KUSKUREN BAYA 1 TO 48

dukkanin su kallon anas sukeyi yadda yake maganar siyar da rai jikinsa na rawa yadda kasan an jona masa shocking ne da kuma yadda yake mika amanar matarsa da cikin jikinta wanda su sai alokacin suka san da wani ciki sannan suka juya suka kalli JAGUWA wanda idanunsa yayi wani irin canzawa kamar zai yi kuka kuma sun san na tausayin anas ne , “kana hauka ne anas da zakace muyi gaba da gaba jami’an tsaro “? ai gara mu cigaba da tsayuwa nasan duk runtsi bazasu kashemu ba muddin muka mika wuya “.inji cewar jubi .”
“Ina zuwa !.”
Jaguwa ya fada tare da juyawa da sauri haka né ya katse maganar jubi yabi bayansa da kallo yana huci bedroom dinsa ya nufa nan ya shiga tattara abubuwansa masu mahimanci ya fito da sauri ya dawo inda suke tsaye suna kallon kallo a tsakaninsu ya turawa malam mudi sako sannan ya tura wayarsa acikin aljihunsa ya nufi wani daki da suke ajiye abubuwansu masu mahimanci.
A natse asp kaccala ke takowa me gadi da yan jarida na biye dashi abaya yana zayyane masa abubuwan dake cikin gidan “shi fa kama wannan mutumin daidai yake da tonuwar asirin wasu daga cikin manyan kasar nan ,yanzu haka nasan sun fahimci zuwanku, kamashi shine hujjar da zai bama hukuma damar kama masu mara musu baya, amman fa inda satarsa zata burgeka yana taimakawa talakawa da marasa galihu da marayu kullum safiya kofar gidan nan cike yake da jamaa masu zuwa kar’ban taimako wallahi koni yana burgeni domin a zamana dasu basu min wani abu na batanci ba girmamawa ne a tsakanina dasu banci aikinmu bisa kaida da amana ne wallahi da babu abinda zai sa nayi sanadin da zai shiga hannun hukuma .”
suna tafiya yana cigaba da bashi bayanai , kai tsaye bq suka nufa inda d’akunan dasu zahra suke ciki,dakin farko da’aka bud’e da alqali idanunsu yayi tozali nan yan jarida suka fara aikinsu ta hanyar d’aukarsa vedio,ya rame sosai kasumba ta cika fuskarshi idan ba kwararran sani kayi masa ba bazaka ganesa ba ,aka fito dashi da taimakon wasu daga cikin ma’aikatan tsaro ,daya bayan daya me gadi yake nuna masu dakunan da mutane suke ciki ana fito dasu .”
Suna tsaye jaguwa ya dawo hannunsa rike da akwatin karfe eku da sky suka soma kokarin karba a hannunsa ya sakar masu sannan yace “maza ku bude cikin sauri suka soma budewa , mamaki ya mamayesu ganin wasu manya filiti irin na masu gadi da jami’an tsaro suke amfani dashi agabansu kala biyu ne aciki na hannu da wanda ake d’aurewa a goshi , ya kai hannu ya d’auki guda biyu na hannu dana goshi ya mikawa anas ya kar’ba ya rike yana dubansa sai dai hankalinsa ba’a kwance yake ba shi kadai yasan halin da yake ciki amman haka dai ya daure ya cigaba da kallonsa yana cigaba da mikawa kowa yana basu umarnin su d’aura goshi sannan su rike na hannu.”
Bayan ya mikawa kowa ya dubi anas da bai daura nashi a goshi ba “ka daura mana “.bai ce masa komai ba ya cigaba da kallonsa yana kokarin daura wa qirjinsa na cigaba da bugawa jaguwa ya shiga gaba yana cewa “ku biyoni muje .”nan take suka biyosa har suka isa parlour’n baya wanda kusan girmansa daya ne dana gaba “ku tsaya anan “.suka koma inda ya nuna masu suka tsaya suna jiran suga wani irin taimako zai yi masu ,zasu bace ne kamar na wancan rana ko kuwa wani abu dabam zai masu domin su tsira “.makeken table din dake tsakiyar parlour’n ya fara ja”.
a daidai wannan lokacin kira ya shigo wayar Ib dake zaune kusa da tanwer yana fama daita taci abinci a samu ta sha magani dan jikinta ya dauki zafi sosai numfashi ma da kyar take fitarwa ,ba komai ke damunta ba illa soyayyar da adnan dake nukurkusanta ,ita kadai tasan yadda take ji a duk sanda taga bacin ransa,fushinsa na daga mata hankali “. Ib ya d’auki wayar yana duba screen din wayar sunan “AA shalem ya gani yana yawo a screen din wayar ,me gidansa ne a hukumar dss ,da dan sauri ya mike ya fita daga parlour’n ya d’auki wayar “hello sir “daga can bangaren akace “kana ina ne “?”na dan fita ne sir “kayi hakuri sir gani nan zuwa yanzu yanzu zan samesu acan ya katse kiran tare da dawowa inda ya bar tanwer ke kwance akan doguwar kujerar me zaman mutun uku “baby zanje wani guri me mahimanci zan dauki lokaci ban dawo da wuri ba kai ina ganin ma dai sai yadda ta yuwu dawowata a yau .”
lumshe masa idanunta tai tana jin wata irin mummunar faduwar gaba duk da ta matsu
Ya tashi ya kama gabansa amman sai da taji wani iri ajikinta ,gbdy tsigar jikinta suka mike ganin yadda tayi ya qaraso gabanta yana kokarin shafa fuskarta ta goce ta mike zaune hakan nan zuciyarta ta bata kwarin gwiwar tambayesa inda zashi .”Ina zaka ?”.
Yayi shiru bai so tayi masa wannan tambayar ba d’an a aikinsu basa yarda su fadawa kowani mahaluki inda zasu koda kuwa iyayensu né ,sai dai suce suna da aiki a tayasu da addua samun nasara .”
Ta tsura masa ido tana son taji amsar da zai bata
yadda ta sanya kwayar idanunta cikin nashi bazai iya kin fada mata ba dan ji yake kamar tana fixgarsa zuwa gareta,ai kuwa kwayar idanunta sunyi tasiri sosai ajikinsa a hankali muryarsa can kasan makoshi ya fara mgn ta yadda babu me jinsa sai ita kadai “tantirin dan fashin da makamin da kasa ta dade tana nema ne yau aka samu nasarar shiga gidansa bayan tsawon lokaci daakayi ana bibiyarsa yanzu haka ma jami’an tsaro suna gidansa anyi ta kirana a waya baa sameni ba sai yanzu “meye sunansa?”ta tambayesa qirjinta na cigaba da dokawar da yake “Jaguwa”!ya bata amsa atakaice yana kokarin juyawa wani irin bugu gaban tanwer yayi da karfi daga bisani qirjinta ya shiga dokawa da sauri sauri bata san sanda ta yunkura ta mike zaune ba jikinta na daukar rawa.”
“wayyo allah adnan dina ta furta acikin zuciyarta tana dafe qirjinta daidai inda yafi bugawa ,har ya kai bakin kofa ta kira sunansa jikinta na d’an kyarma “IB!” ya tsaya cak tare da juyowa ya fuskanceta dan ma itace yasa ya tsaya a yadda ya samu kiran gaugauwan nan da wani ne ba zai tsaya ba ganin tayi shiru tana dubansa kamar ranar ta soma ganinsa yasa shi motsa lip’s dinsa “ya akayi tanwer “?zura masa ido tayi kawai ba amsa “bazakiyi magana ba byn kinsan sauri nake ?”Ta kallesa da raunannun idanunta da suka canza tana son dauke masa hankali dasu ,tasan shi sani na ainihi baya wasa da aikinsa da wahala ya shiga cikin aiki bai yi nasara ba, ko kowa ya kasa shi zai iya sbd kwarewarsa da sanin kan aikinsa da wahala idan ya tafi jaguwa bai shigo hannunsa ba “ke nake jira idan akwai abinda zaki fad’a min ko kike bukata ? bana son komai kuma bana bukatar komai kawai bana son kaje wannan aikin ne saboda banason na rasaka a halin yanzu “. tayi maganar kamar gaske bata son ta rasashi.
Wani murmushin jin dadi ne ya bayyana akan fuskarsa“bazai yiwu ba tanwer zuwana ya zama dole domin wannan aikin alkwari ne akaina ,a kowani hali kake muddin kafafunka suna tsaye a kasa dole ne ka gabatar dashi ,sannan koda baka da cika alkwari idan zaka shiga wannann aikin ya zama dole ka koyi yadda ake cika alkwari ,wannan aikin alkwari ne karki damu zanje lafiya na dawo lafiya fatana Kiyi min adduar samun nasara ya zamo ni dana yi fita karshe ne zan samu nasarar kamashi kinga qarin girma daga dawowata zai samu ?.”
ta gyada masa kai kawai kamar zatayi kuka a ranta tace “da izinin allah bazaka ta’ba samun nasarar kamashi ba bare ka samu wani qarin girma na banza da wofi ya fahimci yanayinta ya sauya zai ma iya cewa yanayin daya gani tattare daita bai taba gani ba amman sai yayi tunanin ko saboda bata son ya fita ne yasa yanayinta ya sauya ya daga mata hannu kawai ya juya ta fita da sauri .”