qara matakan tsoro mai karfi yanzu harinmu na gaba cikin manya abokansa ne dama wannann yaron nasa yace wani abu ne da yanzu mun san ta inda zamu fara aiki lallai sai mun kama jaguwa da gbdy yaransa a mace ko araye inshaallahu ma a raye zasu zo hannu sir ya juya ya bar office din .”
Jaguwa ya furzar da iska yana cizan lip’s dinsa da karfi “wannan itace damar da nake son nayi amfani daita, idan bata samu karbuwa ba bansan me zan yi ba kuma? yayi maganar a fili ya zagaye dakin .
anas ya matso shi yana cewa “karka damu zaka yi nasara ka sake yin wani tunani akai ko kuma ka kira number office din commissioner kai tsaye nasan shi bazaiki amsar maganarka ba ,take zuciyar jaguwa ta amince masa da hakan,ya kira da wani layi ya nemi yayi magana da commissioner ai kuwa kai tsaye aka hadashi da commissioner wanda shima alokacin yana tare da mataimakinsa A kwantagora ya soma magana a natse “ko zan iya sani dawa nake magana”?
“Kana magana da Amir ali ne batun mutuwar honorable abdulaziz ba hatsari yayi ba kashesa akayi
“taya akayi kai kasan ba hatsari yayi ba kashessa akayi “? shikenan idan zaka bani dama sai mu hadu zan baka bayanan komai domin ina da hujoji a hannuna commissioner yay shiru yana sauraronsa tare danna record acikin wayarsa “duk naji bayaninka yanzu daga ina kake magana ?”
“daga kano !
“to me zai hana ka sanar da jami’an dake aiki a kano ko abuja ?”ai gani nayi anan lagos honorable abdulaziz din yake daga nan aka fara bincike kafin case ya koma abuja kuma ni yanzu haka ina airport zan taho lagos daga lagos Australia zan tafi jirgina karfe bakwai zai tashi “to shikenan ka bani numbarka zan nemeka idan ka shigo ,”Aa yallabai ni ne zan kiraka ka bani number wayarka ,to shikenan ka rabuta commissioner ya karanto ma jaguwa numbersa yana maimatawa anas kuma na rubutawa sannna ya katse wayar .”