KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bangaren jaguwa kuwa yayi tafiya me nisa daga gidan Ana’s sannan ya samu guri yayi parking a daidai Devol hotel dake kan titi alabi ,yayi baya da kujerar da yake zaune ya koma ya kwanta ya runtse idanunshi tanwer kawai yake gani cikin kwayar idanunshi shigar abaya da tayi yayi matukar masa kyau , kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta ,
bude idanunshi yayi yana tunaninta yana duba lokaci har awa uku ta cika ya kira commissioner Kira biyu ya dauka ya fada masa inda zasu hadu , suna gama waya ya canza fuska ya shirya bindigarsa mai cin harsashi goma ya soke biyu ajikinsa ya sake shirya biyu ya soke a kafafunsa yayi wa na karfasa shiri me kyau sannan ya dauki hanyar water park daman yana kusa da gurin tafiya kadan yayi ya karaso gurin yayi parking ta kofar baya ya fito ya shiga cikin inda mutane suke wasu da rigar wanka wasu kuma suna zaune akan kujeru na alfarma da kaya ajikinsu shima ya samu guri ya zauna ya kirasa a waya “na karaso okay sir “.
Ko cikaken minti talatin bai yi da kashe wayar ba ya soma jiyo qarar jiniya daman yayi tunanin bazai zo shi kadai ba dole sai da masu tsaronsa nan take ya tashi ya boye har suka karaso ciki tare da masu tsaronsa yana maboyarsa yana kallonsa daga inda yake ya kirasa a waya yana kallo aka mika masa wayarsa “kana ina gani nazo ?”Okay sir ina bayan ta gurin swiming pool ” kai kadai fa nace zazo ? “karka damu ni kadai ne .jaguwa yayi murmushin gefe baki yana kallonsa yayiwa masu tsaronsa magana wasu suka biyosa ,wasu suka tsaya gbdy ya gama tsara yadda zai kawar dasu ya damki commissioner yana zaune commissioner ya karaso daga nesa jaguwa ya daga masa hannu alamun shine commissioner bai karaso ba ya samu wani guri dabam ya zauna jaguwa ya karaso a natse cike da girmamawa kafin ya zauna
abinda yayi tunani shine ya faru masu tsaron commissioner mutun biyu da suka biyosa suka fara kokarin duba jikinsa sai dai basu ga komai ba boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sakamakon basu tabo bidigir dake boye a kafafunsa ba ,commissioner ya nuna masa gurin zama yana cewa “ina bayyana mutuwar honorable Abdulaziz da inda gawarsa yake ?wondonsa yayi sama dashi kadan sai ga wani abu kamar roba shima yayi sama dashi sai ga bindiga ta bayyana muryarsa can kasa yace “ga bayyanan anan ” ya fada yana sauke wondonsa yana dubansa a tsanake “.
“Jaguwa !?
Commissioner ya furta ahankali ta yadda babu wanda zai ji dan tun ganin bindiga yanayinsa da komai nasa ya canza jaguwa ya lumshe masa idanunsa yana cewa ” nasan ka girgiza da ganina ko ?amman karka girgiza ,nayi haka ne saboda banason na rasa wani na kusa dani ,ku kuma burinku na rasa kowa nawa ciki kuwa har dani kaina, yanzu yanzu ka sallame masu tsaronka kafin muyi mutuwar kasko dan ni da ka gani mutuwa bata tsoratani da shirinta na fito .”
dago kai commissioner yayi yana basu umarni su matsa daga guri babu shiri suka yi nesa dashi jaguwa na ganin haka ya zaro bindiga ya soke ajikinsa yace “oya tashi ko “! kamar wani karamin yaro commissioner ya mike tsaye suka jera ta baya yabi dashi inda motarsa take “banason na taba lafiyar tsoho kamarka amman fa sai kayi abinda nake so zaka tsira da ranka da lafiyarka .”
Cikin mintunan da basu wuce uku ba jaguwa ya fice da commissioner suka nufa inda motarsa yake ya bashi umarnin ya zauna a bangaren direba shi kuma ya shiga baya “ka ja motar muje suka bar area gurin gbdy shi kuma yana baya hakince ya saita kan commissioner da bindiga ,babu wanda yaga saita kan commissioner da jaguwa yayi kasancewar glass din motar baki ne “idan kayi aiki acikin second daya, kaima zan barka acikin second daya kayi tafiyarka ka cigaba da rayuwarka cikin koshin lafiya .”commissioner bai ce komai ba saboda matukar girgiza da yayi ,bama dansa ko wani nasa ba ,ko cikin yaran aikinsa zaa danawa tarko ba shi da kansa ?
“lallai wannan barawon ya wuce yadda suke tsammani”kasa a sako min yarona a yanzu nima na sakeka yanzu Idan wani abu ya samu yarona lallai kasawa ranka mutuwa, ban taba kashe kowa ba amman zan fara akanka muddin wani abu ya samesa ba .”
“Babu abinda zai samesa amman kai ka mika kanka zuwa ga hukuma tunda daman an kamashi ne saboda ya bada bayanai akanka ,idan ka mika kanka nayi maka alkawarin zansa a maka hukunci mai sauki , lokacin dana fara alqallarta kasani ko na nemi shawarka bare yanzu ka bani shawara na dauka”?ni nan da kake gani kamani zai yi matukar baku wuya saboda nayi rayuwa acikinku nasan in and out dinku kai bakayi mamakin yadda na samu number office dinka ba “?”Ace baka bani number ba zan samu kuma cikin sauki kuma na tare da kai ne zasu bani dan haka babu ruwanka kayi abinda nake bukata kawai ka tsira da ranka ,babu waya a hannuna da me zan kira headquarters? sun yi tafiya me nisa sannan jaguwa ya tsaidashi alokacin duhun dare ya shigo dan bakwai da wasu mintuna sun wuce .
Yayinda water park na can ya hargitse adalilin neman commissioner da akayi aka rasa kafin kace me headquarters ya samu labari aiko nan ma ya hargitse ska soma Kokarin baza manya ma’aikata titi titi lungu lungu domin bincike kowace mota jaguwa ya kira number Ana’s kira daya ya dauka yana tambayarsa halin da yake ciki “nayi nasarar kamashi abokina kasan na fada maka rikitaccen tsoho ne gashi ma na sashi yin abinda ya jima bai yi ba sai dai ayi masa ,tuki mana ai shi ya tukoni ,sai anjima daman na kiraka né kasan ina cikin koshin lfy dan nasan hankalika bazai kwanta ba yana gama wayar yace “wa zaka kira acikin wadan da suke karkashinka ?
“Mataimakina !”
Ya fada yana sauke numfashi “ina jinka karanto numbersa bai bata lokaci ba ya kirawo masa number sai da jaguwa ya boye number sannan ya kira tare da sata a hands free ,kira biyu cikin na uku A kwantagora ya dauka jaguwa ya manna masa wayar a kunnensa cikin harshen turanci yace “hello kwantagora ni ne commissioner hope baka cikin mutane ?okay abinda nake son fada maka rayuwata tana cikin hatsari ,yanzu abinda nake da kai ka faki idanun kowa ka fito da yaron jaguwa da’aka kama idan ba haka ba sai dai ku tsinci gawata okay!!!
jaguwa ya katse wayar ya gyara zama .
Bayan kamar minti talatin suka sake kira “sir gashi na fito dashi ina zan kai shi ?kaje under bridge din iyanapaja zan turo wanda zai daukesa yaji sautin wata muryar amadadin yaji ta commissioner bance karaka ka tafi da ma’aikatan sirri ba kaje dasu ni kuma nan zanji da commissioner. babu wanda zanje dashi dan allah karku taba lafiyrsa dan ….”
Jaguwa bai tsaya jin me zai ce ba ya katse kiran
Hankali a tashe kwantagora ya figi mota ya dauki hanyar iyana paja shi kuma jaguwa ya kira layin eku ya bashi umarni zuwa iyana paja cikin mintuna talatin kwantogora ya isa sai dai dole yayi parking ya jira kira daga jaguwa ,alokacin shima eku ya karasa ya kira jaguwa ya sheida masa nan take ya kira number kwantagora yana dauka yace “kana daidai ina ?
“Ina daidai inda ake shiga motar ondo ,da uniform ne ajikinka ?eh !Ya katse kiran ya kira eku sukayi mgn sannan ya sake kira kwantagora yace ya bawa scorpion waya ya mika masa wayar sukayi mgn suna gama waya kawai yaga scorpion ya fito daga cikin mota yana dingisa kafasarsa tun yana iya hangosa har ya daina akan titin mowe ibafo jaguwa ya ajiye commissioner ya kara gaba .”