KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Kamar kullum tana zaune a offi dinta ya shigo yana cicci magani da hannu ta nuna masa gurin zama “ba zama ne ya kawoni ba “to kana iya wucewa dan ina da abun yi “baki isa ba yadda na baro tarin ayyukan dake gabana nazo lallai kema dole kiyi lokacina ya fada yana dukan table din gabanta ta dago ta tsura masa ido shima ita yake kallo jikinsa na tsuma dan gaji da wahalar dashi da take “ina jinka yau kuma da me kazo ?tsaki yaja ya watsa mata hararar ta shiga hankalinta jin tayi shiru yaki magana ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin dake gabanta on-expecting taga ta janye file din gabanta ya barka ta dago a rikice tana dubabsa cike da manaki ,bata gama mamakin ba taji ya watsa mata a fuska ya sake daukar wani ganin zai dauki na uku ta tattara ta boye a bayanta tace “wai meye haka ?.
“Bansani ba ki ajiye komai kiyi lokacina shine zaman lafiya taja dogon numfash ta sauke kana ta soma mgn “ya kamata zuwa yanzu ka fahimceni muyi soyayya ada a yanzu kuma babu ita wannan soyayyar ka fahimceni kayi hakuri allah zai baka wacce zatayi daidai da rayuwarka dan yanzu Ib ..”
“Karki sake ki qarasa wannan sunan kinji na fada miki ya katseta a fusace yana huci kamar zakin daya ga abinsa ya rasa byn second biyu ya kwantar da murya “ni ban san taya zan fahimceki ba amman ina son ki fahimci cwion abinda nake ji akanki,tanwer ba ban ta’ba faduwa a komai ba dan hakan bazan fadi a soyayyarki ba .”ga tun wuri ka cire wannan soyayyar kaga ni gbdy so nake ka rabu dani ko dole ne ?”
Ya tsura mata rikitattun idanunsa yana kallonta can kuma murmushi ya bayyana acikin fushin da yayi “kika ce na rabu dake ko ? ta gyada masa kanta alamun Eh!.
“Daman kin koyar dani yadda zan soki ne dan ki juya min baya ?”Ban sani ba amman dole ka karbi faduwa tunda bazaka dauki shawara ba ka ajiye girman kan nan naka sannan ka jajurcewa zuciyarka ka zubar da makaman yakinka ka sauya rayuwarka daga ta dabbobi zuwa ta bil’adama dole ka amsa faduwa, idan ma har ka kasa aikata hakan ni da kaina zan sa polisawa su damkeka damka kuma ta har abada dan sai ba tabbatar da kashiga hannu “.
“Wannan ne kuma karya dan zuciyarki bazata iya ba tanwer kina ganina cikin damuwa zaki fini shiga tashin hankali saboda kema maya ce akan sona.
“wannan labarin da né adnan ,wannan zuciyar ta daina sonka kai ina jin ma ban taba sonka arayuwata ba ,wancan ma na burgewa ce kawai kamar yadda na fada maka kana burge zuciyata ce da wasu abubuwa daga lokacin dakace kana sona naji babu wadan abubuwan da…”
“ you’re lie tanwer ,why are you lie to me?”
“Daman akwai abun burgewa agurin dan dashi da makami ? Karki manta nifa tantirin dan ta’ada ne da kasa gbdy take nemana me yasa zan burgeki.?tayi shiru qirjinta na dokawa wallahi tasani ba iya burgewa bace kawai tsantsar soyayya ce sai dai bazata iya sadaukar masa da farincikin da yake bukata daga gareta ba “Wallahi ban taba faduwa a komai ba tundaga kan jarabawa aji har zuwa muamula ta rayuwa, lokacina na awa daya shine lokacinki na awa biyar ki maida hankalinki sosai bazaki iya komai akan ki raba zuciyarki da soyayyata ba gara ma ki yarda cikin sauki muyi abinda ya kamata lokaci na Kure mana d’an kome zai faru ni bazan rabu dake ba”yana gama fadar haka ya juya ya nufi hanyar fita cikin tsananin fushi ,yana qaqarin fito ib na kokarin shigowa babu wanda ya tsayawa danuwansa har gara ib ya dan karkace shi kuwa jaguwa kai tsaye ya fice ib ya bi bayansa da kallo babu abinda ya dauki hankalinsa kamar zanen hannunsa daya dan leko ta kasan hannun rigarsa .”
“Ib !
Ta kira sunansa da sauri ya maida hankalinsa kanta yana dubanta tare kulle kofar “tanwer waye wannan mutumin ?kaina ciwo ib kamar ya cire ,oh sorry my tan kinci abinci kuwa ?ta rausayar masa da kwayar idanunta tana girgiza masa kai “kefa likita ce bai kamata kina barin kanki da yunwa ki dinga kokarin kina cin abinci akan lokaci .”bari na qarasa aiki mu wuce gida yayi shiru yana kallon takardu dake watse a office din “wa yayi wannan aikin ?Tayi shiru dan ta rasa me zatace “wannan mutumin …”
“Kai Ib me yasa ka fiye damuwa da tambaya “okay nayi shiru qarasa muje ya cigaba tsayuwa yana tunanin zanen hannun jaguwa kasa yin komai tayi ta tattara abubuwanta tace su gida .”
Gudu jaguwa yake akan titi cikin rashin natsuwa ji yake kamar zuciyarsa zata buga hakan ne ma yasa yaga kamar baya gudu akan titi tsaki yake tayi yana qara gudu duk jikinsa tsuma yake kwakwaluwarsa ta hargitse kamar wanda sabon hauka ya kama bayan doguwar tafiyar da yayi ya qaraso bakin tafkeken get dinsa yayi hon me gadi ya fito da sauri daga dakinsa ya bude masa ya shigo tare da qarasawa inda yake parking motocinsa yayi parking ya fito ya nufi cikin gida duk zaune a babban falonsa ya samesu sun baje yayinda wasu daga cikin su ke shan taba wasu wiwi banda anas da kunnensa ke manne da waya wanda yasan da matarsa yake .”
Gbdy yaransa na ganinsa suka mike suna masa sannu da zuwa da kai kawai ya amsa musu ya nufi hanyar bedroom dinsa yana balbale botiran gaban rigarsa zuciyarsa na matukar zafi .”
A tsaye Ana’s ya samesa yana zariya a d’akin tamkar wanda yayiwa sarki karya “adnan !.a zuciye ya juyo a hankali ya kallesa kamar zai yi kuka “meke faruwa da kai ?shiru yayi ya kasa magana ya rungume hannunwansa duka a qirjinsa yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsa shi “dan allah ka fada min abinda ke damunka duk kayi wani iri kallonsa kawai yayi batare da yace uffan ba ,”
“Ka fad’a min mana ko kana da wanda zaka fadawa daya fini ne ni abokin kukan ka ne idan ma damuwa ce muyi tare idan ma ta kama muyi kuka muyi ajiyar zuciya jaguwa ya sauke “ina cikin damuwa na rasa yadda zanyi Ana’s wallahi ina son tanwer soyayyar da bazata misaltu ba zuciyata zata daina bugawa in har ban mallaketa ba .”
Kamar anas yayi dariya amman ya danne “ai wannan duk abu ne me sauki zaka mallaketa sai dai na godewa da yau ka furta yadda kake ji akanta “kaga yadda tanwer take wasan kwallo dani anas,wai ni anas? Sorry my friend shiyasa naketa fada maka a can baya kaki fahimtata na fada maka ka kiyayi ranar da zaka dawo kana mutuwar sonta “ please Ana’s ka taimakeni ta fahimceni ta barni da aikina kai kasan yana da mahimmanci “inshaallahu zamu san abunyi haka dai sukayita tautaunawa har sanda abokin cid ya shigo gidan basu sani ba .”
Cikin dakinsa ya turasa “da gaske da bindiga ajikinka ka shigo ?daita na shigo mana ,lallai hakarmu zata cimma ruwa yau zamu taki saa gabadayansu suna nan yanzu sojoji da polisawa da dss zamu kira suyiwa gidan diran makiya na godewa allah yau aikina yazo karshe matsayi na mai gadi ya qare ya dauki waya ya tura sako ,”
suna cikin wannna tautaunawar jaguwa ya fito ya nufi lambu yana zukar wiwi har zai shiga sai kuma adaidai lokacin mai gadi ya fito tare da bakonsa “kaga mu zauna anan kafin su qaraso suna zama sai ga jaguwa yana tafiya yana zukar wiwi yayinda hannunsa daya ke cikin aljihun wandonsa a hankali idanunshi ya kai bakin kofar dakin me gadi mutun biyu yagani zaune yayi mamaki matuka dan haka cikin tsananin tashin hankali ya yar da Karan sigarin hannunsa yana kokarin qarasowa inda suke “tun daga nesa me gadi yace “gashi nan fa shine jaguwa bakinsa kawai jaguwa ya kalla ya fahimci abinda ya fada .”