KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Muryarsa a matukar hargitse yace “minti biyar na baki ki shirya idan ba haka ba sai dai ki nemi wanda zai kai ki ya fada yana shan kamshi tare da zira hannunsa daya cikin ajihinsa “kiyi maza ki shirya ki fito tun kafin ammi ta karasa maganar ta fada daki a wulakamce yabi bayanta da kallo sam sam bata da natsuwa da kamun kai wannan sai tanwer ita kuma dan taga ta samu kanshi shine take son juya zuciyarsa da rayuwarsa.”
Minti biyar din ma bata gama cika ba ta fito da sauri kamar an korota yayi gaba yana sake yiwa ammi sallama kanta kawai ta girgiza wannan zuciya bata san ranar da zai daina ta ba abun zuciya da wanda bana zuciya ba duk fushin né agurinsa allah dai ya kawo maka sauki ta kalli haseera dake kokarin sanya baby shoe akafafunta “kiyi sauri fa kinsan halinsa zai iya wucewa ya barki ki dai san yadda zakiyi ki dan shawo kansa ku fahimci juna dan ina son ayi komai cikin kankanin lokaci a wuce gurin qarar hon din motarsa yasa ammi ta takaita maganarta “maza wuce gashi can ya fara danna hon dinsa me hargitsa lissafi da sauri tayo waje ta bude murfin mota “kayi hakuri please na tsaya saka takalmi ne “wa ya tambayeki wannan shirmen sannan da zaki wani bude min mota nace ki shiga ne ?ke me yasa baki da natsuwa ne bare wani abu shi class?ranta yayi mugun mugun baci zuciyarta ta soma zafi da tuttukin bakinciki amman dai ta danne ta tsaya tana dubansa batare data shiga din ba ,shima kallonta yake yana son yaga wani abu ajikinta wanda zai dauki hankalinsa ko guda daya kawai ya aureta ya manta da wata tanwer a rayuwarsa amman sam ya kasa hango komai bare ya dauka zallar shirme ne ke tattare daita sai daya gama wulakantata sannan ya motsa bakinsa”shigowa !”
A ranta taja tsaki tana cewa duk ka gama iskancinka da wulakancinka zaka shigo hannu ne zaka gane baka da wayo sai kaga kudi kace kashi ne dan iskan me daurin kai da zafin zuciya kawai ta shiga ta zauna bata gama rufe murfin motar ba yaja da gudu tayi sauri ta qarasa rufewa tana dubansa kamar zatai kuka .”
Gudu kawai yake a natse akan titi batare daya waigo inda take zaune ba bare ya kalli fuskarta ta waigo a tsanake tana kallonsa da kallon hannunsa daya dake kife yana motsawa a hankali ,taji kamar ta daura hannunta aka kyakkyawan hannunsa masu matukar haske da sheki ,wani sanyi dadi ke ratsata hade da sanyi ac wanda ke sake tsokano da matsanancin soyayyrsa dake daskare acikin zuciyarta ,hagu da dama shine kawai zuciyarta take muradi wani irin tuqi yake cikin salo me kashe wa duk wanda ake tukawa jiki .”
sai da sukayi rabin hanya taga ya tsaya a tsakiyar titi batare daya kashe motar ba sannan bai kalli inda take ba “maza sauka ki kama gabanki “
A matukar tsaro ce ta kallesa “bana da kudi ajikina fa tayi Kmr zatai kuka wani abu ya daga a gefensa ya ciro bandir din yan dubu day day na dubu dari ya daura mata akan cinyarta “ki sauka zaki samu wata motar da zata kai ki duk inda kike so kai tsaye dan ni bani da wannan lokacin “haba danuwna me yasa zaka min haka ?Sam bai kyautu ba da zaka barni anan abun sam babu dadi “Shiiiiiiii bance ki dameni da hauka ba just ki fita nace kuma karki qara kirana da danuwa kirani da sunan da kowa yake kirana dashi okay dan ni ba danuwanki bane “.
“Wai ma me yasa ka tsaneni baka sona haka ?,me na rasa ya adnan ?tayi masa tmbyr tana tsareshi da idanunta “amman daka soni da karka soni duk daya ne aurena ne dai babu fashi sai ka aureni kuma sai kayi rayuwar aure dani tamkar sauran ma’aurata “ai bazaki ta’ba samun wannan damar ba arayuwarki ,
oya dauki kudin nan kiyi out yayi maganar a tsawa bata san sanda ta wawiro hand bag dinta ta fito ta koma gefen titi ta tsaya tana kallonsa yaja motarsa ya qara gaba da mugun gudu.”
Hankalinta yayi kololuwar tashi da gatanta da komai arzikin ma da yake takama dashi byn mahaifinta ne silar samunsa da ba dan shi ba da yanzu killa ma bara suke yi akantiti gashi yace shi ba danuwanta bane , taji kamar ta kira mahaifinta ta fada masa wulakanci da yayi mata “amman kuma idan kika kira zaki lalata komai dan adnan ba mutunci garesa ba zai iya fadawa mahaifinki ido ido baya sonki alhalin shi bai san da wannan matsalar kinga kin kunnowa kanki huta gara ki share ki cigaba da hakuri da sannu komai zai daidaita tunda ammi tana son aurenki dashi ai ko baya só sai ya aureki dole ta numfasa kana ta soma kokarin tsaida mota wata mota “tsaya ta fada cikin harshen turanci mai mota ya tsaya, ta fada mata inda zata ” babban gurin siyayya dake kusa da nan zaka kai ni ya gyada mata kai ta shiga mai motar yaja “.
Da misalin karfe biyar daidai na yammacin rana acikin shopright dake ikeja tayi musu kowannensu sanye da kananan kaya idan kagansu zaka d’auka shopping zasuyi ,daya bayan d’aya suka raba kawunansu bangare dabam dabam cikin salon kawar da hankalin mutane akansu ,kamil né zaune akan keken guragu yayinda anas ke tsaye abayansa yana turasa sai dai bada siffar bara ba dan sam shigar jikinsu batayi kama da wadan da suka zo neman taimako ba ,kowanne daga cikinsu kunnensa manne da abun jiyo sautin maganar jaguwa, haka zalika sauran jubi da jabir suna saman gurin suna baza idanu suka ta inda indoor zai shigo domin har zuwa wannan lokacin da suka rigada suka shigo suka fara bincikensu babu wata alama daya shigo gurin .”
Ahankali jaguwa ke hawowa saman lift hannunsa rike da wani had’adden karfe wanda marasa idanu ke amfani dashi ,idanunshi rufe cikin bakin glass me shegen kyau da tsada jikinsa sanye cikin kayan dark army green sai dai riga ta kasance me hula ce yayinda wando ma ya kasance kalar rigar jikinsa sai dai daga kasan wandon a tsukakken yake , jikinsa na wani irin fitar da kamshi turare flower ross .”
a natse yake komai nashi hankalin wasu daga cikin mutane dake gurin ya raja’a akansa most especially mata domin yayi matukar yin kyau sai dai fahimtar da sukayi makaho né yasa fuskarsu ta sauya ta nuna alamun tausayawa garesa ,ya dan waiga kasa inda yaga shigowar wasu fararen mutane su biyu suna magana da juna kamar ya juya ya sauko sai yaga kamar mutanen dake kallonsa zasu fahimci wani ba dan haka ya cigaba da kallonsu yana motsa lip’s dinsa a hankali domin hankaltal da yaransa kamar ance ya dago kansa idanunsa suka sauka akan sanyin idaniyansa ,soyayyarsa ,haukansa ,rayuwarsa tanwer ce ke saukowa sanye cikin doguwar riga hannunta rike da farar leda suna hada ido gabanta yayi wata irin mummunar faduwa shima faduwar gaba yaji ta riskeshi kwayar idaunta ta tsaida akanshi wanda yasashi jin wani abu na ratsa jiki da zuciyarsa take yaji komai ya sauya masa wasu abubuwa suka shiga yawo ajikinsa suna zaga jinin jikinsa gabadaya .”
So yayi ya dauke idanunshi daga kallonta saboda yanzu ba lokacinta bane idan yace zai biye mata komai zai wargaje masa amman ya tsinci kansa da kasa aiwatar da haka ‘wani irin kallo me daga hankali take binsa dashi tsigar jikinta na mikewa, Kallonsa take tun daga kan fuskarsa da kafafunsa dake rufe har zuwa yatsun hannunsa dake rufe cikin bakar safa babu wani abu daya nuna shine mutumin da ko baiyi amfani da ainihin fuskarsa idan ta gansa zuciyarta na fahimtar shine .”
saitin zuciyarsa tabi da kallo wanda hakan ya tabbatar mata da shi din ne tsaye a gabanta zuciyarta ta cigaba da dukan tara tara wanda yasata gaugauwan dauke idanunta daga kallon juna da suke shi kuwa har lokacin ya kasa dauke idanunshi akanta yana kallonta har ta sauka ta barshi zuciyarsa na wani irin dokawa da sauri ya biyota yana tsaidaita a hankali cikin sanyayyar murya batare da yayi amfani da sunanta ba só yake ya gano wani abu ba tayi mamaki jin ya tsaidaita ba .”