KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Ai gskiyar kenan da baka so nifa banga laifin yarinyar nan ba kuma bazakasa naga laifinta ba
dan gskyar dake ranta ta fad’a ,”ai sai tayita fama da gskyarta takamarta ina sonta ba taje na hakura daita “au kana sonta ne a she ?”Bansani ba dan rainin hankali kawai kaga ni yanzu zabin uwata zanbi zan ma fi jin dadinta , nan da mintuna talatin ma gidan ammi zanje zaka fita operation ko ka fasa ?” Me zai hana masoyi kai kasan kai ne kwarin gwiwa ta hira ce ta balle a tsakaninsu kafin daga bisani jaguwa ya mike tsaye shima ya mike “ka tsaya ka duba system zakaga yadda muka shirya komai y akan tsari amman dai ka sake dubawa abinda kaga bai yi ba ka gyara bari naje bazan dade ba zan dawo yasa kai ya fice “.
“Okay zan duba idan na gama zan koma gida nayi sallama da madam saboda halin rayuwa zamu sake ganin juna ko kuma tafiyar kenan ?kai fa matsalar ka kenan sai ana jin dadi ka wani sako zance mutuwa murmushi Ana’s yayi yana karyar masa da kai tare da nuna shi da dan yatsantsa daya,ba dole na fadi haka ba tunda muna aikin sai da rai .

A hankali suka fito tare daga cikin bangaren jaguwa anas ya nufi inda system yake shi kuma ya fito zuwa haraban  gidan kai tsaye inda jerin motocinsa suke ya nufa yana kokarin shiga mota eku ya qaraso da sauri da hannu ya dakatar dashi baya son zashi gurin ammimsa ajashi, ya shiga motarsa Range Rover black colour yaja ya fito daga cikin haraban gidansa   ya tsaya a kofar gida batare daya kashe motarsa ba ya sallami masu zuwa amsar kudin taimako a duk safiyar duniya ,cike da farinciki suke saka masa albarka yaja motarsa yayi gaba ,a natse yake tuqi zuciyarsa na tunanin tanwer amman sai yayi sauri kawar daita ya sako wani tunani dabam a haka har ya qaraso kofar gidansu yayi parking ya fito yana taku a hankali tamkar baya son taka kasa  nan ma dai mutane sukai masa casaaa yan maula ya tura hannu cikin ajihunsa ya zaro bandir din kudi ya mimika masu sannan ya shiga gidansu bakinsa dauke da sallama  yayi mamakin da yaji baa amsa ba dan da wahala ka shigo gidan kana sallama ammi bata jiyo ta amsa ba .”

Yana kokarin kutsa kai cikin falon ammi hasera ta fito da sauri hannunta rike da plet  tana cin soyayyar kaza sauran kadan ta fada jikinsa yayi saurin ja da baya  yana kakkabe jikinsa murmushi ya bayyana akan fuskarsa  “a’a danuwana sannu da zuwa haka nan ya tsinci kanshi da jin haushin ta tamkar ba dan ita yazo gidan ga , yaja tsaki batare daya amsa ba , ta kada kafadanta alamun bata damu ba ta cigaba da yagar kazarta shi kuwa yayi matukar hade fuska  yana sake jin damuwa yaji komai ya sauya masa ba karamar yadda yazo da niyyar zai karbeta ba ,yadda ma take cin kazar ma kamar wata mayunwaciya “ina ammi ? yayi tmbyr a can kasan makoshi tare da juya wa ya nufi  part dinsa na gidan   “me kace ? ta biyosa da plet tana tmbyrsa “mara kwakwaluwa kawai yanzu zakice bakiji me nace ba da zaki min wata irin tmby ?”.ya fada a zafafe yana cigaba da tafiya .”

“Allah ya baka hakuri ai banji abinda kace bane shiyasa da zaka wani ce min mara kwakwaluwa .”ya waigo inda take a bayansa ya kalleta a natse ,gata dai Kmr goggagiya amman sam villager ce ko magana bata iya ba komai  da hauka take yi ,to daman yaushe zaa hada  mutumin  da yazo daga maiduguri da wanda yake rayuwa a lagos ?”.ita kwakwaluwa bata aiki yadda ya kamata idan ana dankara mata nama dan allah malama ki ajiye kazar nan haka kin wani rungume kaza Kmr baki taba ci ba yasa kafa ya buge plet din hannunta  ya shige part dinsa  shiru tayi tana kallon kazarta a kasa  ba tace masa komai ba dan  ta fahimci rigima yake ji dashi ta zuba wa kazarta  ido tana kallo .”Ta dauki lokaci tana kallon kazar kamar ta dauka amman ta guji  ta disga kanta ta hakura   tabiyosa dakin ta samu guri ta zauna tana fuskantarshi tare da sha gala da kallonsa atsawa ce yace “ke !.

“Tayi firgigib ta dawo haiyacinta “naam  danuwa ta amsa da hakan batare data nuna damuwar da ke din daya kirata dashi ba ita da zai dinga shiga tsabgarta koda zagi ne ai zataji dadi ,”kawo min  ruwan sha a cup”.  ta mike ta juya da sauri yabi tafiyarta da kallo sam babu natsuwa kamar tanwer ya lumshe rikitattun idanushi “Anya kuwa zan iya karbarta na hakura da tanwer “ ? Yana wannan tunanin taje ta kawo masa ta mika masa ya bude idanunshi da kyar yace “sha !
Ta bisa da kallon mamaki dan ita bata bukatar wani ruwa “ki sha ki samu natsuwar  wannan bare baren kallon da kikyi wa mutane Kmr zaki cinyesu ya sake bata umarni ta narke masa fuska  alamun baza tayi ba “ke wasa nake dake  ne ? nan take tayi kamar yadda ya umarceta ta shanye ruwan tasss ta rike cup din tana kallonsa ,” kije ki ajiye cup din ki dawo,tana fita ya zaro kwalin sigari acikin aljihunsa ya kunna yana zuka a hankali har ta shigo a matukar tsorace take dubansa “danuwa daman kana shan sigari ne ?meye sabo aciki ? ai  duk suna cikin munanan dabi’una dana fada miki ko ma nace kadan daga ciki dan idan kikaji sauran ko kika gani bub zuciyarki zatayi ta buga “babu komai ina sonka a haka dan ni ko warin sigarin ma banji ba ta fada tana kokarin zama “bala’i ! Ya fada a kasan ranshi yana kallonta a kaskance abinda tanwer take mugun kyama shine ita wai ko warinsa bataji ba ?“nace ki zauna né ? ya fada a matukar fusace tayi sauri ta mike tsaye tana dubansa ya cigaba da abinda yake batare daya sake cewa komai ba .”

Bata  zauana ba  ta cigaba da tsayuwa tana dubansa  tana murmushi d’an duk abinda yayi mata bata ji zafi ko haushi acikin zuciyarta  ba bahasalima dadi taji dan tana mugun son kusancinta dashi  wani irin kallon soyayya take masa idanuwansa suna matukar mata kyau a duk sanda ta kallesu sai taji kamar ta sunbaceau amman babu hali  ya mike tsaye ya fito itama ta biyosa abaya sai ga ammi ta dawo “a’a yaushe kazo adnan ?Na  dan jima da zuwa ya fada yana shafa sumar kanshi ina kikaje? “nan kusa na shiga nayi barka  ne jikar gidan baba yaro ce ta haihu .ta shiga ciki  bangarenta hasera ta biyota da sauri tana yi mata rada shima dole yabiyota  bangarenta ta  zauna akan kujera me zaman mutun biyu suka gaisa ta tamvayesa aikinsa da abokan aikinsa duk yace mata suna lfy ta kira hasera “ki kawowa yayanki abinci mana  “aa ammi a koshe nake daman akwai wani aiki da zamu fita ne yana da matukar hatsari muna bukatar adduarki.
Aikawa nan take  ta shiga zubo masa sun dan ta’ba hira yace  “ammi ni zan wuce tô shikenan adnan allah yayiwa rayuwa albarka ke hasera kibi yayanki ya kaiki shopping din tunda baki da me kaiki dan allah ka sauke min hasera a wannan plaza din dake ayabo zata dan yi siyayyan kayan amafninta ne idan ma da hali ka tsaya har ta gama ka dawo min daita kaji dan alabarka .”

ya hade rai sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa sai dai bai amsa mata da zai kaita ba ko bazai kai ba  har sanda hasera ta shigo falon “dan allah ku tafi tare mana kaji yarona ai ba kullum né zaka dinga kaita ba  yau ne kawai ta fadi haka ne saboda ganin yadda ya hade rai “.aransa yace zamu fita tare amman babu inda zani daita a rabin hanya zan ajiyeta na qara gaba “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button