KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Boot din motar ya bude ya dauko wani karamin akwati dake dauke kayan gyara ya bude sannan ya duba tayar tan take ya gano matsalarta notikan tayar ne suka dan sake abun daure taya ya dauka ya tsugunna ga ruwan sama na dukansa amman bai damu ba ya fara aiki.”cikin haka motarsu jaguwa ta karaso har ta gotasu kadan ya dawo baya yayi parking yana cewa”Ana’s “bari na taimakawa tsohon can ya gyada masa kai kawai ,ya fito yana tare ruwa dake dukan fuskarsa da hannunsa har ya karaso gurin tsohon ya tsaya tsayuwa irinta ingarman namiji mai tattare da natsuwa da Kamala, a hankali ya motsa lips dinsa yana cewa “baba kawo na taimaka maka ka koma cikin mota ,tsohon ya dago yana yarfe ruwan dake dukan fuskarsa ya tsurawa jaguwa ido yana kallonsa yana ji dadi acikin ranshi yace “yaro na gode Kwarai da gaske allah yayi maka albarka amman kayi tafiyar zanyi da kaina .”
“karka damu baba ka kawo ya kai hannu ya karbi karfen hannunsa shi kuma tsohon ya shiga cikin mota ya zauna “har ka gama baba ?Aa wani dan albarka na samu zai taimaka min ban taba tunanin har yanzu akwai mutane masu kirki haka a cikin wannan duniyar tamu ba ,shiru tayi hakan nan taji gabanta ya shiga duka uku uku bata sake cewa komai ba ,”Jaguwa ya tsugunna a inda tsohon ya tashi ya kwance tayar motar kadan ya sake daureta tanwer dake zaune bangaren da tayar ta samu matsala kamar tayi warning din glass amman ta kasa aiwatar da hakan sai dai ta kasa dauke idanunta daga kallon gurin ga wani faduwar gaba daya dabaibeyeta .”
Bayan ya gama ya tattara kayan aikin da yayi amfani dashi ya nufi byn boot nan ma zuciyarta ta bishi da kallo sai dai bata dago ba ya bude boot din motar ya mayar masa da akwatin kayan aikinsa ya maida murfin ya rufe yana dagawa tsohon hannu dake kallonsa ta cikin mota sai alokacin tanwer ta waigo sosai ta bayan motar domin taga wanda ya taimaka masu ana tsaka da tsuga ruwan sama byn ga motaci nata falla gudu akan titi karaf idanunta ya sauka akan jaguwa ,gbdy kayan jikinsa ya jike sharkaf har sun bayyana tsayayyun nipples dinsa.”
ta kasa dauke idanunta akanshi shima idanunshi
ya tsaida akanta cike da mamaki yake kallonta dan tsantsar mugunta da zalumci shine ta bar tsohon mutane cikin ruwa ita tana hakikce abayan mota lunshe idanunta tayi tana kokarin fitowa daga cikin mota sai dai kafin ta fito har ya juya bata damu ba ta fito cikin ruwan tana kiran sunansa da sauri ruky tabi bayanta da kallo .”
Cikin sauri tanwer tasha gabansa tana sauke numfashi “haba adnan ka tsaya mana .” ransa yayi mugun baci akan wanda yake ciki ” me yasa ta fito cikin ruwa tana kiran sunanshi gashi ta jawo duk jikinta ya jike da ruwa har ya nuna sha shin jikinta ?a kallon da yake mata ta fahimci abinda yake nufi yana da tsanani tausayi da kulawa ,tausayinsa ya kamata shi din mutun ne me matukar tausayi ga mutane matsalarsa dai taurin kai idan ya tsaya akan abu babu wanda ya isa ya kawar dashi ko tsaida shi ,tarasa me zatayi domin ta canza shi ya dawo mutumin kirki a idanun duniya .”tsaki yaja sannan ya riko tsintsiyar hannunta cikin nashi atare qirjinsu ya buga da matsanancin karfi ,ji yayi wani shock ya caki jikinsa da duk wasu jijiyo dake aiki ajikinsa,itama haka taji a sansar jikinta,”
maganad’insun son junansu ne ya shiga yawo a jijiyoyin jikinsu sai dai babu wanda yayi magana acikinsu har sanda ya soma tafiya daita bai tsaya akoina ba sai ajikin motarsu ya bude murfin motar sai lokaci yaga ashe ba ita kadai bace aciki ita da ruky cousin dinta ne ,ta bude baki ta gaishesa amman yayi mata banza tamkar bai ganta ba da hannunsa ya nuna mata cikin motar sannan ya raba gefenta ya cigaba da tafiya ya karasa inda motarsu take ya shiga yajata da mugun gudu yana jan tsaki “.
“Lafiya !?Anas ya tmbyesa “wacan motar dana taimakawa tsohon can ashe tanwer ce zaune a bayan motar tsabar rashin Imani da tausayi ta bar tsohon mutane ya fito cikin ruwa ita da cousing dinta suna hakince abayan mota shiyasa naji motar tayi nauyi ya karasa maganar yana murza sterimg yana jan tsaki .”kai adnan tanwer din da consin dinta guda suke da zasuyi nauyi ?bai sake cewa komai ba dan haushi sannan bai tsaya ba sai akofar gidan anas .
“Sauka mana na qara gaba Ana’s yace “ka shiga ka sauya wasu kaya mana .”ya girgiza masa kai ya kara gaba da gudu shi kuma anas ya shiga gidan ya zauna a falo sharaf yana jiran princess dinsa ta fito tayi masa sannu da zuwa wacce lokacin tana can tsaye gaban mirrow tana tsara masa kwaliya.”
byn ta gama ta karasa wordrobe dinta ta dauko daya daga cikin kayan da ammi ta dinka masu ita da shafiq ta saka ,ta dauko dan karamin akwati dake dauke da sarkokinta kowanne na cikin gidansa tare da dan kunnensu ta dauki wanda take son sakawa ta fara saka dan kunne ta dauki sarka wuya zata saka kenan Ana’s ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama .”
A hankali ta motsa bakinta ta amsa masa tana sakar masa murmushi ya tsaya a bakin kofar dakin yana kare mata kallo tsab dan ba karamin kyau tayi masa ba ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako zuwa inda take tsaye ya tsaya ta bayanta tare da riko kugunta da hannunsa daya ,Kallo daya tayi masa ta cikin mirrow ta fahimci yana cikin damuwa dan haka ta juyo gabadaya ta zuba masa ido tana sake karamtarshi ,meke damunka ka fita cikin damuwa ka dawo min da damuwa ? girgiza mata kanshi yayi alamun babu ya kai lips dinsa ya tsotsa bakinta kadan ya zare bakinsa .”
Wani wahalallen numfashi ta sauke wani irin zazzafan soyayya take masa tana kallonsa ya karbi sakar dake rike a hannunta ya makala mata a wuya tare da shafa gefen wuyanta sannan ya zagaya da hannuwansa duka saman cikinta cikin kasalalliyar murya yake mata magana acikin kunnenta “my princess kina da kyau sosai a duk sanda na kalleki sai nayiwa allah godiya daya azurtani da samun salihar mace irin ki dan allah ki soni duk runtsi karki barni “.
Murmushi tayi masa ta dago idanunta suka tsarke cikin nashi “nima ina alfahari da samunka matsayin miji ,ya sake riketa gam yana lunshe idanunshi yana busa mata numfashinsa ta hanyar shinshina wuyanta a karshe ya zira harshnesa cikin kunnenta gbdy ta wani rikice tsigar jikinta suka shiga mikewa ta soma kokarin zare jikinta shima a rikice ya sake riko kugunta sosai yasa dayan hannunsa ya hade fuskokinsu guri daya hade da daura lip’s dinsa akan nata kasa jurewa tayi dan haka ta sakar masa jikinta ta soma maida masa da martani daga cikin salon data koya agurinsa sun dauki sama da minti shabiyar suna tsotsan bakin juna tunawa da amininsa yasa yayi saurin zare bakinsa cikin nata atare suka sauke numfashi “.Adnan ya tafi ya hadu da commissioner zai dawo ko bazai dawo bai sani ba tharoom dinta ya shiga ya dauro alwala ya fito ya dauki carbi ya zauna ya dan jingina da abun gado yana já ita kuma ta fita daga dakin.”