KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A tsanake ya zare hannunsa cikin nata ta sake runtse idanunta gam jikinta na sake ɗaukar zafi jallabiyar jikinsa ya zare, ya ajiye akan madaidaicin table din dake gefen gado, idanunshi na kanta yana zance zuci. ‘Allah kada kasa wani abu ya sameta a dalilin wannan shirmen nata na banza ,ban da abunta ma guda nawa take da zata d’aurawa kanta damuwar soyayyarsa ? tayi kankanta da daukar wannan nauyin, matan da suka fita girma da wayewa da komai fiyye da nata sun kasa shawo kansa a batu na soyayya bare ita , shi sam babu wannan a ransa “
Rankwafowa yayi jikinta tare da tokare hannunsa da katifa idanunshi na kanta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta duk cikin masu nacin sonshi ita kadai zuciyarsa da gangar jikinsa ta tausayawa ,bai sani ba ko dan ita din yarinya ce mai karancin shekarun da bata wuce autar d’akinsu ba ,hannuta daya ta Kai gefen kanta da taji yana sara mata da karfi a hankali ta soma motsa bakinta, matsota ya sake yi dan jin abinda zatace “mr.no name am feeling very dizzy”. tayi mgnr tana bude idanunta akan shi eye’s into eye’s suke kallon kwayar idanun juna “bana gani sosai ta karasa maganar tana kai hannunta kan damtsen hannunsa ta rike gam jikinta na sake daukar zafi “Mr.no name!”. ta sake kira sunansa tana lumshe ido “na kasa fahimtar meke damuna kaina ke…”
tayi shiru tana sake rike gefen kanta, cike da sanyi jiki yake binta da idanunshi yana shafa gefen fuskarta har ya kai hannunsa daidai kunnenta tare da zira yatsansa ɗaya , wani irin zirrrrrrrr taji a gbdy ilahirin jikinta mai kama da shoking take jikinta ya ɗauki rawa ganin haka yasa yayi saurin yin kasa da hannunsa zuwa gefen fuskarta ya cigaba da shafawa a hankali ta sake Kai hannunta kan damtsen hannunsa tana lumshe ido matso da fuskarsa yayi daidai nata har karan hancinsa na gugan nata tare da riko yatsun hannunta ya dunkule guri daya yana kallon kyakkawar fuskarta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke karuwa ,numfashi kawai take janyowa tana fitarwa da kyar .
Motsin kwankwasa kofar d’akin yasa ta tsaitsaita numfashinta ta buɗe idanunta fess tana kokarin kallon kofa shi kuwa har lokacin hannunsa na kan shafa fuskarta haka idanunshi na kan fuskarta ya kasa daukesu “mr.no name, kamar wani yana buga kofa”. Ta furta a hankali “karki damu babu Wanda zai shigo d’akin nan sai da izinina tayi shiru “ki yarda dani babu wanda zai shigo hannuwanta duka ta Kai qirjinsa tana yarfesu, sautin wata murya ce ta doke dodon kunnenta “hey adnan open the door plz, is me”. hade da buga kofor da karfi kamar za’a balla a hankali ya dan juyo yana kallon kofar sakamakon jin kuryar zahra “adnan!”……….
ta furta sunan tana lumshe idanunta wani irin dad’i taji ya mamayeta atleast she know his name yadda yake da tsananin kyau haka sunansa ke dadin ……. .
Tsura mata ido yayi saboda jin sunan daga bakinta “sautin mace naji ko matarka ce?!”. tayi maganar hankalinta a matukar tashe tana mai sake Kai hannuwanta qirjinsa ta fara turesa ya mike yayinda take kokarin saukowa yayi saurin maidaita “ki kwantar da hankaliki ki kwanta ki dan huta bari naje na dawo sai mu tafi”. ya janyo rigarsa ya zira ya nufi kofar sai ganinta yayi ta mike tana neman hanyar buya yayi saurin riko hannunta “ina zaki?!”hannunsa tabi da ido “,ki koma ki kwanta ki bani minti biyu yanzu zan dawo mu wuce”
” adnan dan Allah ka bude min kofa mana!”. Aka Kuma fad’a daga daya bangaren take jikinta ya kama rawa ta soma zazzare idanu hannunsa duka yasa ya riko kafadunta ta zaro ido tana kokarin fixge jikinta “wayyo Allah tsoro nake ji kar matarka ta ganni, if she see me what will she do nasan! kasheni zatai “yes she will definitely kill me, dan Allah ka boyeni”. tayi mgnr a rud’e sound dinta na tashi tana ko’k’arin buya a jikinsa , hade rai yayi “ke malama ki kwanta nace!”.
yayi mgn a tsawace yana nuna mata katifa cike da sanyin jiki da tsoro tayi taku biyu ta zauna a gefen katifa jikinta na rawa ya k’arasa jikin kofar ya Kai hannunsa kan handle yaji kofar a kulle gam tsaki yaja “a she a rufe kofar take shiyasa Zahra ta kasa shigowa” yayi magana a k’asan ransa , murda key yayi hade da zarewa ya fito yana sauke idanunshi akanta “Kai da waye a cikin d’akin?!”. tayi tambayar kamar wata zararriya tana wani irin huci tamkar mijinta .
“Muje”. Ya mata alamu da hannunsa yana nuna mata daya part d’in. Kallonsa tayi cikin zafin rai tabi ta gefensa ta tunkari ko’far da Tanweer take cikin zafin nama yasa hannunsa ya fincikota baya. “Me kake nufi Adnan karuwa ka kawo gidan nan ?”. Tayi maganar tare da k’ura mishi ido. “Ba karuwa bace kar….”. “Karuwa ce mana” ta sake furtawa cikin d’aga murya, runtse idannunsa yayi jin tana Kuma had’a Tanweer da mummunar kalmar sosai ranshi ya soma baci.
“Na fada miki ki daina kiranta da wannan mummunar kalmar dan ba ita bace”. ya fada cike da bacin rai yana huci yayi cilli da hannunta daya rike , Kallonsa tayi tare da murmushin takaici ta kara yunk’urawa. “Koma wacece wannan karuwa sai na…”. Fisgota yayi da karfi tare da shimfid’a mata wani irin gigitaccen mari, kan ta dawo hayyacinta ya fisgeta tuni zuwa hanyar da bataso, bai ajiyeta ko Inaba sai wani katon d’aki.
Cillata yayi gefe ya juya zuciyarsa na masa wani irin zafi. “Adnan!”ta Kira sunansa cikin d’aga murya tana sha gabansa. “Wacece kuke magana? Wace matsiyaciyar yar kar…”. Tasssss ya sake d’auke kyakyawar fuskarta da wani gigitaccen mari wanda yafi wanda ya mata a baya, fashewa tayi da wani irin kuka. “Nace ki daina me yasa bakya…”. “Yanzu akan wata ‘ya mace kad’au hannu Ka mareni? na shiga uku!”. Ta katse shi cikin muryar kuka tare da k’ara fashewa da wani sabon kukan ta koma gefen gadon ta zauna baka Jin komai sai fitar sautin kukanta.
Shiru yayi qirjinsa na masa wani irin rada’d’i da zafi wanda baisan na meye ba b’acin raine ko kukanta ko kuma kalmar karuwa da zahra ta danganta yarinyar dashi ne , shiru yayi yana sauraron kukanta gashi abunda yatsana kenan a rayuwarsa yaga mace na kuka ,sanin hakan yasa Zahra ta k’ara k’arfin kukanta, bud’e idanunsa dake runtse yayi , cikin wani irin zafi ya soma taku a hankali har ya k’arasa bakin gadon, zama yayi daga gefenta. “Look Zahra! Kiy…”. Sake fashewa tayi da wani sabon kukan “Ya Salam! dan girman Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan dan Allah”ya fad’a lokacin daya Kai hannu yana d’an bubbuga kafad’arta, a hankali Zahra ta sulale ta shige jikinsa. “Baby wacece wannan yarinyar daka mareni akanta ? “tayi masa tambayar tare da sauke ajiyar zuciya ..
“Bakowa bace!”. Ya furta hakan cikin ko’k’arinsa na kauda zancen dan jinta a jikinsa ba k’aramun tada mishi sha’awa tayi ba musamman yadda ta tura hannunta cikin k’irjinsa tana wasa da kan nipple’s dinsa lumshe idanunsa yayi gaba daya tare da laso busasshen labbansa.