KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A yanzu tunanin tanwer shine worst da yafi komai d’aga masa hankali don yana jin muddin bata amince ta auresa ba zai iya rasa rayuwarsa ,acikin mayen tunaninsa ya soma canzawa ya dinga magana da zuciyarsa “me yasa zaka zama haka adnan bayan kai din jarumi ne ba’a ta’ba kasaka a komai ba ? “baa ta’ba ganin rauninka a komai ba me yasa zaka bari aga rauninka akan mace macen ma da kake da tabbacin tana sonka ?”ka shareta kawai ka cigaba da rayuwarka ya qarasa maganar hade da zubewa kasa alokacin da karfe hud’u ta buga wani naunayen bacci yayi awon gba dashi .”

Yadda yake kallon anas ta cikin app haka shima anas din lokaci zuwa lokaci yake dubashi ta app yana kallonsa gbdy yaga halin damuwar da yake ciki, hankalinsa yayi matukar tashi amman yaki nunawa dan kar hally ta fahimta ta shiga damuwa ,dan haka ya sake janyota jikinsa yayi mata kyakkyawan runguma bacci bai daukesa ba sai daya sake dubawa yaganshi kwance bai motsi ya fahimci bacci yayi sannan shima ya kwanta da zumar gobe da sassafe zai tashi yaje ya gansa ya kuma bashi hakuri komai ya wuce dan yasan muddin bashine ya bashi hakuri ba ba zai daina wannan fushin na babu gaira babu dalili ba.”

Jaguwa bai tashi ba sai kusan karfe takwas ya mike ya nufi bedroom dinsa yana layi saboda mayen baccin dake idanunshi kai tsaye bathroom ya shiga yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah ya haye gadonsa tare da lullube ilahirin jikinsa da bargo me taushi ya koma bacci wani bacci ne me nauyi ya daukesa bai tashi ba sai gurin 1:00 dot shima kiran sallah daaka kwlla a masalacin unguwarsu ne ya farkardashi ya sauko daga kan bed dinsa bathroom ya shiga yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa daure da white towel ya tsaya gaban mirrow yana kallon qirjinsa da murdaddun hannuwansa ya kai hannu ya shafa qirjinsa sannan ya sauke numfashi “ni din ba irin nmjin da mace zatace bata so bane ko daina so bare macen dana juya rayuwarta daga duniyar kasa zuwa sama jannati da shaukina”ina tanwer bazaki iya rayuwa babu ni ba kamar yadda nima bazan iya rayuwa babu ke ba .”

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke ya dauki lotion din da yake shafawa ya shafa ajikinsa zuciyarsa na ayyana masa abubuwa “tunda ita tace ta daina sonka bazata aureka da sana’arka ba ka auri haseera zabin mahaifiyarka ita ai bazata gujeka ba daman kuma ta tabbatar maka da zata aureka a duk yanayin da zaka kasance ka koma gareta kawai
Ka bar tan na zuwa wani lokaci .”
“Wankakkiyar zuciyarsa tace “da wannan haukan zaka auri hasera? ka dai canza shawara karkaje fushin zuciya ya kaika ya baro “?ka koma gurinta kawai ba sai ka mata jarabawa ba dakakiyar kwakwaluwarsa ta bashi karfin gwiwa da hakan .”

tsaf ya shirya cikin kananan kaya ya feshe ilahirin jikinsa da turare me sanyin kamshi yana sake bawa kanshi kwarin gwiwa ya dauki cum ya taje sumar kanshi da kasumbar dake kwance a kyakkyawar fuskarsa ,ya fito zuwa falonsa inda ya iske an gyara tsaf idanunsa ya sauka akan table babu farantin jiya na tabar wiwi sai wani faranti dabam murmushi yayi dan yasan wannan aikin anas ne dan shi sam bai iya gyaran komai ba kuma baya yarda wani cikin yaransa yayi masa sai anas daman kuma tun fil azul shine me qokarin gyara komai .”
“Anas kenan bai san sanda murmushi ya subuce masa ba da sauri ya hade fuskarsa sakamakon jin qarar bud’e dakin yasan bai wuce Ana’s ba shi din ne kuwa ya shigo shima kyakkyawan shirinsa ya raba ta gefenshi ya fita daga dakin ran anas yay matukar ‘bace ganin sharesa da yayi amman hakan bai hanashi daukar plet din abinci ya biyosa dashi ba .”

Tsaye a bakin fridge ya iske shi ya dauki fresh milk da cake yana ci duk da shi din ba me son zaki bane amman haka ya dinga turawa cikinsa anas ya ajiye plet din hannunsa akan center table adaidai lokacin da jaguwa ya samu guri ya zauna tare da daukar remut ya kunna tv a natse anas ya qaraso inda yake ya mika masa tafin hannunsa “assalamu alaikum .” da kamar ba zai amsa ba sai kuma ya mika masa nashi hannu bayan sun gaisa anas ya kasa sakar masa hannu ya cigaba da dubansa kamar ranar ya fara ganinsa .
“ya kake fatan kana cikin koshin lafiya ? jaguwa yayi masa banza kamar bai jishi ba “a ransa yace ina fa zanyi wata koshin lafiya byn an hada kai da kai ana neman haifar min da damuwa ,”allah yasa mu dace ya kuma bamu ikon zama da juna lafiya da amana kasan idan kana tarayya da mutun sai ana hakuri ,
idan wanda kake tare dashi yayi ba daidai ba ka fad’a masa gsky tunda kana zaune dashi ne tsakaninka da allah ,karka ce zaka zuba ido kana kallonsa bazaka masa magana ba ,ni kasani kasan halina adnan bana kwanciya da kowa araina duk kuma wanda yace yana sonka to yana sonka .”

“Ban iya son mutun ba anas kai ma ka sani amman yadda kayi min jiya kamar ka buga wani abu ne haka naji har yasa jikina yayi sanyi “jaguwa ya fada cikin mawuyacin hali yana ciza lip’s dinsa da karfi .
“Nima haka ne adnan ina bugan jiki qirjina akanka iyayena dangina kowa nawa yasanka kafin su bar duniya ,kai kasan you’re so special to me ,abinda kayi min banji dadi ba ,”nima ai haka ne banji dadi ba ka wulakantani ka fada min magana me zafi ka tafi ka barni cikin zafin radadi “?
“Ya zan maka adnan ? kona tsaya bazaka saurareni ba ,mintuna nawa na dauka a gidan kafin na wuce ? ko ka dakatar dani kana kallonfa na bar dakina,koda yake gani kake kamar bazan iya rayuwa ba idan babu kai wanda ba haka bane kawai allah ne ya jarabceni da qaunarka acikin abokai na cireka daya tilo wanda zan bugi qirji ince wannan shine aminina amman sai kake son ka daukeni kamar ban san me nakeyi ba wanda ban san dalilinka ba ina jure kowani wulakaci da cin fuska amman idan yayi yawa sai na dakatar da mutun domin shine kawai zai sa na samu sausauci dan banason wulakanci kai kuma abincin ruhinka kenan kaga kana wulakata mutun gashi baka son gaskiya ni kuma muddin muna tare da kai zan fada maka gsky ko zata maka dadi ko zata maka ciwo amman sai na fada maka idan ya bata maka rai muyi zage zage amman banda zargi abokina ya karasa maganar yana dubansa Kamar zai zubar da kwalla “.

“Ka gama abinda ya kawoka “.?jaguwa ya fada yana dubansa zuciyarsa na karkarwa.”
“Eh!
“To sakar min hannu haka nan dan ka wani rike min hannu zakasa jijiyon hanuna suyi week ,sannan ka tashi ka wuce tunda kai kace bazaka fita aiki ba mu kuma shirin fitar da zamuyi yau muke yi kaga tunda bazaka ba ai ya kamata ka barmu ko ?.ya share wacan maganar da anas shima anas din yadda yayi masa haka yayi yace “bakace komai ba akan maganar da nayi yanzu ? “me zance maka kayi duk abinda ya fiyye maka idan ka shirya rabuwa damu ne bismillah “?”banason wulakanci adnan wai kana tunani zan mutu ne idan na barka da kake wasu abubuwa?” bari na fada maka zan iya rayuwa babu kai “dana mallaka maka abinda zai rike kai da rayuwar taka ba “? Eh naji koma me zakace ina sonta da ganin kimarta sbd ta mallaka min dukkanin farincikin dana rasa”. jaguwa ya kallesa a dage yana tabe lips dinsa .”
Sannan murmushi ya sube masa “dan iskan abokina zaka rabu dani akan mace kenan ?ni bance haka ba ni dai bana son rigima komai ya wuce kai ne ka bani haushi yasa nace maka bazan je koina ba ,Ina fatan komai ya wuce yanzu zumuncinmu ya kai har aljanna don Allah idan kayi ba daidai ba ka dinga natsuwa a fada maka gsky “Naji inshaallahu komai ya wuce har abada amma don Allah kai ma ka daina bin bayan tanwer bana jin dadi ,yarinya nason ta dinga juya ni kai kuma kana side dinta kai da zakayi side dina mu taru mu yaketa “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button