KUSKUREN BAYA 1 TO 48

commissioner ya kalli mataimakinsa yana sake yi masa bayani abinda jaguwa ya fada masa “ya kake gani zamu yi yanzu “kwanta kwata yallabai ni ban yarda da wannna mutamin ba “taya yasan labarin mutuwar honorable abdulaziz da mutanen da suka kashesa da inda aka binne gawarsa byn har yanzu ana kan bincike ne baa gano inda gawar take ba su kansu abokansa sunki amsa laifin su suka kashesa dan haka ni ban yarda dashi ba karka sauraresa.”
“amman kuma gaskiya ya fad’a mana tunda duk abinda ya fada haka ne kuma da alamun zai yi matukar yi mana amfani,” nan dai suka cigaba da tautaunawa shi dai commissioner ya yarda da maganar jaguwa kuma idan dai har ya kirasa zai bari su hadu ya bashi bayanai akan komai bayan mataimakinsa ya tashi ya koma office dinsa kira ya shigo wayar hannu ta commissioner yana dauka ya fahimci mai magana “me kuma kake so daga gareni ?
“so nake idan na shigo mu hadu da kai kai kadai na baka sheidu masu matukar mahimanci idan kuma hakan bazai yiwu ka hadu dani kai kadai ba shikenan sai na tattara sheidun na watsasu a ruwa daman yanzu adalci yayi wuya ayi sharia a lahira a inda babu wanda ya isa sai allah ,ya tunhumeku akan abinda kukayi ,ni da zaku fahimceni ma bayan wannan mahiman bayanan akwai wasu akan masu safar miyagun kwayoyi wanda dayansu polisawa ne duk zan baka amman kai kadai ,dan da kai kadai kawai na yarda .”To shikenan ai kuwa daka taimaka mana yanzu dai ka sake kirana nan da awa uku zan fada maka inda zamu hadu jaguwa najin haka ya dunkule hannunsa yana jin dadi ya katse kiran ya zauna yana cewa “shikenan tarkona bai kama dcp ya kama commissioner ,sai yanzu hankalina ya kwanta”ya karasa maganar yana sakin murmushi.
“ya yarda zaku hadu kenan ?da alama tunda yace na kirasa byn awa uku zai fada min inda zamu hadu kasan fa shi wannnan commissioner din rikitaccen tsoho ne ina ganin ma a karshen shekara nan zai yi ritiya ,zan bika muje tare .”baka da hankali bakaji nace babu inda zakabini ba , ance maka haduwa da commissioner abu ne me sauki ? ka barni kawai naje ni kadai idan ma matsala ce ta tsaya iya kaina ban da kai ya karasa maganar tare da mikewa ya nufi bathroom dan lokacin sallah laasar yayi .”
Bayan jaguwa ya fito Ana’s ya tashi ya shiga bai bata lokaci ba ya fito alokacin jaguwa ya tada sallah ya karaso ya bishi jim’i byn sun idar suka sake zama sai lokacin jaguwa ya tuna da jama’arsa dake kofar gida gashi ya soma jin alamun hadari ya kuma san muddin bai bada sakonsu ba anan zasu wuni har sai sun ga fitowarsa “anas kira sky kace ya sallama mutanen dake waje ,numfashi ya sauke “gsky kam dan wasu da wannan kudin daake raba musu kullum suke cin abinci batare da bata lokaci ba ya kira layin sky ya bashi umarnin .”
Suna hira suna duba lokaci a hankali har akaci awa daya acikin awa ukun da commissioner ya bayar dan haka suka cigaba da hirar yadda jaguwa zai hadu da commissioner “tunanina idan na kira shi zai ce mu hadu dashi a hotel ko gurin shakatawa ba lallai mu hadu dashi a gidansa ba , nima gaskiya bazan so ku hadu a gidansa ba akwai hatsari gara ku hadu a waje zai fi ,muna haduwa a yau ina tabbatar maka a yau scorpion zai fito domin bazan sausauta masa ba.”
suna cikin hirar wata awa daya tazo ta wuce karfe shida daidai kenan cikin haka hally ta kira layin anas ya zaro wayarsa yana dubawa “my princess .”
Ya fada yana dauka “wa’alaikis salam matata fatan kina Lfy?alhamdulillahi kinji shiru ban kiraba ko ?sorry my princess inshaallahu bazan jima ba zan shigo sukai sallama ya maida hankalinsa ga jaguwa wanda ya dauki sigari ya kai bakinsa “kasan yanzu hatta sigari ina kyamar shanta saboda banason matata taji warinsa ajikinsa “.
Wannan kuma damuwarka ce ni dai ko zan rabu da komai ban da sigari ina mugun qaunarta murmushi Ana’s yayi “wallahi adnan ina maka kwadayin aure da zarar kayi aure gbdy rayuwarka zata canza zaka rage wasu abubuwa tunda ga zahiri na gani akaina idan akace zan daina shan giya da neman mata zan karyata sai gashi hatta sigari ina neman barin ta “kai dan allah tashi mune garin ma ya sake hadewa da hadari nasan muna kan hanya lokaci zai yi na ajiyeka agida na kara gaba da motarka .”
Mikewa yayi ya shirya kansa sosai tare suka jera har suka karaso haraban gidan babu kowa acikin abokan aikinsu sai mai gadi kadai zaune akan farar kujera mai zaman mutun daya dakin ajiye makamansu ya wuce ya dauki bindiga masu lafiya guda hudu da harsashi ya zuba cikin karamar jaka ya fito inda motar anas take fake ya nufa Ana’s ya ciro keyn mota a aljihunsa ya mika masa sannan kowannensu ya bude murfin bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna jaguwa ya waiga ya ajiye jakar abaya ya sanya key ya tayar da mota suka bar gidan .”
Suna barin gidan cid ya soma kai kawo a haraban gidan bashi wannan lungu bashi wancan lugun wanda a garin leke lekensa yasan adadin mutanen dake rufe acikin gidan babu wanda ya bashi tausayi kamar alqali mutumin dake kan aikinsa shima fa da asirinsa zai tono wannan ne hukuncinsa agurin jaguwa tunda ya fahimci basa kisa sai izaya suka iya .”
A halin yanzu shi kansa ya matsu wa’adinsa ya cika ya tattara ya bar gidan domin yana matukar jin tsoro yana cikin tafiya yana dube dube kamar ance ya daga idanunshi sama ya hangi wata tukunyar kasa yar karama acikin tsakankanin fulawas din dake shuke a gurin ,bai yi sanya ba ya juya zuwa daki ya kira number dcp ya sheida masa ,”okay to shikenan amman ban zan samu damar fita ba yau dana zo da tukunyar ,no bai nan yanzu ya fita tare da amininsa .”
“Gaskiya bana tunanin suna zargina ,”okay to shikenan sai dai nayi haka ya fito yana waige waige babu kowa ata bangaren da yake dan haka ya dauki kujera ya kai daidai inda yaga tukunyar ya lallaba ya ajiye ya kara tsayi daita yayi bismillah ya dauko tukunyar ya ajiye yana kallon tukunyar babu komai acikinta sai kahon rago da madubi aciki sosai tsoro ya kamashi .” amman hakan bai hanashi yayi fitsari acikinta ba kamar yadda dcp ya fad’a masa ai gama fitsarinsa ke da wuya wani bakin hayaki ya tashi yayi sama ya dauki tukunyar ya mayar inda ya ganta ya lallaba ya bar gurin .”
Jaguwa kuwa tunda da suka shiga mota hirar yadda haduwarsa da commissioner zai kasance suke har suka hau kan babban titi ilu peju a lokacin garin ya sake hadewa da hadari “idan ruwan sama ya sauko allah kadai yasan lokacin da zai tsaya ,nima tunanina kenan ga aiki mai girma agabana fatana na samu nasara haduwa da commissioner suna tafiya ruwan sama ya tsinke kamar da bakin kwarya gbdy jikin anas yayi sanyi dan haka ya dif ya daina magana yana kallon motocin dake falla gudu akan titi .”
wata mota kirar farari baka wuluk ta wucesu da mugun gudu akan titi ilu peju tafiya kadan motar tai ta tsaya a gefen titi direban dake tuka motar ya waigo alokacin da matan daya tuko suke kokarin tmyrsa dalilin tsayuwarsa a halin yaga ana ruwan sama “tayar motar ce ta samu matsala bari na fita na duba na gani ya fad’a yana kokarin fita cikin ruwa , acikinsu babu wacce tayi kokarin hanashi fita sai hirarsu da suka cigaba da yi gashi mutumin ya dan manyata ,tsohon direbansu ne minister ma ya so kwarai ya ajiye aiki amman tsohon yaki a cewarsa zai iya kuma tabbas yana kokari idan gurin tuki ne .”