KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Who is Ibrahim to you? In tambayeka ma”. Yayi maganar cikin bacin rai. Cikin girmamawa Nazifi yayi k’asa da kansa.
“Tambayarka nake!”. Ya fad’a da d’an k’arfi saboda damuwa.
“Abokina ne”. Ya bashi amsa batare da ya kallesa ba. “Good naji dad’i da kasan wannan, so stay within your limits kaima you are like a son to me karkayi abunda zai b’ata zumuncina da kai da iyayen ka, I know
What is good and bad for Ibrahim karka damu bazan cutar da d’ana ba shi kad’ai gareni nima kamar yadda Tanweer take gun iyayen ta na tabbatar babu abunda zai sameta she will be back kaji?”ya karasa maganar cikin sanyin murya .
“To Abba, ni zan tafi aiki”. Ya fad’a lokacin daya d’au hanya.
“Owk sai ka dawo my son god bless you for me zaka ji alert kaji ko”. “To”. Abunda Nazifi Ya fada kenan ya fice cike da mamakin halin Alh.Tahir ya rasa dalilinsa na sa d’ansa a wannan halin gaba d’aya da harara Alh.Tahir yabi bayan Nazifi daga bisani ya koma cikin gida abunsa ya cigaba da wayarsa …


ba’a dauki  cikakken minti shabiyar   ba  eku  ya  karaso yana knwoking din kofar a daidai lokacin daya fito daga bathroom kugunsa daure da towel ya amsa da” Yes yana  dakatar dashi sai daya goge jikinsa ya karasa jikin wordrobe dinsa ya zaro jallabiya  milk colour  design  mai shegen kyau da santsi ya zira ajikinsa ya fesa turare mai sanyin kanshi  sannan  ya karaso bakin kofar ya bude ,ya  amshi farar  laida  da flaks din dake rike a hanun eku ya sallameahi ya murd’a kofar dakin da take  ya  shiga bakinsa ɗauke da sallama ,tana tsaye a   lokacin sanye   da daya daga cikin  dogayen rugunan da yasa aka siyo mata, kallo daya yayi mata ya dauke kanshi daga gareta  saboda wani irin abu daya ji ya tsinkari ilahirin jikinsa mai kama da sukar allura   , ya karasa shigowa  tamkar  bashi ne   ya dawo mata  tamkar  bawa ba a dazu ko wani mayunwacin zaki ,ya balain hade ransa kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tun daya shigo hankalinta da idanunta tatare da natsuwarta suka koma  kansa ta kasa dauke idanunta akanshi  ina ma zai aureta ….
tayi kewar iyayenta sosai sai dai bata son rabuwa dashi, tuna sauran awani kadan ya rage ya sadata da gidansu kamar yadda yace  yasa hankalinta ya sake tashi  “why will you disturb yourself over him? Uhm! kika sani ko yana da mata shiyasa yaki amincewa dake, why bother your mind? Why?!”.  zuciyarta ta jiho mata wannan tmbyr take idanunta yayi raurau ya cicciko da ruwan hawaye , sosai take kallonsa tana jin wani irin sonshi nabin lugu da sako na gangar jikinta  ,ta bala’in kafeshi da  idanunta , ya ɗan dago ya kalli inda take batare da yayi magana ba ya ajiye flaks da laidar hannunsa “menene kuma kika  wani tsareni da idanu?  yayi maganar cikin rashin damuwa “a ranta tace kaji da munafurci kana wani ciccin magani like he is not the person that try to…”. Da sauri ta katse tunanin. ” ga abincin nan ki tabbatar da kin ci nan da awa biyu zaki koma hannun iyayenki ta yatsin fuska tana turo masa karamin bakinta cike da shagwa’ba tace “ni ni babu abinda zanci sannan babu inda zani, I won’t go anywhere I will stay here!”.
niyyar fita yake Jin abinda tace yasa  dole ya dawo ya zauna wanda zuwa  lokacin itama ta zauna a gefen gado tana fuskantarshi ya kafeta da kyawawan idanunshi yana kallonta a tsanake, bata fuska tayi tace “meye na wani tsareni da ido kamar zaka cinyeni kana tunanin maidani batare da nasan matsayina ba, ni dole sai ka fada min matsayina kafin! Are you marrying me or not?!”.
“ba ke kike da wannan ikon ba ganin damana ne ko akasin haka yayi maganar a dake yana mikewa  ya karasa ya dauko cup da spoon  ya dauraye wannan tsarin na cikin tsarinsa da  dokokinsa tun bai san zai taka matsayin da yake a yanzu ba ,ya dawo inda take tamkar an dasata ya hada mata coffer ya tsiyaya zuma a ciki ya juya ya  mika mata “ki sha karki ‘bata min lokaci dan lokacin sallah ya karato dole ta Kai hannu ta amsa  saboda  yadda ya  hade rai ta soma kurba kadan kadan tana kallonsa , ya janyo farar laida ya buɗe ya ciro takeway ya buɗe ya janyo karamar stood gabanta ya ajiye tayi murmushin karfin hali tace ” laila kamar wata matarka gsky i will love to be tha…”. “shut up I don’t want hear ….
Sai kuma yayi shiru ya kasa karasa maganar  “ki daina kusanta kanki dani zaki sa zuciyarki cikin rudani  da wahala  dan I can’t be that person”.

shiru ne ya biyo baya kafin daga baya yaja numfashi ya  cigaba da motsa lip’s dinsa  “ina ke ina ni  ? “da kinsan koni waye na tabbatar da ba zaki yi kwadayin kasancewa dani ba har kiyi muradin son zamowa mata agareni , nasan kyawuna ne ya rudeki ko ?”.

tayi saurin hadiye ruwan shayin data kurba tana girgiza masa kai  “no just like that I fa…”.
“Shiii! karki bata bakinki duk abinda zaki fada bazan taɓa yarda ba dan dubunki sun fada Kuma ta nan yake bi  ya fita ta nan ya nuna kunnenshi ,  ta narkar da fuska kamar zata yi kuka ” ka fahimceni dan Allah give me chance to sho…”. “nace bamu dace ba sam! Let’s this be the first and last” ya kasara mgnr yana tsura mata idanunsa dake bugar mata da zuciya”Anyway daga yau basai kin Kuma ganina ba”.
yayi mgnr  a fusace “ki ci abinci kawai , girgiza masa  kai tayi “ka kwantar da hankalinka wallahi da zuciya daya nake son zama abokiyar rayuwarka ,zan zauna da Kai tsakani da Allah, baxan damu da wani abu naka ba idan kuma kana da mata ne yasa kaki   amincewa dani ka fada min bazan so na shiga tsakanin ma’aurata ba? “.  ta karasa maganar kmr zatayi kuka cike da hassala ya katseta  “just eat!

yana zaune ta soma tsakuran abinci kamar bata son ci  har sanda aka soma Kiran  sallah  magrib ,ya  mike tsam ya shiga bayin dake manne da dakin bai wani dauki lokaci ba ya sake bayyana a parlour a kallon da yayi mata ya fahimci gbdy attention dinta yana garesa “ki tabbatar da kin cinye abincin da shirin barin gidan  nan  kafin na dawo daga masallaci”. ya  fita daga d’akin yana taku cikin isa da izza kamar wani jinin sarauta tabi bayansa da kallo har ya bacewa idanunta “ya rabbi Allah ! You alone knows that I am not attracted to him for his handsome face, haka kawai  na tsinci kaina Allah ka kawo min ɗauki ya fahimceni before is too late”.   ta lumshe idanunta wasu siraran hawaye suka gangaro mata  yana fita ta saki spoon din hannunta  ..

Kai  tsaye matsallaci ya nufa da kafafunsa yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda mutane unguwan suke gaisheshi cike da girkamawa yana amsa musu a mutunce  lokacin daya karaso cikin matsallacin tuni sawun gaba dana biyu ya cika bai ji dadin haka ba  yabi sawu na uku cike da ladabi ga ubangijinsa yake tada kabbara  bashi ya fito daga massalacin ba  sai da akayi isha’i yana fitowa daga masallaci Kai tsaye gida ya dawo ya sameta kwance cikin bargo  idanunta a lumshe “ke ki tashi muje kou gabanta ne yayi mummunar faduwa  har ga Allah tana son komawa gida  ga iyayenta dan tasan suna can cikin tashin hankali most especially mum  dinta sai dai  bata son barinsa dan tasan ba lallai ta sake had’uwa dashi ba kamar yadda ya furta , akwana  daya datayi dashi ta fahimci shi din mutukin kirki ne wanda samun irinsu ke da wuya “ki tashi muje there is no time to waste”.
tana jinsa tayi shiru ta sake  lafewa  haɗe da kamkame jikinta ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button