KUSKUREN BAYA 1 TO 48

ta runtse ido tana jin wani irin ciwo ajikinta “ya allah ya hayyu ya qayyum ka tsare min adnan ka kawo masa karshen wannan maseefa dake yawo acikin rayuwarsa ,ka yaye masa banason ya mutu cikin wannan maseefar shiyasa nayita kokarin ya bar sana’ar saboda gujewa wannan ranar ya Allah ga bawanka adnan ka tsare min shi idan kamashi shine silar shiriyarsa kasa ya shiga hannu a yanke masa hukunci ,ta karasa maganar tana zubar da hawaye masu zafi kwanciyar da ta kasa komawa kenan ta dauki wayarta zata kirasa taji halin da yake ciki tunani tayi kota kirasa da layinta ba lallai ya dauka ba saboda yanayin da suka rabu dashi tayi sauri ta shiga dakin mumy babu ko sallama allah yasa bata dakin tana bathroom ta dauki qaramar ta soma kiran layinsa ,kiran na shiga amman baa d’auka dan haka ta dawo falo sai dai tá kasa tsaye ta saka zaune ”
Gama jan table din keda wuya Anas, Kamil, Jubi, Jabir da suke tsaye cikin rudani suka zubama JAGUWA ido suna masa kallon mamaki sanadiyar gani wani murfin karfe daya bayyana me kama da abun masuburbud’an sanyi ,yasa yaransa suka bud’e bayan sun gama bud’e murfin sukayi tsaye suna kallo kofar sirri ko hanyar sirri zasuce wanda ke dauke da matakala bayyane a gabansu wannan shine karo na biyu da ya nuna musu abun mamaki, haka akaso kamasu a Abuja yace sudafashi sunayi sai gasu sun bace battt ,yauma gashi suna cikin rudani da tashin hankali ya sake zuwa musu da wani fik’iran nashi ,toma yaushe akayi wannan wurin wanda su suna gida tsawon shekara basu sani ba take Jaguwa ya basu umurnin kowannensu yaje store ya dauki katon na ruwan nestil ya shiga dashi .”
hakan kuwa sukayi d’aya bayan d’aya suka dinga takawa suna gama shiga wani mamakinne suka sake gani wani hadadden gida suka gani wanda babu abinda babu acikin sa harma yafi wanda suke ciki tsaruwa dakuna ne masu yauwa ga parlor yasha kayan more rayuwa komai akwai shi a wurin sukam sun gama sarewa da jaguwa shi din na daban ne Jaguwa na ganin su Anas sun gama shigewa ya lalubo wayarsa ya tura ma Tan sako kamar haka.”
“burinki ya cika yau ganin na shiga hannun hukuma sai ki zuba ruwa a k’asa kisha tanwer, hankalinki ya kwanta kisa a ranki Inuwa na rabu dake rabuwa ta har abada domin kuwa mutuwa ce gabana kinga idan na mutu bazaki sake ganina ba .”yana gama tura mata ya shiga yayi step biyu sannan ya janyo kofar bai kai ga rufewa ba ya janyo table din kusa yana sakin kofar table din na sauka akan kofar adaidai lokacin sifikar jami’an tsaro ya karade gidan “ku fito ku miko kanku cikin sauki kafin mu shiga mu sakar muku wuta .”
Duk da sun dan samu mafaka amman hankalinsu baya jikinsu yadda suke bin koina da kallo haka shima yake binsu da kallo bayan kamar mintuna shabiyar suka maida hankalisu garesa suna dubansa sai kuma yaga gbdy sun kwashe da dariya ban da anas d’an shi har lokacin zuciyarsa bata samu natsuwa ba yagansa a wajen gidan kawai yafi bukata baa kasan gidan ba d’an komai zai iya faruwa “yaransa suka shiga daga masa hannu suna sara masa “lallai gaba da gabanta ,gsky da gaske kai kadai ne fadera a kaf kasar nan ,kwarewarka na matukar burgemu, daman idan da kai ai babu wani fargaba ko tashin hankali,kai ne kwarin gwiwarmu ,haka ma sauran abokansa uku sun jinjina masa daman kuma
ya dade yana basu abun mamaki amman na yau dabam ne Kenan ya shiryawa zuwa wannan ranar “?
Abinda suka barwar ransu muddin yana raye zasuyi safe babu wani abu da zai samesu.”
Jaguwa ya gyara tsayuwarsa sosai yana fuskatarsu sai daya kallesu daya bayan daya batare da yace uffan ba su dai har lokacin kallonsa suke yi cke da matsanancin farinciki baiwar da allah yayi masa magana suke yi kasa kasa kowannensu na fadar yanayin daya shiga ya gyara murayarsa da yayi ne
ya katse su ya sake gyara tsayuwarsa yana tura hannuwansa duka acikin ajihunsa wondonsa muryarsa a sanyaye ya fara magana “ku daina murna domin har yanzu da sauran aiki a gabanmu domin kuwa bamu tsira ba .”anas ya sauke numfashi da ajiye zuciya zuciyarsa na rawa ya juya ya kalli Ana’s kullum maganrka mu ajiye wannan aiki mu ajiye aikinan bayan kasan komai ajiye wannan aikin bazai ajiyu ba kamar yadda kake fad’a.”
“Ajiye wannan aikin lallai yana bukatar nazari kamar yadda muka tsara komai kafin mu fara shima haka zamu tsara komai kafin mu barsa dan idan bamu kawo sauye sauye ba ko mun barsa dole zamu samu matsalar da’ake wa gudu faruwarta , yanzu kaga aiki da kwakwaluwa ko ?” acikinku babu wanda yayi tunanin wannan gidan ba aiki kawai zamu dinga yi ba kawo tsare tsare acikin aikin wanda idan matsala taso afkuwa akwai mafaka yanzu meye abunyi .”?
Tana tsaye tana cigaba da kai kawo taga alamun shigowar sako layinta da wani irin sauri ta qarasa inda wayar take jikinta a kasalance ta dauki wayar daga sama taga shigowar jaguwa jikinta na rawa ta soma karantawa Ji tayi jikinta da kafafunta sun dauki rawa suna barazanar kasa daukar ta ,lokaci daya zuciyarta ta nemi ta tarwatse ta dinga bin sako tana sake karantawa cikin tsananin kaduwa da tashin hankali bata son ta rashi “wata irin qara ta saki wanda gabadaya gidan ya dauka ta daura hannuwanta duka bisa kanta tana kiran “wayyo allah na shiga uku, shikenan adnan ya sadaukar da rayuwarsa a banza ,amman ba kansa cuta ba ni ya cuta .”
mumy ta dake daki tana amsa waya ta fito da sauri tana dafata “tanwer tanwer!! lafiyar ki kike kiran sunan adnan haka cikin tashin hankali what’s wrong with him”?” Mumy adnan zai mutu.” ta fada cikin mawuyacin hali jikinta na sake daukar zafi “taya akayi kikasan hakan “?batayi magana sai hawaye masu zafi dake tsiyaya akan kuncinta ta mika ma mumy wayarta dan bazata iya karanta mata sakonsa ba “shikenan ya cuci zuciyata mumy “.“me yasa kayi min haka ? me yasa ka cuci zuciyata adnan “.?
mumy ta zauna ta kamota ta rungumeta tsam ajikinta wacce gbdy ta rude ta fita haiyacinta mumy ta shiga shafa bayanta idanunta na kawo ruwa wata irin murya me hade da tashin hankali suka jiyo ana cewa “weldon abinda ya kamata kenan ya shiga hannun hukuma wannan shine burina shine adduar dana dade ina yi.” a matukar agigice tanwer ta dago daga jikin mumy tana duban dady dake tsaye a bakin kofar shigowa zuciyarta na kadawa Kmr ana kada qararrawa , lokaci guda dady ya cigaba da maganarsa hankalinsa kwamce “abinda na fada haka ne naji dadi kwarai da gaske da zai shiga hannun hukuma , a she daman yaudarar Ibrhim kikeyi ?
“Kika wani sake dashi a she har yanzu zuciyar na ga wannan tantirin ?”allah yasa a harbesa kowa ya huta wata irin zabura tayi tana girgizawa dady kai tamkar kadangariya tana cigaba da dubansa a matukar firgice “dady kana kuwa qaunata ?tayi maganar hawaye na turereniyar zubowa daga idanunta .”
“Dan girman allah kacewa hukuma su hada dani dady dan zan gwamaci mutuwa da wannan rayuwar , dan allah mumy kice Dady ya fada ma hukuma su hadani na mutu na huta yadda take maganar zaka fahimci tana cikin tashin hankali da firgici suna cikin wannan halin dady ya dauki remut ya kunna tv ya kai tashar labarai, nan take kuwa gidan jaguwa ya bayyana domin daukar kai tsaye ne akeyi ,tana kallo polisawa na basu umarnin su miko kansa amman shiru babu wanda ya fito acikinsu ai kuwa Ib da shugaban tawagar polisawa data sojoji suka bada umarnin harbi nan take sauran jami’an tsaron dake tsaye jiran umarni daga sama suka soma budewa gidan wuta wata razananniyar qara ta saki tare da zubewa kasa sunammiya.”