KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Yana gama karasowa yace “waye wannan?yallabai kanin abokina ne ya kawo min ziyra byn tsawon lokacin da yayi baya qasar Sa’ad ga gaishesa mana wanda aka kira da Saad ya gaishesa jaguwa bai amsa ba dan haka nan yaji maganar me gadi bata shigewa ba bugu da kari faduwar gaba me tsanani dake kai kawo a qirjinsa kuma ya kasa danganta hakan da matsalar tanwer juyawa yayi ya nufi hanyar baya bai tsaya a koina ba ya sai inda tukunyarsa take kallo daya yayi mata yaga alamun an taba koma yace an canza mata zama daga yadda ya ajiye dan shi mutun ne da ko yaya ka taba masa abinsa zai gane duk kuwa tsawon lokacin da yayi bai waiwayi abun ba .”
Tsaye daya yayi kasancewar dogo ya dauko nan yaji wata sabuwar faduwar gaba sakamakon ganin madubinsa da mahonsa sunyi bakin kiri sabanin yadda ya ajiyesa kuma baba ya fad’a masa duk sanda yayi haka akwai damuwa da sauri ya zagaya ta dayan hannun ya koma bangarensa hankalinsa a tashe yana kiran layin baba yana masa bayani “tabbas aiki aikin wannan alama da kagani alama ce da polisawa zasu iya shigowa gidanka a duk sanda suka so ,haka zalika Wacan aikin na saduwa da yarinyar nan ma ya lalace shiyasa nace ka aureta ka tsaya jayayya danj “kokarin da nake yi kenan ba saboda na kamu da tsanani soya …”bai qarasa maganar ba ya soma jin jiniyar yan sanda a guje ya fito daga dakin sunan Ana’s ya fara qira da karfi sannna sunayensu sauran ya biyo baya cikin kankanin alokacin suka hallara agabansa “ku kulle gbdy windows din part din nan da duk wata kofa da zata fitar da mutun waje akwai da…”

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️44

…..basu tsaya jin dalilinsa ba gabad’aya suka watse cikin tsananin tashin hankali zuwa kulle kofofi da window’s kamar yadda ya basu umarni, cike da kwarewa da aikinsu suke aiwatar da abinda me gidansu ya sakasu, yayinda shi kuma yake faman kai kawo a parlour’n yana neman mafuta ,
sosai kwakwaluwarsa ta shiga cajin nemo hanyar ku’buta ,cikin kankanin lokaci sukayi suka gama lokacin da polisawa , sojoji har ma da dss sun firfito acikin motocinsu sun kewaye gaban gida da bayan gida atakaice dai sunyiwa gidan zobe rike da bindigu .”

cike da tsinkewar zuciya anas ya qaraso ya jigina bayansa da bango tare da tokare kafarsa d’aya da bangon parlour’n ya rungume hannuwansa duka a qirjinsa idanunshi na kallon sama gabad’ayansu sun shiga tsananin tunani da firgici domin kuwa sun fahimci wannan ranar itace ranar tonon asiri agaresu da wahala wani ya tsira acikinsu .”

bangaren anas shima abinda yake tunanin kenan rayuwarsu tazo karshe ya rungume kome da zai faru dashi “amman halimarsa da d’an cikinta sune damuwarsa ” ko ya zataji idan ta wayi gari ta samu sakon mutuwarsu ko kuma aka haska fuskokinsu agidajen tv shi da dan’uwanta a matsayin rikakkun yan fashi ?”nan take zufa ya shiga tsatsafo masa a ilahirin jikinsa ,ahankali ya dinga motsa bakinsa yana furta kalmar “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “wannan kalmar kawai yake furtawa yana maimaitawa acikin zuciyarsa da zahiri .”

Jaguwa ya tsaya cak ya sauke idanunshi akan
ana’s dake tsaye cikin tsananin damuwa koda
bai yi magana ba ya fahimci halin da yake ciki
jikinsa tattare yake da jin tsoro da faduwar gaba ganin bayansu da’ake son yi shi da tawagaru ,
cike da sanyi jiki ya d’auke idanunshi akanshi
ya soma tafiya cikin sarsarfa sakamakon fahimtar da yayi an shigo gidansa bai tsaya akoina ba sai ajikin window dake had’e da koridor dinsa
ya dan bud’e kad’an babu wanda ya gani yana magana da daya daga cikin polisawa sai ya’u me gadinsa’ wani irin mugun bugu gabansa yayi da karfi ,qirjinsa ya shiga dukan tara tara a d’an rikice sannan cike da tashin hankali ya dawo inda ana’s yake tsaye cikin zullumi ya riko hannunsa cikin nashi ya soma tafiya dashi ya dawo bakin window alokacin da me gadi ke kokarin cire gemun karyar da yake amfani dashi ya mike sosai bisa kafafunsa daga rusunarwa da yayi ya tsaya cak bisa kafafunsa babu wata alamun tsufa ajikinsa a she yaro ne matashi kamar su “ka duba ka gani ana’s “.yayi maganar a tsawace cikin tsananin fushi .”

“a she wannan ne dan leken asiri da’aka turo ?”daman an kirani shekaranjiya daga headquarters
cewar ina tare da me daukar rahotonmu , ni kaina naji hakan ajikina baba ya’u ba tsoho bane basaja yake yi domin yasan sirrinmu ? zan d’auki mataki a wancan ranar kaki yarda yau ga irinta nan .”shima ana’s zuciyarsa ce ta shiga bugawa fiyye da kaida nan take ya shiga kokuwa da numfashinsa dake barazanar d’aukewa saboda tsananin mamakin baba “ya’u ahankali Ana’s ya shiga girgizawa jaguwa kai “yanzu dai ka yarda ko babu sauran abinda zakace?” idanun anas yayi ja ya kasa sarrafa harshensa .”lallai mutane duniya abun tsoro ne ,mutun ba abun yarda bane ,wanda zuciyarsa ta zarga dabam wanda ya zamo maci amanarsu dabam wata irin tsanar baba me gadi ne ya caki zuciyarsa.”

Wani wawan tsaki jaguwa yaja yana shafa goshinsa yana furzar da iska me zafi daga bakinsa .”Yayinda anas ya shiga wurwurga idanu domin neman yadda zasuyi ,a yanzu yana ganin gara wasu su rayu kodan abinda baba ya’u yayi masu ya duba gabas da yamma ,kudu da arewa babu wani gurin mafaka a inda suke, ringin wayar jaguwa ta soma yi ,ya dawo inda sauran abokan aikinsa suke tsaye jugun jugun ya jingina ,hannunsa rike da kugunsa ya soma receiving call “ya’akayi fatan ba wata matsalar bace ?” shine abinda baba ya tambayesa .”

idanunshi dake a lumshe ya sake lunshewa sosai “qatuwar matsala ce baba “. ya furta yana katse wayar dan ya fuskanci idan ya tsaya ‘bata lokaci komai zai kwa’be masa ya fuskanci yaransa yana dubansu daya bayan daya gbdy yanayinsu ya sauya , a yadda yake kallonsu kawai suka fashe masa da kuka ,sky kuka ,eku sconpio kuka hatta su kamil da jubi da jabir idanunsu yayi jawur dan basu shiryawa mutuwa a yanzu ba .”

shi kuwa jaguwa ya cigaba da tsayuwa a dakensa amman duk da haka kana kallonsa zaka fahimci yana cikin rud’ani muryarsa can kasan makoshi ya soma magana “da fari kowannenku ya saka wayarsa a silent “ jikinsu na rawa duk suka ciro wayoyinsu suka saka a silent suka zuba masa ido suna jiran umarni na gaba wannan dakiyartashi ya bawa anas kwarin gwaiwar soma yin magana”abinda nake so da kowannenmu idan mun shiga hannu duk azabar da za’a ganawa daya daga cikinmu karmu kuskura muce wani abu kamar yadda kowannenmu yasani akwai akida a aikinmu ,abu na gaba mu fita kawai ayi bata kashi a tsakaninmu da jami’an tsaro nasan wasu zasu mutu wasu kuma zasu tsira wadan da suka tsira acikinmu suyi kokarin su daina wannan sana’ar dan haka muje mu d’auki bindigu mu fara farmasu kafin suzo garemu ya qarasa gaban jaguwa ya kamo hannuwansa cikin nashi “idan na mutu amanar halima da abinda zata haifa suna hannunka domin jikina ya bani kai zaka tsira acikinmu ya qarasa maganar yana jin saukar hawaye acikin kwayar idanunshi “ka rike min amanarsu nasan zakayi fiyye da haka ina matukar qaunarta da qaunar abinda zata haifa min .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button