KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ta ta juyo a natse aiko idanunta suka tsarke cikin nashi yana tsaye abayanta still rike da sanda naunayen numfashi ya sauke ita kuwa ganin rauninsa yasa ta sake had’e rai sosai tamkar bata ta’ba yin dariya ba ,muryarsa a tsarke yace “kamar naso na sanki sai dai na manta inda na sanki yayi mata tmbyr yana shafa sumar kanshi “wannan ba wacce kasani bace ko akwai taimakon da zan iya maka ?”kankance idanunshi yayi ya saka cikin nata qirjinsa na wani irin luguden bugu “okay ina ganin kamace “. baiyi mamaki ba dan a irin shigar da yayi ba lallai ta ganeshi ba, ya soma qakarin kusantota da niyyar fitar daita daga gurin dan kar hargitse ya faru tana ciki hankalinsa zai rabu gida biyu amman yaga ta qara taku ta matsa baya ita anata tasan muddin shine mutumin da zuciyarta ke dokawa akanshi yana gama qarasowa ba qaramin aikinsa bane ya had’eta da faffadan qirjinsa sake motsota yayi da sauri ta dakatar dashi “malam ka tsaya a iyakarka karka sake ka karaso inda nake adnan ko ka dauka bazan ganeka bane .”ta fada a matukar firgice.
step daya ya qara yana cewa waye kuma haka ?ya tamabayeta cikin wata irin murya “maganar wasa ta wuce ni nasan kai ne , ko wani irin canzawa zakayi hakan bazai sa na kasa ganeka ba kai ne dai adnan ahmed já…”Shiru tayi sakamakon karfen hannunsa daya saki a kasa kuma san dan katse mata maganarta yasa yayi hakan ,”ai kece kawai kakisan wannan.” tana gama jin abinda ya fada ta juya fuuuuuu tana rausaya tamkar wata bishiya
Bashi da yabi bayanta da kallo ba mutane dayawa sun bi bayanta da kallo sakamakon tafiyarta me d’aukar hankali nan take yaji wani kishi me tsanani ya caki kahon zuciyarta soyaytarta ta shiga masa kuwa acikin zuciya .”ahankali ya shiga daga kafafunsa domin biyota alokacin indoor ya shigo tare da yaransa shima kamar jaguwa da yaransa haka suka raba kawunansu ai kuwa nan take hankalinsa ya rabu gida biyu “.ya waiga yabi indoor da kallo sannan ya waiga hanyar da tanwer tabi da kallo har lokacin tafiya take na daukar hankali wanda ke sake kunno wutar soyayyarta…”
Manage please ????
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️43
….”Ahankali ya sake waigawa ya kalli bayan indoor dake tafiya ,a d’an rikice ya kamo lip’s dinsa na qasa yana taunawa gumi na karyo masa bisa goshinsa at the same time yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fiyye da kaida ,baya jin zai iya kasadar rasa tanwer arayuwarsa sam bai so ya had’u daita ba ,da kuma yasan da zuwanta da babu abinda zai sa ya fito wannan aikin a yau, daya hakura da duk abinda za’a samu domin kuwa duk son da ya kewa aikinsa rayuwarta ta fiyye masa .”
Cikin tsananin tashin hankalin ya soma tafiya cikin sarsarfa yana magana kasa kasa “duk kuna jina ?suka had’a baki gurin amsawa da “eh!”To kusa ido sosai akan indoor da wad’ancan mutanen guda biyu na d’azu .”ya karya yabi hanyar da tanwer tabi tana kokarin karya wani layin , ta samu guri ta labe qirjinta na dokawa da matsanancin karfi dan ta lura kamar ya biyota ,dube duben nemanta yake amman babu ita babu alamunta ,daya bayan daya yake shiga gurin tsiyayyar amman stil bai ganta ba dan haka shima ya yanke shawara ya samu guri ya boye.”
Leko da kanta tayi ta duba hagu da dama bata ganshi ba ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta fito ta cigaba da tafiyarta ,bai fi taku uku tayi ba taji saukar hannun mutun ajikinta da sauri ta juyo a matukar tsorace tana qokarin bud’e baki ta kurma ihu ta gansa tsaye dan haka tayi shiru tare da sauke ajiyar zuciya,ya zuba mata ido duk da ba asalin idanunsa bane amman sai data ga wasu abubuwa na fitowa daga cikinsu suna daure jijiyoyin jikinta .”
Ya d’auki second goma yana tsaye yana kallonta sannan ya kai hannunsa ya riko tsintsiyar hannuta cikin nashi ya nufi wata hanya da mutane basu kai kawo ya tsaya ya sake zuba mata ido, had’e fuskar tayi sosai tana cewa “wai meye haka ne ?”da sauri jaguwa ya girgiza mata kai “kinga ni bawani tashin hankali nake nema ba kawai ina bukatar ki bar nan kuma a yanzu .”
“saboda me kenan zan bar nan ? saboda banason wani abu ya ta’ba min lafiyrki “wacece ni da zaka
ce baka son wani abu ya ta’ba lafiyata ? ya lumshe idanunshi yana shafa goshinsa da hannunsa ya dauki second biyu a haka sannan ya dago kanshi “kinga malama ki maida hankalinki kiyi abinda nace kafin raina ya baci “tsaki taja da karfi ta cigaba da magana cikin tsananin fushi “kaga nifa banason wata matsla idan wani abu ya sameni meye damuwaarka ?”kamar yace mata babu amman ya kasa furta mata hakan ya cigaba da dubanta a tsanake . “kaga kaje dan Allah kayi abinda ya kawoka dan ni babu ruwana da abinda ya kawoka duk ma abinda ya kawoka nasan bai wuce …”
cikin tsananin fushi yasa hannu zai buge mata baki ta kauce da sauri muryarsa cike da hassala yace “wannan bakin ina mutuwar sonshi amman sam bashi da mutunci amman zanyi maganinsa ne .”
wani irin kallo tayi masa wanda ya shagaltar dashi dan bai san sanda ya soma murza hannunta dake cikin bashi ba “wannan ikon duk na da ne a yanzu babu me maganin wannan bakin ta hanyar isa ko nuna iko sai wanda zan aura dan haka ka tsaya a matsayinka na wanda naso a ada “.tana gama fadar haka ta zame hannunta dake rike cikin nashi ta juya ,hannunsa taji ya riko kugunta gam ya hadeta da jikinsa sosai kmar zai hade bakinsu gurin daya “karya ne tanwer har yanzu ina cikin zuciyarki bama zaki iya saka wani mahaluki acikin zuciyarki ba wannan zuciyar tawa ce kuma ni kadai “. tanwer ta lumshe idanunta tana jin yadda soayyyarsa ke sake hud’a jiki da zuciyarta “wayyo allah adnan gbdy ka mamaye komai nawa amman duk da haka bazan ta’ba sadaukar maka da farincikina ba har sai ka saduda ka zubar da makaman yakinka kayi abinda nake so , cikin murya me cike da kasala ya cigaba da magana “dan allah tanwer kiyi abinda nake bukata”.
hancinta ta hura masa kawai batare data amsa masa zatai ko bazatai ba sai dai alamunta ya nuna masa bazatai abinda yake bukata ba dan sai kokarin turesa take domin ta bar gurin dan haka ya jata zuwa wani madaidaicin plaza dake cikin shopright din wanda ake siyar da dafaffen abinci ya zaunar daita akan daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin , ya matsota sosai kamar zai shige jikinta yana shafa gefen fuskarta “kiji maganta ki zauna anan kada kiyi Kuskuren barin gurin nan duk runtsi duk wuya har na dawo ya furta cikin wani irin salo me kashe sansar jiki ,bata amsa ba ta dauke kanta daga kallonsa ta fuskanci masu siyar da abincin shi kuma ya juya cikin sauri ,bata juyo ta kallesa ba har ya fice daga gurin yana fita ya gyara abun kunnensa ta yadda kowannensu zai jiyosa “lokacin kutse yayi .” ya fada cikin zafin nama bayan fitarsa da minti biyar tanwer ta mike cike da tsinkewar zuciya tana jan tsaki ta fito sai dai batayi nisa ba opposite din plaza data fito ta shiga tana duba agogon mata qirjinta na cigaba da faduwa wanda ta danganta faruwar hakan da ganin jaguwa da tayi duk da a nata bata dauka operation yazo kasancewar shi kadai ta gani .”